SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

S A R K I IS NOT FOR FREE IS 300 VIA 1401611541 FATIMA LAWAL SAID, ACCESS BANK AND THEN SCREENSHOT TO 08167888934

Or mtn card to 08167888934

IDAN BA SUBSCRIBING ZA KI YI BA KAR KI BIYONI

[11/12, 5:14 PM] Muslima????: LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI, NAIRA 300 KACAL TA ASUSUN 1401611541, FATIMA LAWAL SAID, ACCESS BANK, SAI KI YI SCREENSHOT ZUWA 08167888934, KO KUMA KATIN MTN ZUWA 08167888934

S A R K I

         *31&32*

Ko da suka sa ni a mota kafin mu isa bansan inda kaina yake ba

Na kwashi lokaci mai tsayi ina bacci dan har haske ya fito kafin na buɗe idona cikin kasala, kaina wani mugun ciwo yake kamar zai tsage

Ƙoƙarin motsawa nayi, sai a lokacin na kula da dukkan jikina a ɗaure yake ram da igiya, ina zaune bisa kujera, cikin rashin jin daɗi nace “ya rabbb, ka taimakeni”, wajen kamar garage ne babu komai sai ƙarafa, gashi da mugun sanyi kamar freezer

Na ɗauki lokaci mai tsayi ina a haka kafin naji ƙarar buɗe ƙofa, a galabaice na kai idona kan ƙofar

Wani sundumemen ƙato ne ya shigo sai muzurai yake hannunsa riƙe da robar abinci ya nufo ni

Kauda kaina nayi dan wani irin baƙin ciki ne ke ci na

“Ga abinci” ya faɗa yana ɗebowa haɗe da ƙoƙarin kai cokalin bakina

“Ba na ci” na faɗa ina kauda kaina gefe, ƙwalla na tsiyayowa bisa kuncina

Hannu ya sanya ya ɗaukeni da mari mai zafin gaske sannan ya damƙi gashina ya ɗago kaina ya na faɗin “dole ki ci dan ubanki”

Damtse bakina nayi duk da tsananin azabar da nakeji kaina na min

Dariya ya saki sannan ya cikani yace “kanki kika cuta yarinya” ya faɗa yana komawa gefe ya fara cin abincin

“Dan Allah ka sakeni bawan Allah” na faɗa muryata har rawa takeyi

Dariya ya kece da ita sannan yace “ai ba ni na riƙe ki ba baiwar Allah”

Bayan ya gama cin abincin miƙewa yayi ya fice tareda saka kwaɗo a gate ɗin

Wasu hawaye ne suka saukarmin masu mugun zafi, nayi hawaye sosai sannan nace “ya Allah ka kawomin mafita”

Wata iriyar ƙishirwa nake ji, kasala, ciwon kai, tunanina duk ya karkata kan neman hanyar da zan bi na bar wajen nan sai dai banida hali, domin a ɗaure nake ram da kujera

Na galabaita ainun dan na ɗauki tsawon awa huɗu a haka kafin naji ana buɗe ƙofa

A galabaice na kai dubana kan fuskarsa, ɗauke kaina nayi ina jin wata muguwar tsanarsa a raina

Murmushi ya saki ko da ya ƙaraso gabana sannan ya ɗan ranƙwafo tareda ɗago haɓata yace “you look sad Batool”

Wasu hawaye naji na ƙoƙarin zubomin, cikin dauriya na maida su sannan nace “mai kakeso da ni?”

Murmushi yayi yace “Batool bana son ganinki cikin damuwa, please ki daina wannan baƙincikin, just tell me ina Prince Sydeek yace miki zai je, ya kamata ya ƙarasa shan dose na maganinsa ko?” Ya ƙare yana ɗaga min gira haɗe da sakin wani killer smile

Nima murmushin nayi a galabaice sannan nace “har abada bazaka taɓa nasara ba, mugu a koda yaushe a ƙasa yake baya taɓa yin sama”

Ɗan ɓata fuska yayi sai kuma ya saki murmushi yace “Batool why are you so stubborn, ki daina ƙoƙarin ɓata min rai mana” ya ƙare yana shafa gefen fuskata

Cikin baƙin ciki na juyar da kaina sannan nayi shiru, ina jin wani mugun raɗaɗi a zuciyata

Wayarsa ce tayi ƙara, tashi yayi sannan ya ɗauki wayar

Wani irin tsananin ɓacin rai da baƙinciki ne ya bayyana a fuskarsa, ya ɗauki lokaci yana wayar kafin yace “sun ƙone wajen duka?”

Bansan mai aka ce ta ɗayan ɓangaren ba sai dai cikin fushi Prince Yar yace “ka tabbatar duka ma’aikatan sun gudu”, gyaɗa kai kawai yayi bayan an bashi amsa ya datse kiran

Cikin tsananin ɓacin rai ya juyo, kallona yake cikin ɓacin rai, fuskarsa har jaa tayi

Murmushi ya saki sannan yace “Batool kece?”

Ɗago idona kawai nayi na zubesa a kansa batareda na furta komai ba

Wata iriyar zabura yayi tareda shaƙe wuyana yace “kece kika jawo min asara?”

Cikin tashin hankali na fara juya kaina dan matsar da yayi min kamar zai ɗauke numfashina idona sunyi waje, cikani yayi nan na fara maida numfashi

Sai da na ɗan huta sannan nace “dan Allah ka cikani, bansan komai ba, na roƙeka”

“Ƙarya kikeyi Batool, kece da haɗin bakin Sydeek ku ka cutar da ni, kinsan irin asarar da kika ja min, wallahi bazanyi asara ba dukkanmu zamuyi ta, kun ci wasan dan yanzu amma yanzu zamu shiga wasan gaske”

Cikin tashin hankali nace “dan Allah ka kwanceni, bansan komai ba”

Murmushi yayi sannan yace “Sydeek zan so ka rayu dan muyi wasa mai muni” a fusace ya juyo ya kalleni sannan yace “Batool ke ce ƙwallon wasan” ya ƙare yana ficewa

Murmushi nayi nace “nasara ta ɗaya, ta biyun saura a kama ka” na faɗa a galabaice…..
[11/12, 5:14 PM] Muslima????: LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI, NAIRA 300 KACAL TA ASUSUN 1401611541, FATIMA LAWAL SAID, ACCESS BANK, SAI KI YI SCREENSHOT ZUWA 08167888934, KO KUMA KATIN MTN ZUWA 08167888934

S A R K I

         *33&34*

Bayan fitarsa wani ne ya kawomin abinci, babu yanda na iya haka na dinga amsar abincin ba dan raina na so ba sai dan tsananin yunwar da nakeji

Bayan ya gama bani ya fita, jim kaɗan sai gashi ya dawo shi da wata mata sanye cikin uniform irin na palace maids

Da taimakonta na shiga toilet nayi wanka sannan na shirya cikin wata doguwar riga

Cikin kalar tausayi nace “dan Allah baiwar Allah ki taimaka min na bar wajen nan, ki dubi Allah da manzonsa ki taimakeni”

Jim ta ɗanyi sannan cikin muryar tausayawa tace “dan Allah kiyi haƙuri tabbas da inada hanyar tausaya miki da nayi amma bazan iya ba, idan nayi hakan zan cuci kaina na jefa ahalina cikin mawuyacin hali, kiyi haƙuri” ta faɗa tana dafani

Wasu siraran hawaye ne suka zubomin sannan na ɗaga kaina nace “toh, nagode amma dan Allah mai kike tunanin zasu yi min?”

Shiru tayi sannan tace “kinga dai bansan abinda kikayi musu ba gaskiya, amma dai zancen gaskiya kiyi ta addu’a kawai, Allah zai kawo miki ɗauki”

Gyaɗa kai nayi nace “tabbas addu’ar mumini bata faɗuwa ƙasa”

Sai da na gabatar da sallolina duka na kuma sha ruwa mai yawa sannan muka koma aka kuma ɗaureni kamar huhun goro

Misalin takwas da rabi na dare Prince Yar ya shigo wajen fuskarsa ɗauke da murmushi

Kujera ya janyo ya zauna gabana muna facing juna sannan yace “kinyi kyau Batool”

Taɓe baki nayi nace “ban taɓa ganin muninka kamar yau ba Yar”

Murmushi ya saki yace “ina son jarumtarki, tun farko ita ta sanya na zaɓeki”

“Wai dan Allah mai kakeso dani ne, dan Allah ka ƙyaleni, na faɗamaka banida saka hannu a duk abinda kake zargi, ni banyi komai ba” na faɗa cikin damuwa

Murmushi ya saki sannan yace “Batool aiki zaki min”

“Aikin!, aikin me?” Na tambaya cikin ƙosawa

“Na rasa komai na kuma silar Prince Sydeek dan ina sane da duk wani bin diddiƙi da yake min, na ƙyaleshi ne dan naga gudun ruwansa”, bai ƙarasa ba na katsesa nace “tau, ka ga gudun ruwan nasa ni ka ƙyaleni haka”

Dariya yayi sannan yace ” da ke zanyi amfani wajen kassara shi kafin na kauda shi, yanzu nafi son ya ɗanɗani baƙin cikin asara kafin ya bar duniya”

“Ba zan taimaka maka ka cuci wani ba, ni ka ƙyaleni” na faɗa ina masa mugun kallo

Murmushi yayi sannan yayi ma wani nuni da waje

Babu jimawa mutumin ya dawo da tray a hannunsa, kaskon turaren wuta ne a kai sai wani hankici fari

Amsa yayi ya buɗe hankicin, nan wata baƙar hoda ta bayyana

Cikin rashin sanin meye a hannunsa nace “mene wannan ɗin?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button