SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

Ture hannunta yayi tareda faɗuwa ƙasa ya sunkuyar da kai

Wani tsananin tausayinsa nake ji, ji nake kamar na ƙarasa na rungumesa na rarrasheshi amma nasan hakan babu dama dan haka nakoma gefe na raɓe ina ƙwallar tausayinsa

Bayan Prince Yar ya dawo, Big Madam ta umarci dukkanmu mu koma parlor

Cikin awa biyu an shirya gawar

Makusantansa mata ne suka shiga sukayi masa addu’a sannan jama’ar da suka cika maƙil suka ɗaukesa dan masa rakiya gidan gaskiya

Tun daga nan ban sake saka Prince Sydeek a ido ba, har ƙarfe takwas na dare, Big Madam ce ta sanya aka kaini ɓangarensa, gyara wajen na kuma yi sannan na saka turare mai daɗin ƙamshi na kunna Ac

Kitchen na wuce na yi masa faten dankali wanda na barsa ya dahu yayi rugu rugu sannan nayi masa farfesun ƴan ciki da mint tea

Misalin ƙarfe goma na dare ya shigo, kana ganinsa kasan baya da nutsuwa, yayi kalar tausayi ga rama har ta bayyana a fuskarsa

Hanyar ɗaki ya nufa

Da sauri na bi bayansa nace “Prince Sydeek”

Tsayawa yayi batareda yace komai ba kuma bai juyo ba

“Ya haƙuri?” Na faɗa a sanyaye

Gyaɗa kai kawai yayi sannan ya saka kai ya shige cikin ɗaki

Kujera na koma na zauna ina tunanin hanyar da zan bi in tunkaresa nace ya ci abinci, shawarar binsa da su ɗaki nayi

Kayan abincin na ɗora kan ƙaton tray sannan na shiga ɗakin da sallama a bakina

Ban tadda shi a ɗakin ba sai dai na ji ƙarar ruwa hakan ya tabbatar min yana wanka

Tsiyaya mint tea ɗin da ke ta tashin ƙamshi nayi a cup sannan na ajiye masa, ina ƙoƙarin miƙewa ya turo ƙofar

Ɗaga idona na sauke su a kansa, ɗaure yake da towel a ƙugu yana goge ƙaƙƙarfan jikinsa mai nuni da shi ɗin cikkaken jarumi ne da ƙaramin towel, sumar kansa tayi luff a kansa da goshinsa

Kallon kallo muke sosai ganin ba zai yanke kallon ba na ɗauke nawa idon, sannan na miƙe na fice

Parlor na koma ina addu’ar Allah ya sanya zai ci abincin, bayan mintina kamar arba’in na miƙe dan shiga ɗakin na kwaso kwanuka

Knocking nayi sai dai bai tanka ba, na ɗan jima kafin na tura ƙofar na shiga

Kwance na gansa kan gado ƙudundune yana ta ɓari, da hanzari na nufesa ina faɗin “bakada lafiya?”

Idanunsa rufe suke gam amma nasan ba bacci yake ba, miƙewa nayi na kashe Ac dake aiki sannan na nufi drawer inda nake da tabbacin ba zai rasa magani ba na buɗe

Sai da na buɗe uku sannan naga mugunguna birjik, pain reliever na ɗauko masa sannan na nufesa ina faɗin “ga magani ka sha”

Bai tankani ba kuma bai buɗe idonsa ba

“Dan Allah ka sha, za ka ji daɗin jikinka” na faɗa ina ƙoƙarin janye blanket da ya rufa

Buɗe idanunsa yayi da sukayi jaa sosai sannan yace “ki ƙyaleni!!!” Sounding commanding

Jikina ne yayi sanyi sai na ajiye masa maganin kan bedside drawer na nufi kwanukan, bai taɓa komai ba sai ruwan zafin da ya shanye cup ɗaya da na ajiye masa

Ɗora masa flask ɗin nayi gefen gado sannan na tattare sauran kwanukan na fice ina mai jin tausayinsa ainun…..
[11/16, 4:19 PM] Muslima????: 59&60

S A R K I

LITTAFIN KUƊI NE, KI TUNTUƁENI TA 08167888934 DAN KARANTAWA CIKIN AMINCI

Sashenmu na yanke shawarar komawa dan ko bakomai ƙila yana buƙatar lokaci shi kaɗai, kuma babu daɗi nake ji ganinsa cikin damuwa banida halin yaye masa

Nayi nisa cikin tafiyata na ji an fincikoni da ƙarfin gaske, ko kafin na fahimci waye an ɗauke ni da zazzafan mari tareda hankaɗani jikin bango

Dafe ƙeyata da ta bugu sosai nayi nace “washh”

“Ashe da ma ke mahaukaciya ce?, meyasa baki faɗamin aiko ki yayi da takaddun ba, ki ka kawomin kikayi shiru, da ke za’a haɗa baki a cuceni?” Ya faɗa muryarsa cikeda ɓacin rai ya maƙure wuyana

Da dukkan ƙarfina na fara ƙoƙarin ɓamɓare hannunsa daga wuyana da ji nake kamar numfashina zai ɗauke, ganin ina struggling ya sakeni

Tari na fara ina riƙe da wuyana da nakejin wani azaba idona na zubda ƙwalla, sai da na ɗan samu sa’ida sannan na ɗago nace “haba!! Na rantse maka da Allah ni bansan abinda ya faru ba, bai aikeni ba wallahi, ya ajiye na ɗauko na kawo maka kamar yanda ka buƙata bansan yanda akayi hakan ya faru ba”

“Meyasa baki duba ba?!!!!” Ya faɗa a fusace yana kuma nufoni

Jaa da baya nayi tareda saka hannuna kan wuyana gudun ka da ya kuma shaƙeni sannan nace “dan Allah ka tsaya, ni taya zan gane?, ta ya zan fahimci ma wasu takaddu, dan Allah kar ka kuma matsowa kusada ni” na faɗa cikin firgici

Tsai yayi sannan yace “wallahi sai na rama, wallahi ba zai ja min asara ba, na rantse da Allah sai na mallaki dukkanin dukiyarsa” ya faɗa cikin tsananin ɓacin rai

Gyaɗa kai kawai nakeyi alamun amincewa gudun kada ya kuma birkicewa

“Zan tura na kwaso dukkanin. …” bai ƙarasa ba kawai ya ja ƙwafa sannan ya saki murmushi

A ɗan tsorace da yanayinsa nace “dan Allah ni dai kayi haƙuri ba laifina ba ne”

“It’s alright, i’m sorry for hurting you Batool Habeebty” ya faɗa yana nufoni

A tsorace na jaa da baya ina faɗin “dan Allah kar ka matsoni”

Dakatawa yayi sannan yace “i’m sorry”

Shiru nayi ina sakin ajiyar zuciya dan ba ƙaramar shaƙa na sha ba

“Gobe kar ki kwana a sashen Sydeek” ya faɗa yana shigewa

Sighhh na saki nace “mugu”

Fasa zuwa sashenmu nayi na koma side ɗin Prince Sydeek

Da wuya bacci ya ɗaukeni a ranar, washegari da safe Prince Sydeek da wuri ya fita bai tsaya cin komai ba, nasan saboda masu zuwa condolence ne

Bayan na gyara dukkan sashen tunanin zancen Prince Yar na cigaba da yi wanda na kwana da shi na tashi da shi

Miƙewa nayi na nufi ɗakin Prince Sydeek, na jima a ciki kafin na fito ɗauke da bagpack mai ɗan girma, a parlor na ajiyeta har zan tashi sai na koma

Pc ɗinsa na ɗauka tareda jona flash, na jima a kai kafin na cire na ajiyeta tareda wiping dukkan abinda ke cikinta, sai da nagama nace “i’m sorry Prince Sydeek” na miƙe na fice zuwa sashenmu

Cikin wani ƙaramin store a ɗakin da ya sha ƙura da datti sakamakon rashin amfani da shi na tura jakar sannan na kwanta bacci zuciyata wani ɓarin wasai wani ɓarin tunanin abinda Prince Yar ke shirin aikatawa

Bani na koma sashen Prince Sydeek ba sai ƙarfe bakwai dan nasan da wuya ya na nan

Zaune na gansa kan kujera hannunsa riƙe da mug yana sipping tea

Ƙarasawa nayi ɗan nesa da shi na zauna kan carpet sannan nace “ya ƙarin haƙuri?”

Fuska babu yabo ba fallasa yace “angode Allah”

Murmushi na ɗan saki sannan nace “dan Allah alfarma nake nema a wajenka” kaina a ƙasa

Ya jima kafin yace “ta me?”

Ɗan shiru nayi sannan nace “dan Allah kar ka kwana a nan”

Cikin mamaki ya ɗago kai ya kalleni sannan yace “as in?”

“Big Madam ce aka ce zazzaɓi ta keyi tun ɗazu kuma ya ƙi sauka, batada wanda zai rarrasheta itama an mata rashi” na faɗa

Shiru ya ɗanyi sannan yace “wa ya ce ba lafiya?”

“Maids ɗin sashenta” na faɗa ina raba ido

Miƙewa yayi ya shiga ɗaki mintina kaɗan sai ga shi ya dawo cikin wasu kayan, hannunsa riƙe da wayarsa

“Ka tafi?” Na tambaya

“Eh” ya bani amsa a taƙaice sannan ya fice

Ina ganin tashin motarsu na dawo na saka ma wajen kwaɗo kana na fice zuwa sashenmu zuciyata fes…..

TEAM BATYAR OR TEAM BATSAD WANNE ZAIYI WINNING NE???

Ni dai ina Batyar????????

[11/16, 5:58 PM] Muslima????: ???? S A R K I

61&62

Washegari da safe ban tashi da wuri ba sai wajen ƙarfe takwas da rabi, cikin sauri na fara shiri

Around 9:30am na wuce sashen Prince Sydeek, tun daga ƙofar gate na san da matsala kasancewar ƙofar Prince Sydeek da ke a ɓalle ta faɗi ƙasa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button