SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

A gurguje na karya da su Mom sannan na nufi sashen da yake, kamar jiya sai da securities ɗin sukayi min bin diddigi harda ƙarin fara tambayarsa kafin suka bani izinin shiga

Raina a ɗan ɓace na shiga, zaune na gansa kan kujera sanye cikin ƙananan kaya farare kamar kusan kowani lokaci yana danne danne a pc

Tsaye nayi bayan ya amsa sallamar ina ɓace ɓacen rai, ya kai minti guda kafin ya ɗago yace “lafiya kikayi tsaye a nan Anisa?”

Turo baki nayi sannan nace “wai kai bazaka faɗawa waɗancan samudawan wace ni ba a wajenka da zasu dinga min bin diddiƙi kamar wata ɓarauniya”

Dariya ya saki ƴar siririya mai ƙaramin sauti kafin ya sauke kyawawan idanunsa a kaina yace “toh afuwan, zo ki ji”

Zama nayi a kusada shi duk da haka ina turo baki nace “gani”

“Take a look, a nan nake son aurenmu ya kasance” ya faɗa yana nuna min five star hotel mai suna RITZ CARLTON, PENTAGON CITY HOTEL ɗaya daga cikin manyan hotels da ke VIRGINIA

Murmushi na saki nace “it’s beautiful”

“The decorations?” Ya tambaya yana kallona

“I like it” na faɗa ina sakin dariya

Murmushi ya saki sannan yace “yau nake son mu fara maganan aure da Daddynki, by tomorrow nake tunanin Big Madam da jama’a zasu fara zuwa, kinsan nace a week ɗin nan, nasan bakuda matsala wajen prepation coz duk zan ɗauki nauyin komai” ya faɗa

“Are you for real!, wai dagaske week ɗin nan zanyi aure?” Na tambaya ina blushing

Bai tankani ba sai girgiza kai kawai yayi

Murmushi na saki sannan nace “ka ci abinci, sai muje wajen Daddy formal introduction” na faɗa cikin jindaɗi

Bayan ya gama cin abinci tare muka nufi wajen Daddy, bayan sun gaisa na gabatar da shi sannan ya gabatar da kansa matsayin mai neman aurena

Cikin jindaɗi Daddy yace “dukkan abinda Anitha take so shi zan bata, ina sonta sama da dukkan abinda na mallaka, zan kuma iya jure komai a rayuwar duniya banda wulaƙantamin yarinya, dan haka duk da ka kasance mai mulki da arziƙi ina gargaɗinka da kada ka sake ka samun yarinya zubar ƙwalla domin bazan taɓa yafe wannan ba, fatan ka fahimci zancena” cewar Daddy yana kallon Sydeek

Wasu ƙwallar farinciki ne suka zubomin, Mom ce ta janyoni jikinta tana faɗin “meyasa zaki kuka?”

Sydeek da ɗan murmushi yace “insha Allah zan kiyaye dukkan abinda ka gindayamin, zaka sameni mai riƙe ƴar ka cikin aminci”

Sosai akayita jindaɗi daganan suka zauna suka ɗan tattauna sa’ilin nan na raka shi mota dan zai fita ne

Wunin ranar cikin farinciki nayita

Shirye shirye ya kama gadan gadan su buga cards da rabawa duk washegari aka fara kasancewar bikin ya zo a ƙaramin lokaci, ranar Big Madam ta iso kamar yanda Sydeek ya sanar min sai dai bamu samu haɗuwa ba kasancewar ta sauka ne da yamma kuma a hotel ɗin da Sydeek ya kama baki ɗayansa har ranar da za’a gama biki

Washegari Mom ta fara min gyaran jiki kasancewarta ƴar gayu kuma balarabiyar usuli, haɗuwa da Sydeek sai tayi mana wuya domin duk yanda na so satar hanya sai nayi kiciɓus da Mom ta kasa ta tsare har ana washegarin fara biki

Bawani events da zamuyi mu bayan ɗaurin auren dai, sai dai can ɓangaren Sydeek su kanyi wasu shagali nasu na larabawa kafin bikin. Yau ta kama ranar da zasuyi Henna

Cikin wata farar gown mai taushi na shirya sannan akayi min light make up muka wuce hotel ɗin da suka sauka inda nan ne za’ayi Henna ɗin

Bayan na zauna a pillow ɗin da aka tanada domin ni inata sakin ɗan murmushi Big Madam ta zo

Saurin sauke kaina a ƙasa nayi dan sai nake jin kamar har yanzu bata amince da ni ba

Hannuna ta kamo tareda ɗan matsawa tace “Batool kiyi haƙuri, idona ne ya rufe nayi miki abinda bai kamata ba amma ba dan bana son ki ba kinji?”

Murmushi nayi tareda gyaɗa kai

Rungumeni tayi sannan tace “welcome to our family”

Hawayen da bansan dalilinsu ba naji sun gangaromin, bayan ta raba hug ɗin hannu ta sanya ta sharemin hawayena sannan tace “daina kuka”

Gyaɗa kai nayi sannan nace “toh”

Ɗan yafitoni tayi alamun na kawo kunnena, cikin raɗa tace “ashe dama ke baturiya ce harda blue eyes gareki”, dariya na saki domin yanda tayi zancen ne ya bani dariya sosai

Sai da na gama sannan nace “eh, i’m sorry”

Dariya tayi sannan tace “bakomai”

Lalle ta ɗauko tareda sakamin a tafin hannu sannan tace “Allah yayi miki albarka”

“Amin” na amsa da murmushi

Bayan ta miƙe mai lalle tazo ta zauna ta fara zanamin zane mai kyau, ina ta kallon ƴammata na rawa gwanin burgewa ina dariya, haka har muka ƙarasa lallen

Cikin son barka dai aka gama wannan shagali sannan na koma gida da jama’ata

Wahegari ta kama ranar ɗaurin aure, tun asuba na kasa komawa bacci kasancewar wani baƙon yanayin da nake ji na ciki, shi ba baƙinciki ba kuma bana ce zallar farinciki ba, ta wani sashen na kan iya cewa farincikin ne amma da zarar na tuna mahaifana da zan bari, bari na har abada in ba zuwa nayi kwanaki ba sai in ji babu daɗi a raina

Misalin bakwai na fita ina zagaya wani sashe na mansion ɗinmu wajen da nafi ƙauna ina yarinya har girmana, wani ƙaramin ruwa ne garai garai mai wanda fulawoyi suka masa ƙawanya masu kyawun gaske, butterflies na zama wajen hakan ya kuma ƙawata wajen ainun

Na jima tsaye a wajen hawaye na ɗigomin kafin nace “yanzu barinku zanyi na canza duniya, na canza wajen zama”

“Zan iya yi miki wajen a inda zaki koma!” Naji ya faɗa ta bayana

Cikin sauri da mamaki na juya, sauke idona ƙasa nayi bayan na kallesa sannan na fara ƙoƙarin maida ƙwallata nace “yaushe ka zo?”

Bai tankani ba sai dai hankey ɗinsa ya zaro ya miƙa min, amsa nayi na goge idona sannan nace “thank you”

Kan wani wooden chair muka zauna kowa shiru

“Anisa!” Ya kira

“Na’am” na faɗa tareda kallonsa

“Zan kula da ke insha Allah” ya faɗa

Wani sanyi haɗe da daɗi naji a raina, ɗan murmushi na saki sannan nace “nima zanyi iya ƙoƙarina na faranta maka da dukkan iyawata”

Murmushi kawai yayi bai kuma cewa komai ba, mun ɗauki lokaci mai tsayi muna kallo yanda butterflies ke ta tsalle tsallensu kan flowers kafin ya dubeni yace “ya kamata mu je mu fara shiri”

Gyaɗa masa kai nayi tareda miƙewa, har ƙofa ya rakani kafin ya wuce nasa ɓangaren

Ina shiga ɗaki Mom tace “kin gama gantaltal ɗin, sai ki shiga wanka tunda lokaci ba tsayawa jiranki zaiyi ba”

Gyaɗa kai nayi tareda faɗawa toilet

Ina fitowa aka fara min kwalliya, sosai nayi kyau sanan na shirya cikin white wedding gown ɗita wadda tayi min kyau ba kaɗan ba, rolling akayi min tareda ɗora min jewelleries sannan muka wuce inda motoci ke jiranmu

Tareda Daddy, ƙaninsa, Mom da ƴan uwa muka shiga wajen ɗaurin auren, sosai wajen ya cika da al’umma maƙil, gefen Sydeek aka zaunar da ni

Ƙamshin turarensa mai masifar daɗi ya bigi hancina, duk yanda nakeson na kalli kyakyawar fuskarsa daurewa nayi

Takaddun aure muka fara cikewa sannan aka fara shirin ɗaurin aure na musulunci, bayan waliyyi na yayi dogon bayani Sydeek ya amshi mike yayi nasa tareda alƙawarin ɗaukar dukkan wani nauyina a matsayinsa na mijina, daga bisani aka ɗaura aure

Kuka kawai nakeyi na jingina jikin Mom da ke ɗayan gefena, bayan an gama ɗaurawa sannan aka ɗaura na Yameen da Salamat ma wanda yazo min a bazata, Sydeek yana shirin miƙewa dan gaisawa da mutane ya ɗora hannunsa bisa nawa, ɗago idona da yayi jage jage da ƙwalla nayi na kallesa, kashemin ido guda yayi tareda sakin wani killer smile

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button