SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

Big Madam haɗe da Salamat da Princess Zairah tare suka shigo ina kallonsu sai dai fuskar Zairah babu walwala kamar dan dole ta zo

Tare suka nufoni, Zairah tana a bayansu tana kalle kalle har muka gaisa da Big Madam da Salamat

Big Madam ce ta taɓota tana faɗin “ba ki gaisa da ita ba”

Juyowa tayi ta sauke idonta a kaina, cikin firgici ta gwalalo idanunta waje tareda faɗin “Batool!”

Murmushi na saki nace “Princess Zairah!”

Zaro ido ta kuma yi cikin tsananin mamaki sannan ta zube ƙasa a sume…..
[11/24, 7:23 PM] Muslima????: ???? S A R K I

100

????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Bayan faɗuwar Princess Zairah haka aka lallaɓa aka ɗauketa sannan suka fita da ita zuwa asibiti

Shagali bai tsaya ba, haka na cigaba da gaisawa da manyan mutane suna min Congratulations gamida bani gifts kala kala, ba mu muka tashi ba sai ana daff da isha’i

Sashenmu na koma na watsa ruwa kana na rama sallolina sannan muka ci abinci da Junnut a private room ɗina gudun maids ƴan gulma

Bayan mun gama na tattara na koma sashensa na zauna a parlor ina kallo

Sai wajen tara ya shigo bakinsa ɗauke da sallama

Amsawa nayi da murmushi a fuskata

Hannunsa ya buɗe yace “come here”

Da dariya na ƙarasa na faɗa jikinsa, ɗaukana yayi ya fara juyi da ni yana faɗin “mai matata take ci ne batada nauyi”

Banda dariya babu abinda nake har ya saukeni, ina rungume jikinsa muka shiga ɗaki sannan ya direni kan sofa yana faɗin “bari na watsa ruwa”

Gyaɗa kai nayi sannan na miƙe bayan ya wuce, private kitchen na shiga na haɗa masa abinci mara nauyi haɗe da mint tea sannan na dawo na ajiye

Zaune na taddasa yana latse latse a system, hannu na sanya na rufeta gamida turo baki

Kafeni yayi da kallo sannan yace “ya haka”

Murmushi na saki sannan nace “yanzu kana neman shiga lokacina ne”

Dariya ya saki mai ɗan sauti sannan ya janyoni ya ɗora bisa cinyarsa yana faɗin “zo na ganki”

Sunnewa nayi cikin ƙirjinsa ina jin daɗin ƙamshin da ke tashi jikinsa

Hannunsa ya ɗaura kan duwatsun da ke ƙasan farar lafayar jikina yana wasa da su sannan ya ɗago kai ya kalli ƙwayar idona yana faɗin “kin min kyau Anisa!”

“Anitha ne!” Na faɗa da murmushi

“Anisa!” Ya faɗa yana ɗora hannunsa bayana yana shafani

Murmushi na saki sannan nace “toh sarki”

Dariya ya saki yana faɗin “kema sarkin ce, kinga kin tuna min da kakata Ayya tace na haɗaku kuyi waya” ya faɗa yana janyo wayarsa

Kiranta yayi sannan ya bani wayar, cikin harshen turanci muka gaisa da ita mun daɗe muna hira domin matar akwai barkwanci da ban dariya sannan ta bani mai gidanta, shi kuma da larabci ya min magana, ya min nasiha sosai tareda jaddadamin haƙuri kafin mukayi sallama da su

Sauka nayi daga cinyarsa nace “bari na baka abinci”

Ƙasa ya sauko nayi serving ɗinsa sannan ya ci, ya ci sosai kafin yace ya ƙoshi

Ɗaki muka nufa, bayan yayi brush ya taddani kan gado

Lufff nayi tareda matse jikina gam na ruƙunƙume blanket nayi shiru kamar mai bacci

Ko da ya kwanta ina jin sa ya saki dariya mai ɗan sauti sannan yace “cikin minti goma har kinyi bacci Anisa”

“Um” na faɗa a taƙaice ina juya masa baya

Kwanciya yayi gadon tareda janyoni yana faɗin “gaskiya ki tashi ki bani”

Cikin muryar kuka nace “akwai ciwo fa”

“Kaɗan” ya faɗa yana birkitoni gamida warware lafayar jikina

Washegari da safe sai shagwaɓa nake masa duk yanda ya so ya kuma da subh hanawa nayi dan dole ya haƙura a zuwan mun haɗu da dare

PRINCESS ZAIRAH POV

A hankali ta buɗe idanunta, ƙoƙarin tashi ta farayi sai dai rabin jikinta ƙam ya riƙe ya ƙi motsawa

Maid ɗinta ce ta nufeta da sauri tana faɗin “sannu bari na kira likita”

Likita tareda Big Madam suka shigo

Big Madam cikin damuwa ta ƙarasa wajenta tace “sannu Zairah, Allah ya baki lafiya”

Princess Zairah da ke son magana amma bakinta ya kasa bada haɗin kai kawai sai ta fara tsiyayar hawaye

Likitan ne yace “a’a ki daina kuka, insha Allah zaki samu sauƙi, dalilin stroke ne amma da yardar Allah zaki samu sauƙi”

Big Madam ce tace “yanzu doctor tsawon wani lokaci zata ɗauka a haka kafin ta samu sauƙi?”

Shiru yayi sannan yace “gaskiya bazan iya cewa ba domin yadanganta daga ita ne, wasu su kan ƙare rayuwarsu a haka, wasu shekara goma, wasu biyar, wasu uku, wasu ma a shekara guda suke samun sauƙi”

Wasu hawaye ne masu ɗumi suka tsiyayo mata cikin zuciya tana faɗin wani irin paralysis tana ganiyar cin duniyarta, lallai Allah abin tsoro ne, ita da take burin ta maida Batool irinta sai ga shi lokaci guda Batool ɗin ta shallake mata, ganinta ma wuya zai mata in ba ta nemi izininta ba, sa’ilin nan ga wannan cutar da ta risketa bazata tashi ba, wasu hawaye ne masu mugun ɗumi suka sauko mata sannan cikin zuciya tace astagfirullah, haƙiƙa ta yarda babu bawan da ya san ƙaddararsa, babu wanda ya san ƙarshensa domin da ta nada masaniya da yau bata ko tako ƙofa ba bare wannan mugun abu ya sameta

ANITHA POV

months later

Kwance nake jikinsa idona a lumshe

Hannunsa ya ɗora kan cikina da ke watansa na biyar sannan yace “my baby i am eager to see you”

Turo baki nayi nace “wai kai ni da babyn wa ka fi so?”

Dariya yayi sannan ya ɗaga min gira ya kalli cikina

Hawaye ne suka fara zubomin na fara miƙewa ƙoƙarin miƙewa daga jikinsa, janyoni yayi tareda cewa “ke fa wasa nake, nafi son ki nesa ba ma kusa ba”

“Da gaske?” Na faɗa ina pouting lips ɗina

Jan kumatuna da suka ƙara girma yayi yace “sosai ma”

Murmushi nayi sannan na kuma shigewa jikinsa ina shaƙar ƙamshinsa da na fi ƙauna sama da komai ahalin yanzu

Cikin kunnena ya raɗa min “i want a princess”

Turo baki nayi nace “a’a ni Prince nake so mai kama da kai”

“Ni princess nake so mai kama da ke” ya faɗa yana

Ɗan dukan ƙirjinsa nayi sannan nace “ni a’a, wai yaushe zaka kuma kai ni NIGERIA?”

Murmushi ya saki sannan yace “ke bazaki ba, kinyi zuwa ɗaya ya isa”

Turo baki nayi sannan nace “wallahi mutanen ƙasar na da kirki da girmama mutum, ina son na kuma komawa na sha fura”

Dariya ya saki yace “ni tashi muje ki bani furar”

Da mamaki nace “ina furar?”

Raɗa yayi min a kunne sannan ya

Rufe fuskata nayi bayan na ɗan dakesa sannan na noƙe a ƙirjinsa cikin kunya

Dariya ya saki sannan yace “sarauniyata ina sonki”

Murmushi nima nayi nace “ban taɓa mafarkin samunka a miji ba, gashi yanzu kai ba ma Prince ba ne S A R K I ne”

Dariya yayi sannan yace “ina sonki sarauniyata”

Nima dariyar nayi nace “ina sonka S A R K I na”

Mss Flower POV

Ba kasafai ko da yaushe mutum ke samun abinda yake buri ko muradi ba, ka kanso abu sosai amma ya zamana Allah bai ƙadarci zaka mallakesa ba, ƙila ta dalilin hakan ka kaucewa hanyar Allah ko kuma ka jefa kanka cikin gaggarumar matsalar da baka san ya zaka fita a cikinta ba, haƙiƙa kamar yanda Allah ya faɗa cewar yana tare da masu haƙuri, mu koyawa zukatanmu haƙuri da rungumar ƙaddara mai kyau ko akasinta domin in kayi hakan ka kan kaucewa saɓon Allah da kuma da nasani maras amfani

Sau tari bawa kanyi mantuwar bashi yakeda ikon karɓar ransa ba yayita saɓon Allah kwatsam sai mutuwa ta riskesa babu zato ba tsammani, dan haka a komai na rayuwa mu ringa tuna akwai ranar mutuwa, kuma ita mutuwa! Bata sallama. Mu daina mance akwai ƙaddarar da ka iya gifto maka mara kyau a kowani lokaci batareda kayi shirin tarbarta ba, dan haka mu yawaita khairan mu guji sharran. A nan ni Mss Flower???? nake ce muku Bissalam.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button