SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

Rai ɓace ta ɗago ta kalleni sannan tace “Batool ban faɗa miki cewa ki fita sabgar Sydeek ba, ban faɗa miki ba zai taɓa aurenki ba, meyasa kike son ki zaƙe dayawa, daga ɗan taimako kema sai abin duniya ya ruɗe ki?, ban sanar miki zan miki sallama mai tsoka ba, meyasa zaki zagaye bayan fage kije ki dinga soyayya da Sydeek har kuyi dinner jiya, kin manta gobe ne ɗaurin aurensa?!!” Ta daka min tsawa

A sanyaye ƙwalla ta cika min ido nace “kiyi haƙuri dan Allah, wallahi ina son shi, ko a ta biyu ne kamar yanda yace zan auresa, please let us be together” na faɗa muryata na ɗan rawa

Shiru tayi kafin ta dubi wata maid tace “ɗauko min jakar nan”

Bata kuma cewa komai ba har saida aka kawo mata jakar, miƙomin tayi sannan tace “open”

Buɗewa nayi kamar yanda ta umarta, kuɗi ne masu yawan gaske na ƙasar dan bansan adadinsu ba, shiru nayi hawaye suka fara gangaromin

“Batool take this and leave silently, bana so ko sallama kiyi ma Sydeek, just go coz bazan taɓa approving ɗinki ba, go!!!” Ta faɗa tana kauda kanta gefe

Wasu hawaye masu ƙuna ne suka gangaromin, miƙewa nayi tareda ɗaukar jakar gudun kar tace na mata wulaƙanci sannan na fice

Ina zuwa ɗaki na tadda Junnut tana jin waƙa, cikin sauri ta miƙe tareda nufoni tana faɗin “meya sameki”

Rungumeta nayi haɗe da fashewa da kuka, na ɗauki lokaci mai tsayi ina kuka tana rarrashina kafin nace “Junnut soyayyata bazata taɓa tasiri ba, Big Madam tace na bar nan a yau batareda nayi ma Sydeek sallama ba, Junnut ya zanyi wallahi ina son shi” na ƙare ina sake sakin wani kukan

Junnut sosai ta rarrasheni sannan tace “ki sanar da shi zaki tafi, ki share batunta abinda Allah ya haɗa ita bata isa ta raba ba, ina ji a jikina ke Matar Sydeek ce”

Murmushi nayi tareda cewa “A’a Junnut zan tafi, bazan yi masa sallama ba haka ƙaddarar soyayyarmu take” na faɗa tareda miƙewa, kayana na fara haɗawa ina hawaye har na gama

Junnut cikin ƙwalla ta dubeni tace “yanzu Batool haka zaki tafi batareda kun gana da shi ba?”

Murmushi nayi sannan nace “eh, sati mai zuwa zan wuce ƙasata nima” a taƙaice

Jakar da Madam ta bani na buɗe haɗe da ɗaukan bundle biyu na kuɗin na ajiye sauran nace “ki ɗauka na baki”

Junnut zaro ido tayi tace “kina hauka ne, mai zanyi da wannan kuɗaɗen?”

A lokacin na fahimci sunada yawa, murmushi na saki ina yaba son kai irin na wasu mutanen

Junnut ce tayi min rakiya har wajen motar cefane sannan ta juya bayan ta zubda ƙwalla

Hawaye na share tareda jingina jikin ƙofa, har muka fito daga masarautar zuciyata ta kasa haƙuri da yarda cewa na rasa Prince Sydeek, to amma hakan ne na rasa shi mana, dan bana jin zamu kuma haɗuwa dan sati mai zuwa zan bar ƙasar nima na koma tawa

Bayan anyi packing store da suke cefane, nima shiga nayi na samu waya na siya da kuɗin da Big Madam ta bani sannan na siya sabon layi na fice

Taxi na tsaida na shiga zuwa EMIRATE PALACE HOTEL

Ɗaki na kama sannan na wuce zuciyata cikeda ƙunci

Kwanciya nayi akan gado tareda lulawa tunanin abinda ya wakana tsakanina da shi a jiya, murmushi na saki sannan na miƙe na nufi jakata na cire kaf kayana

Hankalina ne ya soma tashi dan na rasa ID card ɗina, duk binciken duniya rasa shi nayi sai dai na haƙura na fara shirin shiga wanka

Bathrob na sanya bayan na fito tareda tsayawa bakin mirror, hannu na sanya na cire black eye lens ɗina hakan ya bayyanar da blue eye balls ɗina

Murmushi na saki wanda ya bayyanar da dimples ɗina sannan nace “welcome back Anitha”

Blouse and trouser na saka sannan na zauna a gado na fara haɗa wayar da na siya ɗazu, ina haɗawa na danna number Mom sai dai har ta katse bata ɗaga ba

Ƙara kira nayi ta kusan yankewa sannan ta ɗaga tana faɗin “Assalamu Alaikum”

“Wa’alaikhi salam, Mom it’s me” na faɗa cikin dariya

Cikin murna tace “is that you Anitha?”

“Sure” na faɗa fara’a ta na faɗaɗa

“Oh my God! Na kusa mutuwa saboda damuwa, where have you been?, meyasa baki nemeni ba?” Ta faɗa kamar zatayi kuka

“Come on Mom, it’s a long story, yanzu dai na gama dukkan aiyukana a nan, i just need to rest for days sai ku turo azo ɗaukana” na faɗa cikin dariya

“Bakida hankali Anitha, in kin dawo nan kin huta, gobe zan turo helicopter ya ɗauko ki” ta faɗa

“No, please let me, ina son naga garin nan more” na faɗa

“Alright nan da five days!” Ta faɗa

“Huhhh!! Alright, ina Daddy?” Na faɗa

“Yana meeting da wasu shareholders na Aldama oil company” ta faɗa

“Alright, i need to go, take care” na faɗa

“Alright baby girl, i love you, take care” ta faɗa cikin so

Murmushi nayi nace “love you too” sannan na katse kiran

Telephone na ɗauka nayi ordering abinci sannan na zube kan gado ina tunanin ko me Prince Sydeek yakeyi yanzu, ya zai ji idan ya ji na tafi?

Bayan ankawo min abincin ban ma iya cin abincin sosai ba, tsakura kawai nayi na kira cleaners

Har wajen isha’i ina kwance ina tunanin Prince Sydeek, wasu ƙwalla ne suka gangaromin tunowa da nayi bazan kuma ganinsa ba, hannuna na kalla da ya sanya min ring jiya

Murmushi nayi sannan na zare zoben daga hannuna ina faɗin “i will miss you”, window na buɗe ina ƙoƙarin throwing ɗinsa sai kuma naji bazan iya ba

Wasu ƙwalla ne masu ɗumi suka gangaromin, fasawa nayi sannan na samu zare nayi necklace da zoben

SYDEEK POV

Zaune yake kan sofa yana jiran zuwan Batool, tun yammaci yake aikawa a kirata ana ce masa bata nan

Wata maid ce ta shigo kanta a ƙasa tace “your highness Batool fa bata masarautar nan inji roomate ɗinta”

Wata zabura yayi sannan ya saita nutsuwarsa ya miƙe ya fice gabansa na tsananta faɗuwa, tun tashinsa safiyar yau yake jinsa cikin wani irin yanayi

Bai tsaya jiran chauffeur ba ya tuƙa motar har ɓangarensu Batool

Bayan ya isa bai ko jira iso ba ya kutsa kai ciki zuwa office ɗin headmaid, itace tayi masa jagora har ɗakin su Batool

Knocking headmaid tayi, Junnut ta buɗe tana faɗin “waye?”

Ganin Prince Sydeek tsaye ya sanya ta sadda kanta ƙasa tana faɗin “i’m sorry?”

“Ina Batool?” Ya tambaya

Cikin rawar murya Junnut tace “ta tafi ɗazu?”

“Ina!!!” Ya daka tsawa, dan zuciyarsa wani mugun tafasa takeyi

“Ban sani ba, Big Madam tace ta sallameta” ta faɗa a tsorace

A fusace ya juya zuciyarsa na harbawa da mugun gudu

“Ta manta ID card ɗinta!!!” Cewar Junnut cikin ɗaga murya

Dawowa yayi sannan yace “kawo”

Junnut ɗakin ta koma gamida ɗauko ID card ɗin Batool da taga komai na ta ya canza, launin idonta, sunanta amma dai kana gani kasan itace sannan ta ɗauko jakar kuɗin da ta bari

Miƙa masa tayi tace “wannan ma nata ne, Big Madam ta bata wai”

Prince Sydeek amsa yayi ya fice, a mota ya buɗe jakar yaga maƙil take da kuɗi, wato big Madam siyar da soyayyarsa tayi, rai ɓace yace “kaini sashen Big Madam”

Rai ɓace ya shiga ciki, a bedroom ya taddata tana ƙoƙarin kwanciya

Cilli yayi mata da jakar wajen ƙafafunta sannan yace “meyasa zaki koreta?!!” Rai a tsananin ɓace

Big Madam yunƙurawa tayi ta nufosa tace “Sydeek calm down, Batool liability kawai zata zamar maka”

A fusace yace “i love her, and kinsan taimakon da tayi min a duniya, ba dan ita ba da tuni na mutu, ba dan ita ba da na jima da rasa komai nawa, why are you so selfish”

Big Madam biting lips ɗinta tayi tace “whatever na biyata, meyasa ta ƙi ɗaukar kyautar da nayi mata?”

“Because she love me, ba kuɗi takeso ba, she risked her life several times to save me, kin ɗauka kuɗi shine komai?” Ya faɗa ransa a ɓace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button