SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

Ya fara karanto min nace “ka kira manager na bank ɗin da kake banking kace su dakatar da duk wani transaction da zai fita daga account ɗinka”

Bai tanka ba sai dai yayi kamar yanda na faɗa ɗin

Within few minutes na kwashe kaf kuɗin da ke bankin da akayi transfering kuɗin Prince Sydeek ɗin da farko which is Prince Yar other account

Alerts ne suka dinga faɗowa cikin wayarsa, murmushi ya saki yace “how can i repay you?”

Murmushi na sakar masa sannan na miƙe na koma parlor ina faɗin yanda murmushi ke wa fuskarsa kyau ainun

PRINCE YAR POV

Kwance yake kan cinyar Princess Zairah yana lissafin companies da zai buɗe bayan ya kauda Prince Sydeek

Princess Zairah ce ta saki murmushi sannan tace “ni fa kuɗin ba su kaɗai ne damuwata ba, na ganka kan kujera shine abinda zai sanya hankalina ya kwanta, yanzu duk bani cikin nutsuwa burina mu samu hanyar da zamu ga wannan shegiyar Batool ɗin ta faɗa mana inda seal yake in yaso wannan tsohuwar ma mu haukata ta da allurai da drugs, bare ta zamar mana obstacle a shirinmu” ta ƙare tana sighing

“Ki daina damuwa, the throne belongs to me for your information jira nake kawai a gama mourning a fara maganan throne ɗin, lokacin ne Sydeek zai san wane ne ni” ya ƙare yana sakin devlish smile

Ƙarar saƙo ne ya faɗo wayarsa

“An turo maka message” cewar Princess Zairah da ke shafa gashi kansa

“Network ne share” ya faɗa yana kuma tura kansa jikinta

Wani message ɗin ne ya faɗo, wani ya kuma faɗowa, dan dole Prince Yar ya miƙe yana yatsina fuska ya ɗauki wayarsa

Cikin tashin hankali ya zaro ido yana faɗin “what!!!!”

Princess Zairah da ta ga yanayinsa ya canza ta miƙe da sauri ta karɓi wayarsa, mutuwar tsaye tayi sakamakon account Balance ɗinsa da ta gani yana reading 0.00

Cikin tsananin tashin hankali Prince Yar ya kurma ihu yana faɗin “i’m done for, na shiga uku!!!” Ya ƙare yana zubewa ƙasa a sume

Princess Zairah da ke kuka da gudu ta nufesa ta shiga jijjiga shi tana faɗin “please wake up, we will find another way”

Ganin ya ƙi miƙewa ta nufi fridge ta ɗauko ruwa haɗe da yayyafa masa, doguwar ajiyar zuciya ya saki sannan ya buɗe idonsa yana faɗin “sai na kashe Sydeek wallahi sai na kashesa!!!!”

BATOOL POV

Ina kwance kan kujera ina tunanin gida, Prince Sydeek ya fito

Zama yayi kan kujerar da ke opposite ɗina sannan yace “how are you feeling?”

“Na ji dama sosai” na bashi amsa a taƙaice

Gyaɗa kai yayi sannan yace “i think kije ɗaki ki kwaso kayanki, ba zan samu kwanciyar hankali ba kina nesa da ni” ya faɗa yana kauda kansa

Ɗago kai nayi na kallesa tareda sakin ɗan murmushi sannan na miƙe nace “toh”

Abayan na rufa ba dan na so ba sannan na nufi ƙofa

Miƙewa yayi shima ya biyo bayana

Da mamaki na juyo nace “ina zaka?”

“Ba zan iya barinki ke kaɗai ba” ya faɗa a taƙaice

Murmushi nayi a zuciyata nace “na samu bodyguard”

A nesa da building ɗinmu ya tsaya sai dai yana hangoni har na shige

Da sallama na shiga ɗakin, zaune na tadda Salamat na ta sharɓar kuka yayinda Junnut ke rarrashinta

“Meya faru da ita?” Na tambaya dan she looks pitiful

Harara Junnut ta watsomin sannan tace “wai ina kike tafiya ne kiyi kwanaki?”

Ɗan langaɓar da kai nayi sannan nace “wallahi kinsan abin ne babu daidaituwa tun rasuwar his majesty, gabaɗaya ragamar kula da Prince Sydeek a hannuna ta ke”

“Allah dai yayi masa rahama” ta faɗa

“Meya samu wannan ne take kuka?” Na kuma tambaya

Salamat miƙewa tayi ta shiga toilet batareda ta tankani ba

Junnut ce cikin jimami da tausayawa tace “wallahi kinga Prince Yameen got her pregnant, ya sanya kuma wai sai an zubar da cikin” ta ƙare cikin tausayawa

“Hmmm, Allah ya kyauta” na faɗa sannan na fara haɗa kayana

Bayan na gama shiryawa na dubi Junnut nace “later”

Gyaɗa kai tayi sannan na fice

Ina daf da kaiwa inda yake. ……
[11/18, 5:32 PM] Muslima????: PARDON LAST CHAPTER SUPPOSE TO BE 69&70

???? S A R K I

       *71&72*

Ina daf da kaiwa inda yake ya miƙe daga wooden bench ɗin ya nufoni

Murmushi na ɗan sakar masa yayinda shikuma ya basar ya kauda kansa

Bayan mun isa apartment ɗinsa nuni yayi min da ɗayan room ɗin ciki sannan yace “you can use it” ya ƙare yana shigewa ɗaki

Murmushi na ɗan saki ina faɗin “izzar tsiya” sannan na shige ɗakin

It’s a beautiful and polished room, da akwai dukkan abinda mutum zai buƙata haɗe da toilet da bathroom

Zubewa nayi kan gadon ina faɗin “the Prince room all for me” cikin jindaɗi

Haka rayuwa tayi ta tafiya ina cikin apartment ɗin ina jinyar jikina har tsawon kwana biyu ban taka waje ba, Prince Sydeek ya kan fita sosai sai dai ko da ya fita ya kan kira telephone time to time ina ɗagawa nayi magana yake datsewa nasan duk dan tsoron ka da wani ya cutar dani ne duk da kuma ƙofar is locked with pins, coz yayi modernizing ɗinta da more secured one unlike ta baya da aka ɓalla

Zaune nake a parlor ina sipping juice dan tun safe cikina ke ciwo wanda inada tabbacin period ɗina ne zai zo, ina zaune na ji knocking a ƙofa

Miƙewa nayi tareda dannawa, hoton Prince Yar ne ya bayyana yana tsaye

Taɓe baki nayi sannan na koma na zauna, ina jinsa ya na ta knocking nayi banza da shi

Telephone ce ta ɗauki ƙara, a hankali na ɗaga haɗe da cewa “hello”

“Open the door, we need to talk” sautin Prince Yar ya daki kunnena

Saukewa nayi tareda katse kiran

Ƙara kira yayi har sau biyar ban ɗaga ba, sai a na shida na ɗaga nace “go away monster, bazan taɓa buɗe maka ba” na faɗa

Dariya yayi sannan yace “Batool you either give me that seal ko kuma na kashe Sydeek tsakanin yau da gobe”

“Do your worst” na faɗa tareda jan tsaki zanyi hanging wayar kenan naji an kira sa ɗaga kiran yayi sannan ya fara magana batareda yayi hanging ba while ina jin conversation ɗin wancan mutumin ƙila ya ƙure volume na wayarsa ne

Bayan ya gama wayar yana cewa “hello”, na katse tawa wayar tareda sakin slight smile

Kashe telephone ɗin nayi gabaɗaya sannan na koma kujera na zauna ina jin yanda cikina ke ciwo

PRINCE SYDEEK POV

Kwance ya ganta kan kujera dafe da ciki, idanunta a rufe suke amma yanda take yatsina fuska ya tabbatar masa idanunta biyu

Gyaran murya yayi

Batool buɗe idonta tayi a hankali tace “sannu da dawowa”

Gyaɗa kai kawai yayi sannan yace “lafiya?”

Ɗan yatsina fuska tayi tace “zan je side ɗinmu ne”

“Why?” Ya tambaya

“Bakomai” ta bashi amsa kanta a ƙasa

Bai kuma tankawa ba ya nufi hanyar ɗaki sannan ya juyo yace “kar ki je”

Shower ya shiga, minutes later ya fito tareda shiryawa cikin ƙananun kaya farare, ya taɓa favorite perf ɗinsa sai ya ji ya ƙare

Wani yayi spraying sannan ya fito da niyyar fita shopping

Zaune ya ganta tayi jugum tana kallon tv, tausayinta ne ya kamasa ganin yanda take zaune waje guda kusan kwana uku kamar prisoner

Gyaran murya yayi yace “follow me” yayi gaba

Batool dake sanye cikin abaya zumɓur tayi ta tashi tareda bin bayansa bayan ta kashe kayan kallon

A gidan baya ta zauna kamar yanda ya umarceta, sunyi tafiya mai tsayi kafin ta ɗauko flash ɗin da ta maƙala ta miƙa masa sannan tace “a ciki nayi copying komai na system ɗinka sannan nayi wiping ɗinta”

Da mamaki ya ɗago kai yana kallonta, ashe itace tayi masa wannan aikin, ya baza jama’a su bincika masa dukkan information ɗin da aka kwasa kafin ayi wiping pc ɗinsa kamar yanda ya gani

A sanyaye yace “how?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button