SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

Chan na miƙe tareda nufar sashensa, sai da nayi adduoi kafin na tura ƙofar

Zaune nagansa a parlor shida wata maid tayi baje baje kan cinyarsa yayinda hannunsa na cikin rigarta sai ƙyalƙyala dariya takeyi

Taɓe baki nayi tareda kauda kaina sannan nace “Malam bani wayata”

Zare budurwar yayi daga jikinsa sannan yayi mata raɗa a kunne, dariya ta ƙyalƙyale da ita sannan ta miƙe ta fice, naji kamar ta ɗauki wani abu amma bansan ainahin abinda ta ɗauka

Tana fita naji alamun saka makulli alamun an kullemu a ciki

A fusace zuciyata har zafi take nace “wani irin iskancine wannan?”

Murmushi yayi sannan ya miƙe ya shige ɗaki yana faɗin “zo ki amshi wayar”

Na jima a tsaye a wajen, zuciyata sai tafarfasa takeyi haɗe da danasanin zuwa

Ganin tsayuwar ba zata fishsheni ba ya sanya na miƙe na shiga ɗakin, kwance yake kan gado ya bararraje

Raina a ɓace nace “bani wani makullin zan tafi, ka riƙe wayar”

Dariya yayi sannan yace “zo ki min tausa to”

Wani mugun kallo na watsa masa sannan nace “ban cika son magana da wanda bai da ƙwalwa ba, Malam buɗemin ƙofa!!” Na ƙare cikin tsawa

A fusace ya miƙe yana faɗin “kinsan meyasa nayi rantsuwar sai na shigeki, saboda bakida kunya nikuma ina son naga ƙarshen fitsararki” ya ƙare haɗe da fizgoni ya wullani kan gadon tareda danneni

Cikin ƙarfi ya fara kiciniyar rabani da kayan jikina

Ganin ya danneni banida ƙarfin kai naushi ko duka ya sanya na kafawa damtsen hannunsa haƙorana, ƙin cikawa nayi duk da ihu da roƙona da yakeyi na sakesa

Lokacin da na sakeshi har jini ya fito

Cikin sauri ya jaa baya ya fara yarfe hannu ganin hakan ya sanya nayi maza na ɗauki kwalbar giyar da ke kan bedside drawer ɗinsa na fasata nan take ta zame min makami

Nufarsa nayi gadan gadan tareda ɗaga kwalbar kamar zan daka masa

Ihu ya saki yana faɗin “wai ke mahaukaciya ce”

“Da alama baka san hauka ba, dan ban riga nayi maka shi ba” na ƙare ina tura kwalbar kusada cikinsa

“Ke duba drawer akwai wani makullin, amma kar ki cakamin” ya faɗa jikinsa na ɓari

“Lusarin banza, bani wayata!” Na faɗa ina miƙa masa hannu

Hannu ya saka ya ɗauko tareda miƙomin jikinsa na ta rawa

“Wai ni daa kai mace ne ma kakeson min fyaɗe, sai ka sake sabon shiri dan na riga naga wallenka” na ƙare ina buɗe ƙofa

“Ƴar daba!” Ya faɗa

Dariya ce ta ɗan suɓucemin sannan na wuce dan buɗe ƙofar

Bayan na fito waje na samu kan dandamali na zauna, buɗe wayar nayi dan kiran Mom sai dai banga network ya kawo ba, ko da na buɗe wayar sai naga babu sim

“Innalillahi wa’ina ilaihi raji’un” na faɗa dan ko karen hauka ne ya cijeni bazan kuma komawa sashen Prince Yameen ba

Miƙewa nayi na koma ɗaki, zaune naga wata mata itada Junnut a ɗakin

Junnut na gani tace “ya rabbb, ina kika shige tun ɗazu an turo ana nemanki”

Kallon matar nayi da ke sanye da kayan maids amma na ɓangaren wajen sarki, sannan na maida kaina kan Junnut nace “wa ke nemana?”

Matar ce tace “Big Madam ce”

Gyaɗa kai nayi sannan nace “muje” bayan na sakaɗa wayata ƙasan pillow

Mota muka nufa, ganin mota yasanya nace “dan Allah baiwar Allah ina zaki kaini?”

Da mamaki tace “Big Madam ke nemanki”

Shiru nayi sannan nace “shine sai mun shiga mota, ɗan chan ɗin” na faɗa cikin rashin yadda

“Ohh ba fa Madam ba, kakarsu Prince Sydeek nake nufi” ta faɗa tana shigewa ciki

Shiga nayi jikina a sanyaye, tafiya kaɗan ce ta kaimu

Matar ce tayi min jagora har wani babban parlor sannan tace “ki zauna a nan, bari nayi mata magana”

Jim kaɗan sai ta dawo tace “ki jira gata nan” ta fice

Na jima a wajen dan har na soma gyangyaɗi sannan dattijuwar matar nan wadda gani kasan ta manyanta amma hutu da jindaɗi ya ɓoye tsufanta ta fito ta zauna

Dubana tayi tace “Batool ko?”

Da mamaki nace “eh”

“Kinsan meyasa na kiraki?” Ta tambaya

“A’a” na bata amsa a taƙaice

Dubana tayi sosai sannan tace “akan Prince Sydeek ne, da farko dai meya sameshi ya bar masarauta kuma yayi ɓatan dabo, ina yaje?” Ta tambaya

“Bashida lafiya ne” na bata amsa

“Poison ko?” Ta tambaya

“Eh” na bata amsa

“Bawan Allah, meye haɗinki da Prince Yar?” Ta tambaya tana ƙureni da ido

A ɗan razane na kalleta sannan cikin daburcewa nace “bakomai”

“Kar ki min ƙarya, ina da bayani akan ya rufeki, mai yayi miki, wani shiri ku ka ƙulla?!!” Ta faɗa ranta a ɗan ɓace

Cikin rawar murya nace “kiyi haƙuri bazan iya faɗa ba” na faɗa idona na kawo ruwan da bansan dalili ba

“Meyasa?” Ta tambaya

“I think i’m under hypnosis” na faɗa hawaye na ɗan zubarmin

“So, your mind is trapped right now?” Ta tambaya

Gyaɗa kai nayi kawai batareda nace komai ba

“Meyasa yayi trapping ɗinki?” Ta tambaya

“Bansani ba” na faɗa a sanyaye

“Mai ne haɗinki da Prince Sydeek?” Ta tambaya

“Maid ɗinsa ce” na bata amsa

“Wani irin zama kukayi da shi?” Ta kuma tambaya

“Na aminci, sai dai ya cutar da ni bayan na taimakesa” na faɗa kaina a ƙasa

“Batool!!!” Ta faɗa

Ɗago kaina nayi na ɗan kalleta sannan na maida ƙasa ina jin kaina ya fara ɗan sarawa

“Ɗago kanki ki kalleni, in har kina son fita daga wannan trap ɗin nan ke kaɗai zaki iya taimakon kanki, we need you dan haka help yourself” ta faɗa

Kallonta na sakeyi cikin rashin fahimta

“Look at me in the eyes!!” Ta faɗa

Ɗago kaina nayi na kalleta cikin ido

“Prince Sydeek baiyi betraying ɗinki ba, you are trapped get yourself out of this cage, this kingdom need your help” ta faɗa tana ɗora hannunta bisa kafaɗata

Ƙoƙarin ɗauke kaina nayi dan sai naji ƙwalwata ta fara juyawa, kaina ya fara ciwo

Hannu ta saka sannan tace “don’t break the eye contact, Prince Sydeek bai cuceki ba, think!!!” Ta faɗa da ɗan ƙarfi

Wani irin bugu da sara naji kaina nayi yayinda ƙwalwata ta fara tariyo min wasu hotuna, hoton Prince Sydeek da ke tsaye lokacin da ake turani a mota ya fara fading, wani sarawa kaina keyi yana barazanar tarwatsewa

“Prince Sydeek bai cutar dake ba, try to get yourself out of the cage!!, think Batool!, think!!!!” Ta faɗa

“Ahhhhh” na faɗa cikin azaba tareda ɗora hannuna bisa kaina na dafe dan wani irin ciwo yake min

“Prince Sydeek was sick, he couldn’t stand properly Batool, ta ya zai cutar da ke yana wannan halin” ta faɗa

Bakinta kawai nake kallo kaina na barazanar fashewa, amma tabbas hakane baya ko iya tsayawa, a wheelchair muka kaisa mota, take hoton komai ya tariyomin ya dawo ƙwalwata yanda yake

Zubewa nayi ina sauke numfashi tallabe da kaina haɗe da rintse idona

Matar da kanta ta tashi ta ɗebo min ruwa ta kawo min tareda faɗin “ga ruwa ki sha”

Cikin sauri na miƙe tareda amsa tuni na fara kwankwaɗa

“Kin tuna komai yanda yake?” Ta tambaya

Ban amsata ba har nagama sha sannan na sauke kofin, a galabaice nace “na tuna”

Murmushi tayi sannan ta riƙe hannuna tace “zaki taimakawa masarautarnan ko, zaki taimakawa Prince Sydeek ko?” Ta tambaya idonta a kaina

Shiru nayi sannan na lula tunanin ya Prince Sydeek yake, yana lafiya ko akasin haka

“Batool!, ki taimakemu idan masarautarnan ta faɗa hannun Yar zamu yi asara matuƙa, the king is almost no more, bashida lafiya ainun, ban ankare suna son kasheshi ba ne sai da lokaci ya ƙuremin, ba zan iya taimakonsa ba, amma zamu iya taimakon kujerarsa together!” Ta faɗa tana matse hannuna haɗe da gyaɗa min kai

Shiru nayi dan bansan mai zance mata ba, tunanin fecewa daga masarautar nake ko kuma na tsaya na taimakesun kamar yanda tace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button