SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

Ko da na koma takaddun na gani a hannun Prince Sydeek yana dubawa, bayan ya gama ya gyaɗa kai tareda ajiyesu a gefensa ya dubi Prince Yar yace “sannu da ƙoƙari”, murmushi Prince Yar yayi yace “komai nayi maka ban faɗi ba, yi wa kaine”, sun ɗan taɓa hira kana Prince Yar yayi masa sallama ya fice

Prince Sydeek ɗaukan takaddun da idona ke akansu yayi sannan ya shiga ɗaki da su, ya ɗan jima kaɗan ya sake fitowa riƙe da su kana ya zauna kan dinning ya ci abinci sannan ya tashi ya bar takaddun a nan

Bayan na tattare komai zama nayi nai jugum, ina ta tunanin shin na ɗauko masa ko karna ɗauko masa, tabbas idan ban kai masa akwai gaggarumar matsala domin ace aikin farko da ya sani na kasa aikatawa ai hakan zai sanya masa waswasi a ransa, kafin na kwanta dai na canza musu muhalli zuwa drawer ɗin tv stand, kuma na yanke hukuncin zan kai masa takaddun sai dai daga baya zanyi dukkan ƙoƙarina wajen dawo da su. A parlorn nayi bacci sai dai yau ban samu arziƙin bargo ba, daɗina ma babu sanyi chan a yau ɗin, washegari bayan na kammala komai, na shirya masa abinci sannan na ɓoye envelope ɗin na fice a sace, ko da na isa ɗaki ɓoyesu ƙasan gado nayi

Misalin takwas na dare na fita wajen da nakeda tabbacin zan ga Prince Yar, kamar yanda nayi tsammani yana wajen a zaune, da fara’a ya tarbeni, batareda nace masa komai ba na miƙa masa envelope ɗin, cikin jindaɗi ya amsa yana faɗin “well done Batool”, bai wani ɓata lokaci ba yayi tafiyarsa cikin murna, bayan wucewarsa ajiyar zuciya na sauke nace “ka daina murna dan sai na amso su”

PRINCE YAR POV

Da tsananin farinciki ya shiga parlor, Princess Zairah dake zaune ta miƙe tana faɗin “what’s so good today?”, murmushi ya saki sannan yace “we are taking Prince Sydeek down” ya ƙare yana ƙarasawa wajen chimney (wutar da ake hurawa a ɗaki) sannan ya cilla envelope ɗin baki ɗaya, sai da ta ƙone ƙurmus ya saki ajiyar zuciya, Princess Zairah dake gefensa tace “ai da ka ajiye ba ka ƙona ba”, girgiza kai yayi yace “ba zan iya fitowa nace na ƙwace dukiyarsa ba, so i will just be destroying every piece of his wealth” ya ƙare da murmushi

BATOOL POV

Jikina duk a mace na tura ƙofar apartment ɗinsa, tsaye na gansa a parlor yana kaiwa da kawowa, jin na shigo sai ya juyo ya tattare hankalinsa baki ɗaya ya zuramin ido, kaina na sunkuyar ƙasa zuciyata na bugawa da sauri sauri, a hankali ya tako daf dani, jaa da baya nayi, haka mukayi tayi har na kai bango, yawu na haɗiya sannan nace “me…me…mene?” Ina zaro ido cikin tsoro, banza yayi da ni na sakanni sannan yace “kin kai masa?”, a ɗan tsorace nace “me?”, tsuramin ido yayi sannan yace “takaddun”

Cikin firgici nace “eh…eh amma zan amso”

Gyaɗa kai kawai yayi sannan yayi baya ya bar wajen haɗe da shigewa ɗaki, tunda ya shiga bai sake fitowa ba har bacci yayi gaba dani bayan lokaci mai tsayin da na ɗauka ina tunani…..

SARKI IS NOT FREE ITS 300 VIA 1401611541, FATIMA LAWAL SAID, ACCESS BANK, OR MTN CARD TO 08167888934
[11/14, 1:51 PM] Muslima????: ???? S A R K I

     *51&52*

Washegari ina idar da sallar asuba naga Prince Sydeek ya fito hankalinsa a matuƙar tashe dan ya bayyana ƙarara kan fuskarsa

Da hanzari na miƙe ina faɗin “meya faru da kai?” Dan a tunanina wani abun Prince Yar ya aikata masa dalilin takaddun da na kwasa na kai masa

Bai tankani ba ya fice cikin sauri fuskarsa babu walwala sai tsantsar tashin hankali

“Allah ya sawwaƙa” kawai na faɗa sannan na zauna ina tasbihi har haske ya keto, daganan kitchen na koma na ɗora masa breakfast bayan na gama na kimtsa gidan sannan na wuce sashenmu

Tun fitowata na kula kamar masarautar a hargitse take domin duk inda na kalla cincirondon ma’aikata ne tsaye suna ƙusƙus, haka na ƙarasa ɗaki cikeda tunanin mai yake faruwa haka

Junnut na gani na ta miƙe tana faɗin “dagaske wai his majesty jikinsa yayi tsananin da baya gane wa ke kansa”

Rasss naji gabana ya faɗi babu dalili, ɗan jim nayi sannan nace “ohh shine babu lafiya?”

“Wai baki sani ba?” Cewar Junnut cikin mamaki

“Eh, sai yanzu naji, Allah ya bashi lafiya” na faɗa a sanyaye

“Ameen” ta amsa

Haka muka zauna jugum babu abin cewa daga ƙarshe Junnut ta yafitoni tace “zo ki ji”, matsawa nayi na hau gadonta, chan ƙasan murya tace “ke fa ance cutar da ta kashe matar shi ta farko itace ke damunsa, kawai dan shi ya ɗauki lokaci mai tsayi ne, zancen gaskiya ni fa gani nake kamar mutuwa zaiyi Batool dan ance jikinsa yayi tsanani ya ruɗe”

“Allah ubangiji ya bashi lafiya” na faɗa a sanyaye

“Ameen, wa kike ganin zai hau kujera in ya rasu, Batool ba fa fata nake masa ba wai misali” cewar Junnut da nasan curiosity ne kawai ke damunta

“A’a bansani ba wannan kam” na faɗa a taƙaice

“Allah ya sanya Prince Yar shi zai hau, yanada kirki da tausayi na tabbata zai yi mulki mai adalci, amma kinga Prince Sydeek ya fiya izza, ɗagawa da girman kai bai damu da rayuwar kowa ba sai ta sa, shikuma Prince Yameen dama kinsan ya ɓata rawarsa da tsalle” ta faɗa chan ƙasa

“Hmmm” kawai nace ban furta komai ba

Bayan mun gama wannan zancen gado na hau dan bacci sai dai na gaza dan duk tunanina ya karkata kan Prince Sydeek, tunanin halin da yake ciki ya min tsaye cikin rai, tausayinsa nakeji ainun dan na kula gabaɗayansa anyi sorrounding ɗinsa da maƙiya ne

Misalin biyu na koma sashensa sai dai babu alamun an ko shigo ciki bare taɓa abinda na girka, tattare komai nayi sannan na zauna parlor ina kallo

Prince Sydeek ba shi ya shigo ba sai misalin shida, ina ganinsa nagansa a hargitse dan har ƴar rama yayi kaɗan ina dai da tabbacin bai sanya komai a bakinsa ba

Yana ƙoƙarin shiga ɗaki na sanya hannu na riƙesa nace “dan Allah mai yake damunka?”

Tsuramin ido yayi sannan yace “zan rasa katangar da ta ragemin, tsoro nake ji Batool, ya zanyi ne?” Idanunsa sun kaɗa sunyi ja

Wani tsananin tausayinsa naji ya kamani, jan hannunsa nayi har kan kujera kamar ƙaramin yaro haka ya zauna, cikin muryar tausayawa nace “ka kwantarda hankalinka, dukkan abinda ya faru rabbi ya tsara ne tuntuni, damuwa, tashi hankali ko ɓacinrai basu isa su canza wani abu ba daga abinda ubangiji ya tsara, kayi ta masa addu’ar samun sauƙi insha Allah sai rabbi ya amsa ya zaɓa masa alkhairi”

Ɗan nisawa yayi yace “bani da kowa sai shi Batool, nayi niyyar daga ranar da na rasa shi zan jingine masarautarnan na barta amma ya ɗaura min nauyi yace ya barta hannuna amana!, Batool ba zan iya ba, fatana ya warke kada ya tafi ya barni cikin wannan hargitsatsiyar masarautar, nagaji haka, rayuwa nakesonyi mai daɗi cikin kwanciyar hankali”

Cikin tausayawa nace ” ka kwantarda hankalinka insha Allah komai ya faru da kai alkhairi ne, kuma zakayi rayuwa irin wadda kakeso insha Allah” na faɗa

Bai ce komai ba sai kauda kansa da yayi daga dubana ya jingina da jikin kujera kana ya lumshe idannunsa

“Na kawo maka abinci?” Na tambaya

“Ba zan iya cin komai ba” ya faɗa a taƙaice

Ban tankasa ba na miƙe na nufi kitchen, spaghetti na dafa masa ruwa ruwa, ko da na fito tsaye na gansa ya canza shiri yana shirin fita

“Ina zaka?” Na tambaya

“Zan koma wajensa ne” ya faɗa a taƙaice yana ƙoƙarin buɗe ƙofa

Cikin sauri na zura takalmina haɗe da riƙe flask ɗin na bi bayansa, bai tsaya ba duk da yasan ina biye da shi sai da ya kai bakin ƙofar mota

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button