Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

Ad

_____

Da kallo na bi ƙofar, mind ɗina was telling me da banyi rejecting ɗinsa ba, after all ya min taimako yana kulawa da ni, and my heart was saying Batool bakya son shi, don’t ever kiss him afterall wani taimakon ne yayi miki ma, i tried to think amma sai na kasa coz i’m locked and doomed

NIGERIA

KANO STATE

Kwance yake kan gado, jikinsa fari tas alamun yana cikin tsananin ciwo tareda rashin jini mai yawa, idanunsa a rufe suke amma ba bacci yake ba

Tunani yake ina take, mai takeyi, mai ya faru da ita bayan tafiyarsa

Yana tsaka da wannan tunani wasu ƙwalla suka zubo masa, jin ɗumi a fuskarsa yayi saurin dangwalowa, “hawaye?!” Ya faɗa cikin karaya

Ya ɗauki ɗan lokaci kafin yace “Ya Allah ina roƙonka ka kuɓutar da wannan baiwa taka, Allah ka da ka bawa wani damar cutar da ita, Allah ka kuma haɗa fuskokinmu da alkhairi” ya faɗa a sanyaye

“SARKI ka farka ne?” Cewar wata tsohuwa mai kyawun gaske ta shigo hannunta ɗauke da jug

A hankali ya ɗan buɗe idonsa sannan ya saki ɗan murmushi yace “Ayya bani jin daɗin jikin nan nawa, sai nake gani kamar lokacina ne yayi”

Cikin sauri ta ɗora hannunta bisa bakinsa tace “ka daina faɗin haka, ita cuta ba mutuwa ba ce Sarki, da yardar mai sama zaka tashi cikeda jarumtarka” ta faɗa a sanyaye

Murmushi yayi yace “Allah ya amince Ayya”

“Wallahi Sarki bani son ƙasarku da mutanenta, har wa yau ina jin raɗaɗin rasa Fatima da nayi, an kasheta cikin zalunci, kai ɗinma gashi suna neman kassaraka ta hanya guda da suka kashe mahaifiyarka, mutanenku azzalumai ne kan sarauta basa tsoron Allah!” Ta ƙare cikin hawaye

Cikin muryar rashin lafiya yace “Ayya ki daina kuka haka, komai da kike gani muƙaddari ne daga Allah, su basu isa su min abinda Allah bai tsara ba cikin rayuwata, in kinga na mutu Allah ya tsara ne tun kan zuwana duniyar nan” ya faɗa cikin sanyin gaske

Hannu ta ɗora kan hannunsa sannan tace “tashi mu jarraba wannan, ɗazu Alhaji yace a haɗa an sanar mishi yana kashe ƙarfin guba, kafin jibi ku wuce ayi flushing ɗinta zaka ji ƙarfin jikinka”

Ruwan ɗumi ne da aka tafasa shi da ginger, garlic, cloves, sannan aka matsa lemon aka zuba zuma,

Sosai Ayyah ta bashi ya kwankwaɗa, ko da ya sha jikinta ya ɗora kansa yana sauke numfashi

Ayya a hankali ta hau buga bayansa tana faɗin “ina ma Fatima itama gida ta dawo, rashin sani baiwar Allah bamu san guba ba ce, kasan wannan shegiyar guba ce inji Alhaji bata cika fitowa ba sai mutum ya kai gab da kabari, wasu ma har su mutu ba’a gane mai ya kashesu, Sarki nace ko zaka haƙura da wannan masarautar ne?”

“A’a mahaifina na buƙatata” ya faɗa yana tari

“Sannu, ni na tsorata da lamarin masarautar ta ku ne, ni tun farko banso Fatima tayi aure chan ba kawai dan hakan yana cikin ƙaddararta ne, daga mun je Dubai ta ga mahaifinka ta liƙe masa bata ma san ɗan sarki ba ne, dan jaraba bansan yanda akayi soyayya ta ƙullu tsakaninsu ba, kai wannan abu bai min daɗi ba, ta silarsa na rasa ƴa ta”

“Amma ai kin sameni” ya faɗa a raunane

Cikin tausayawa tace “hakane, Allah ya ɗoraka kan maƙiyanka da yardar Allah sai dai ka ga bayansu ba dai su ga naka ba, nasan baƙinciki suke na kasancewarka babba, tau ya suka iya haka rabbi ya tsara, jinin Nigeria sai ya mulkesu da izinin jallah” ta faɗa tareda ƙarewa da ƙwafa

“Kin isheni da surutu” ya faɗa yana lumshe idonsa

“Kai ni ɗaga ni, zani girki kwanta kan pillow tunda maras kunya kake” ta faɗa tana kwantar da shi kan pillow cikin kulawa

“SARKI da yardar Allah sai ka amsa sunan naka na Sydeek ( KING) su zasu kunyata, da ikon mai sama sai ka hau kujera ka bawa ɗanka, tunda sun salwantar mini ƴa ai dole su karɓi hukunci daga wajen jikana” ta faɗa tana ɗaga labule tareda ficewa

Taɓe baki yayi yace “uwar surutu” chan ƙasan murya

Tunanin Batool ya lula wanda shine sana’arsa tun rabuwarsa da ita. …..

Kina karantamin littafi kina jin daɗi ko, tau! In inada haƙƙi kanki Allah ya min sakayya
[11/12, 5:14 PM] Muslima🧕: LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI, NAIRA 300 KACAL TA ASUSUN 1401611541, FATIMA LAWAL SAID, ACCESS BANK, SAI KI YI SCREENSHOT ZUWA 08167888934, KO KUMA KATIN MTN ZUWA 08167888934

GASKIYA IN KI KA KARANTA MIN BOOK BAKI BIYA BA, BAN YAFE BA. IN DAI HAƘƘINA NE, ALLAH YAYI MIN SAKAYYA

S A R K I

          *39&40*

Washegari tun safe nake zumuɗi da ɗaukin zan koma palace, bayan nayi sallah ban iya komawa bacci ba, na zauna jiran dawowar Prince Yar

Har takwas ta gota babu shi babu alamarsa

Sai tara naji alamun taɓa ƙofa, cikin sauri na miƙe zuciyata fal murna, fuskata ce ta sauya sakamakon wani ne ya shigo ba Prince Yar ba

“Ke Prince Yar yayi tafiyar gaggawa, ki ci abinci sai ki shaƙi wannan abun da kanki, kuma wallahi kika ce masa bani na yi miki ba sai na miki rashin mutunci” ya ƙare yana diremin

Kallonsa kawai nayi batareda nace komai ba

“Ke bar kallona, hauka nakeyi da zan zauna na shaƙi wannan nima a mallakeni?” Ya faɗa yana taɓe baki

“Amma rufe hancinsa yakeyi” na faɗa da gaskiyata

“Toh ni bazan rufe ba, bazan zauna cikin wannan baƙin asirin ba, in kin gama cin abinci ki zuba da kanki ki dinga cewa Prince Yar shine ubangidana” ya ƙare da tsaki sannan ya fice

Taɓe baki nayi sannan na fara cin abincin, ko da na gama ɗan tsurawa kaskon ido nayi zuciyata na faɗin kada nayi na zubar kawai

Na jima kafin na yanke hukuncin watsarwa, a toilet na juye shi sannan nayi flushing na fito, zama nayi ba da jimawa ba wannan mutumin ya dawo

Da murmushi yana toshe hanci yace “har kin gama”

Gyaɗa masa kai kawai nayi

“Yawwa, ko ke fa, yanzu tashi muje na kai ki chan inda kike”, sai da ya rufemin ido sannan muka shiga mota, tafiyar minti shida muka tsaya

Daidai inda suka ɗaukeni suka direni sannan suka amshi ƙyallansu suka wuce

A gajiye na tura ƙofar ɗakinmu bakina ɗauke da sallama

Salamat dake zaune tana ganina ta kwashe da dariya har da riƙe ciki

Da mamaki nace “lafiyarki?”

Dariyar ta tsagaita sannan tace “shegiya Batool an ɗanɗani zumar namiji shiyasa kika kasa dawowa ko?”

Kallon bakida hankali nayi mata sannan na wuce toilet dan yin fitsari

Ina fitowa Salamat tace “yanzu tunda dai kin shigo sahu ya kamata ki sakarma Prince Yameen shima yayi ko, tunda naga ya ƙwallafa rai dayawa, so gara ki basa da kanki ba yayi raping ɗinki ba” ta faɗa in serious tune

A fusace na kalleta nace “ke wace irin mahaukaciya ce, angayamiki kowa ɗan iska ne irinku, toh wallahi har abada ba zai taɓa samuna ba nafi ƙarfinsa” na faɗa ina zama kan gado

“Hmmm, Batool wallahi sai Prince Yameen ya sameki, he can go to any limit akan abinda ya keso musamman mace” ta faɗa tana taɓe baki

Tsaki na ja kawai dan takaici kaɗai take bani

Bacci na kwanta, bani na tashi ba sai bayan la’asar

Tsaye naga Junnut tana murmushi, murmushin na maida mata sannan nace “kin dawo” ina ƙoƙarin tashi zaune

Zama tayi kan gadon sannan tace “na dawo, ina kika tafi ne kwana kusan uku duk hankalina ya tashi”

Murmushi nayi mata sannan nace “aiki ne yayi min yawa, ya kike?”

“Lafiya, tashi ki sallah toh, bari na samo miki abinci” ta faɗa tana miƙewa

Bayan nayi sallah naci abinci, zama nayi muka ɗan taɓa hira da Junnut har akayi magrib sannan ta fice

Bayan nayi isha’i fita nayi zuwa wajen da ke ɗebemin kewa na zauna ina shilla ƙafata, idona ne ya sauka akan apartment ɗin Prince Sydeek, ɗan jim nayi sannan nace “ko ya warke?”

Ad

_____

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button