SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

“Bakya ji na ne?” Cewar Junnut

“Ina jinki fa, Allah ya kaimu” na faɗa da smile kan fuskata……

S A R K I IS NOT FOR FREE
[11/9, 06:05] Mss Flower: ???? S A R K I

By Mss Flower????

SIMILARITIES OR RESEMBLANCE OF STORY/LIFESTYLE IS COINCIDENTAL

???????????? AFUWAN DURLINS NO MORE HARD TURANCI INSHA ALLAH

      *5&6*

Washegari da sassafe na shirya na wuce dining, Junnut na roƙa ta bani gurasa na kora da tea sannan na wuce coz lokacin breakfast bai yi ba

Babu kowa a compound ɗin hakan ya sanya na samu waje kan cement chair na zauna ina wasa da ƙafafuna idona kuma na kan ƙofofi biyu da na Prince Yar da na Prince Yameen

Na ɗan jima kafin naji an buɗe ƙofar sashi na tsakiya na Prince Yameen kenan, wata kyakyawar slim maid ce age of 20-22 haka ta fito idanunta sunyi jajur alamun ta sharɓi kuka and her clothes tattered (yagaggu), kallo ɗaya tayi min ta ɗauke kanta ta saka ƙasa sannan ta wuce

Cikin tausayawa nace “wanan Prince Yameen anyi azzalumi, wai ni shin haka Arabs ma suke saboda kana aiki a ƙarƙashinsu dole kayi enduring this kind of pains da rashin mutunci” murmushi n saki sannan nace Allah ya haɗamu da kai naci kan ubanka Yameen

Ina nan zaune ina saƙe saƙe na fara jiyo ƙashin perfume na Prince Yar, ban ɗago kaina ba sai na saka hannuna nayi tightening jikina alamun ina jin sanyi

“Me kikeyi this early morning?” Naji ya tambaya

Ɗago kaina nayi na saukesu a kan shi sannan na saki smile nace “na gaji da sashenmu ne shiyasa na fito nan”

Gyaɗa kai yayi sannan ya cire jacket ɗin jikinsa ya rufamin yace “kamar kina jin sanyi”

Idanuna na sauke saman nashi sannan nayi smile nace “nagode sosai”, gyaɗa kai kawai yayi ya wuce

Bayan wucewarsa da kallo na bisa ina tunanin anya zai iya cutar da mutum haka har yayi poisoning ɗinsa yanda yakeda kirki da tausayi, ɗan tsaki nayi nace “wancan Yameen ɗin yafi zama heartless ƙila dai wajensa zan fi focusing”

Bayan nagama dukkan aiyukana ɗaki na nufa, ɗaki na tadda Salamat da Junnut

Da fara’a Junnut tace “har kin dawo Batool”

Gyaɗa kai nayi ina zama kan gado nace “ya aikin”

“Alhamdulillah Habeebty” ta faɗa da murmushi

Maida kanta kan Salamat tayi tace “dan Allah Salamat kije kar ki jawo mana jangwal, tun ɗazu yake aikowa kiranki kinyi biris da shi” ta faɗa cikin damuwa

Ɗaga kaina nayi na kalli Salamat sai naga ko alamun taji abinda Junnut ke faɗi batayi ba, ɗan taɓe baki nayi na fara cire kayana dan shiga wanka

Junnut ta dubeni tace “Batool ni bari na koma kitchen sai anjima” ta ƙare tana miƙewa

Da murmushi nace “sai kin dawo” sannan na faɗa wanka

Ban wani ɗauki lokaci mai tsayi ba na fito, ina fitowa naji an banko ƙofa da ƙarfin gaske

Ƙuresa nayi da ido ina yaba kyawunsa kamar yanda shima yake bina da kallo musamman tudun ƙirjina, tunawa da nayi ɗan towel ke jikina nayi maza na juya cikin bathroom

“Wow” naji ya furta daidai lokacin da na tura kaina ciki

“Wannan shine Yameen dagani” na faɗa, kasa kunne nayi dan naji mai zasu ce da Salamat sai dai bai furta komai ba ya fice

Jin fitarsa ya sanya na fito nima, Salamat dake kan gado ta buga uban tsaki ta watsa min kallon banza

Ban tankata ba na fara shiryawa cikin baggy wando da riga sannan na tufke gashina na zubeshi baya, bacci na kwanta

Misalin huɗu naji ana tashina, miƙewa nayi da addu’a bakina sannan na dubi Junnut nace “har kin dawo”

Murmushi tayi tace “tun ɗazu kinata bacci, head maid ta turo kizo tun ɗazu, kiyi sallah sai kije” ta faɗa

Gyaɗa kai nayi nace “thank you”

Bayan nayi sallah na ci abincin da Junnut ta kawomin na ɗauki hanyar office na head maid

Da murmushi fuskarta yau tace “sai yanzu inata jiranki”

Murmushin na maida mata sannan nace “wallahi ina bacci ne”

Gyaɗa kai tayi sannan tace “dama zan canza miki post na aiki ne”

Gabana ne yayi mummunar faɗuwa dan babu wanda ya faɗomin a rai sai Prince Yameen da muka haɗu dashi ɗazu, way ɗin da ya kalleni nasan tabbas za’ayi hakan

“Kina ji na?” Cewar head maid

“Sure ma’am” na faɗa

“Yawwa, side ɗin Prince Yar zaki koma wajen matarsa Princess Zairah ɗazu ta aiko tana buƙatar kyakyawar maid and kece zaɓina” ta faɗa da fara’a a fuskarta

Ajiyar zuciya nannauya na sauke sannan nayi murmushi nace “okay ma’am, nagode”

“Yawwa yanzu kije wajenta tana jiranki” ta faɗa

Gyaɗa kai nayi sannan na fice

Da sallama bakina na tura bedroom ɗinta bayan wata maid tayi min iso, ƙaton bedroom ne wanda sai an haɗe ɗakinmu biyar sannan zaiyi girmansa

Ɗago kyakyawar fuskarta tayi ta kalleni sannan tace “sannu da zuwa”

Murmushi nayi ina mamakin kirkinta unlike sauran jinin sarauta da suke da jin kai da izza

A sanyaye nace “nice sabuwar maid da aka aiko”

Murmushi tayi sannan tace “mene sunanki?”

“Batool ne” na bata amsa

Gyaɗa kai tayi sannan ta ɗan taɓe baki tace “nice name”

“Thank you” na bata amsa

Miƙewa tayi sannan ta tako har inda nake da fara’a a fuskarta ta ɗago haɓata tana kallon ƙwayar idona

Zuciyata bugawa ta farayi da gudun bala’i sai a lokacin na tuna cewar maid akan kishin mijinta da takeyi mai tsanani, zuciyata ta gama yankewa da cewar kan issue ɗin mijin nata ne ta nemoni dan ta ci min mutunci

“You are beautiful” ta faɗa tana ɗora babban yatsanta kan lips ɗina ta ɗan murza

Yawu na haɗiya dan bansan abinda zan ce ba

Murmushi ta kuma yi sannan tace “kinsan mene aikinki?”

Girgiza kai kawai nayi

Murmushi tayi ta cikani sannan tace “serving ɗina sannan hakan ya zama sirri tsakaninmu, na rantse da Allah duk wanda yaji batun muna mu’amala dake sai na kasheki”

Cikin tsananin tashin hankali nace “bangane mu’amala ba, wani aiki ne hakan?”

Murmushi ta saki sannan ta fizgoni jikinta ta haɗe bakinmu, da ƙyar na raba kiss ɗin zuciyata na azalzala dan ji nake kamar na shaƙeta na kashe in akwai abinda nafi tsana a rayuwa bai wuce tarayyar jinsi ɗaya ba

Murmushi ta saki sannan tace “wannan nake nufi Batool, sannan dole ki amince da hakan dan in ba haka ba kisa ne hukuncinki, zaki iya tafiya”

Cikin tsananin tashin hankali da firgici na fito ina jimamin da taraddadin bala’in da na jefa kaina babu gaira ba dalili na zaɓi aikin bincike ina mace gashi na shigo masarautar hatsabibai

A ruɗe na kutsa ɗaki ina baza idanu, Junnut da ke zaune tayi saurin miƙewa ta tarbeni tana faɗin “kin dawo, Batool mun shiga uku naji ance ke aka turawa Princess Zairah”

A tsorace na dubeta nace “mene da Princess Zairah ɗin”

Waiwayawa tayi sannan ta kamani muka zauna kan gado, chan ƙasan murya tace “Batool personal maids uku da aka kai mata sashenta duka kashesu akayi, kuma kema gashi an turaki matsayin personal maid, akwai ƁOYAYYEN SIRRI dangane da wannan sashe”

Duk da zuciyata na cikeda tsoro, na saki murmushi tareda riƙe hannun Junnut nace “i will be alright”

Ƙwalla ce ta sauko mata tace “ina jinki kamar ƴar uwata Batool duk da bamu daɗe da haɗuwa ba, bana son wani abu ya sameki”

Rungumeta nayi nace “kar ki damu, i’m strong, ba abinda zai faru”

Gyaɗa kai tayi tace “please becareful” ……

S A R K I IS NOT FREE
[11/9, 06:05] Mss Flower: ???? S A R K I

By Mss Flower????

SIMILARITIES OR RESEMBLANCE OF STORY/LIFESTYLE IS COINCIDENTAL

☀️FIRST CLASS WRITERS ASSO….

       *9&10*

Washegari bayan na gama cin abinci na huta na nufi sashen Prince Yar, bamu haɗu da shi ba kasancewar yau ban fito da wuri ba

Direct ɗakin Princess Zairah na nufa na shiga

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button