SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

Murmushi tayi ta gyaɗa kai sannan tace “za ki iya tafiya”

Ɗaya daga cikin kwanukan abincin his majesty na ɗauka wanda farar shinkafa ce kawai a ciki, tura akwatin ciki nayi na birne da shinkafar sannan na ɗauki flask ɗin

Big Madam gyaɗa min kai tayi, nima na maida mata kana na wuce waje

Ina fitowa Madam tace “ya jikin nasa?”

Kaina a sunkuye nace “sai addu’a”, tunawa da nayi na hangi hankeys a balcony ɗin wajen nace “ya ɓata hankeys da dama da jini sai da na wankesu sosai suka fita”

Ajiyar zuciya bayananniya ta sauke sannan tace “yawwa”

Ina ƙoƙarin wucewa Princess Zairah tace “mene a flask da zaki fita da shi?”

Gabana ne yayi muguwar faɗuwa, dakewa nayi na juyo nace “abinci zan dafo masa”

“Wani abinci ne da babu shi a nan, sai kin je sashen gida?” Ta faɗa tana nufoni

Kasa magana nayi sai addu’a na fara karantowa ta Allah ya hayar da ni

Hannu ta sanya ta buɗe flask ɗin, tana ƙoƙarin karɓa a hannunta Prince Sydeek da Yar suka ƙaraso

“Lafiya?” Cewar Prince Yar yana kallonmu yayinda Prince Sydeek ya kafemu da ido

“Big Madam ta aikeni na yi ma his majesty porridge shine Princess Zairah ta tsaida ni” na faɗa cikin sauri

Wata tsawa Prince Yar ya daka mata sannan yace “kina hauka ne, dallah cire hannunki, bata murfin taje”

Amsa nayi na rufe sannan na wuce, ajiyar zuciya na sauke ko da na kai ƙofa nace “Alhamdulillah”

Chauffeur ɗinsa ne ya kaini har apartment ɗinsa, bayan na fito nace “ka jirani dan Allah zan koma”

Cikin gidan na shiga na nufi baya da ƙasa ne a wajen da flowers sai shukoki, rami na haƙa mai zurfi kana na ciro envelope ɗin da take cikin bumbag ɗita na naɗeta na buɗe akwatin da ke ɗauke da wani expensive polished gold seal na turata ciki na datse akwatin na binne, sai da na tabbatar nayi labelling ƙasar wajen kana na janyo wani ƙaton dutse na mirginasa a wajen, sannan na karkaɗe hannayena da jikina na fice

Kitchen na shiga na haɗa masu ginger tea, sanan nayi frying plantain nayi warming liver sauce na haɗa a flasks sannan na fice bayan nayi sallar isha’i, har na kai ƙofa na dawo na ɗauko ƙaton blankets guda biyu sannan na koma muka wuce

Ban tadda kowa a parlor ba alamun sun nuna duk suna ciki, waje na samu na zauna ina jin yanda sanyi ke shigata

Na jima ƙwarai a nan kafin aka buɗe ƙofa, nan Prince Yameen, Madam, Princess Zairah, Prince Yar suka fito

Harara Princess Zairah ta watsamin tace “ƴar shishigi”

Prince Yar da ya kafeni da ido yace “har kin dawo?”

“Eh tun ɗazu” na bashi amsa

“Okay, shiga ki basu, Allah yasa zai ci, bari naje nima yanzu zan dawo” ya faɗa

Gyaɗa kai nayi sannan na dubi wajen mutannen nace “sai da safenku”

Babu wanda ya tankani sai Prince Yameen da yace “ƴar daba” chan ƙasan murya

A hankali na kwashi kayan na tura ƙofar ɗakin, kallona dukkansu kawai sukayi sannan suka maida hankalinsu kan mai jinyar

Ban tanka kowa cikinsu ba nayi serving abincin plates biyu sannan na zuba tea ɗin, Big Madam na fara miƙawa

Ɗan yatsina fuska tayi tace “ba zan iya cin komai ba”

“Dan Allah ko kaɗan ne ki ci” na faɗa a sanyaye

Amsa kawai tayi ta fara ci kaɗan kaɗan

Prince Sydeek na kuma nufa sannan na miƙa masa nace “ga shi”

Girgiza kai kawai yayi alamun ba zai ci ba

“Dan Allah ko ya ne ka ci, baka ci komai ba dan Allah ka amsa wannan” na faɗa ina addu’ar ya amsa

Ɗan yamutsa fuska yayi kana ya amsa

Sun ci sosai dan Big Madam har ta kusan cinye plate ɗinta yayinda Prince Sydeek ya ci rabi ya kuma shanye tea ɗin

Sosai na ji daɗin hakan kuma, bayan sun gama na tattare kwanukan na ajiye a gefe

Ganin dare ya fara yi sosai na miƙe na ɗauko blankets ɗin biyu na bawa kowannensu ɗaya sannan na koma gefen kujera na zauna ina rawar sanyi

An jima sosai sannan Prince Yar ya shigo, zama shima yayi babu mai cewa komai

Ganin da nayi bacci na neman cin ƙarfina ya sanya na miƙe na koma parlor na kwanta kan doguwar kujera, duƙunƙunewa nayi na cure har bacci yayi gaba da ni

Ina cikin bacci naji ana rufeni da abu mai ɗumi, kasancewar ba ni da nauyin bacci na buɗe idona

Idonmu ne ya sarƙe da na juna, tuni zuciyata ta fara gudun bala’i tana harbawa da sauri da sauri yanayin da ban taɓa shiga irinsa ba, rintse idona nayi dan dukkanmu mun kasa janye idanuwanmu daga na juna

“Sleeep!!!” Ya furta a sanyaye sannan ya wuce. ……

BOOK ƊINA NA KUƊI NE IN KIKA KARANTA KYAUTA KIN SHIGA HAƘƘINA

[11/15, 5:31 PM] Muslima????: 55&56

????SARKI

Murmushi na saki tareda kuma janyo bargon sannan na rufe idona bacci yayi gaba da ni

Washegari da na tashi rasa wajen alwala nayi, ina zaune ina tunanin inda zani sai ga Prince Sydeek ya dawo daga masallaci, dubana yayi yace “kinyi sallah?”

“A’a” na ba shi amsa a taƙaice

“Idan kin fita, left handside ɗinki akwai toilet kina iya using ɗinsa” ya faɗa yana shigewa ciki

Bayan nayi sallah waje na samu na zauna ina lazimi har haske ya keto, misalin bakwai Prince Sydeek ya fito, dubana yayi yace “tashi mu je”

Ni da na gama haɗa dukkan kayanmu banda blanket ɗin wajen Big Madam na hau tattarosu tareda miƙewa, sai kayan suka fi min yawa saɓanin jiya duk da babu bargo, ko arrangement ne banyi da kyau ba

Ɗan tsayawa Prince Sydeek yayi har na ƙaraso inda yake, hannu ya sanya ya amshi blanket ɗin sannan yayi gaba

Tsai nayi na bi sa da kallo har ya kusa kaiwa mota sannan na cimma masa bayan na murmusa

Bayan mun isa sashensa kitchen na wuce, abinci mai sauƙi na haɗa masa kana na wuce sashenmu dan na shirya kada ya tafi ya barni (Anitha dai ƴar gulma ce)

Ban ɓata lokaci a nan ba, nayi maza na koma sashensa, ko da na isa zaune na ganshi a kujera yana ɗaura takalmi, da sauri na nufi dining dan naga ko ya ci abinci, ganin bai taɓa komai ba ya sanya nace “baka ci komai ba”

“Na ƙoshi” ya faɗa yana miƙewa

Da sauri na fara ƙoƙarin ɗaukar kwanukan dan na bi sa

Tsai yayi sannan ya haɗe fuska yace “ke kar ki biyoni”

Taɓe baki nayi sannan na koma na zauna

Abincin na zauna na cinye sannan na kuma kimtsa wajen, na kwanta dan bacci

Nayi nisa a bacci cikeda mafarkan Prince Sydeek naji ana shafa gashina dan ɗan kwali ya zame min

Buɗe idona nayi na saukesu akan Prince Yar da ke murmushi yana kallona

Miƙewa nayi zaune nima na yafa fara’a a fuskata nace “sannu da zuwa”

“Yawwa, Sydeek ya fita ko?” Ya tambaya

“Eh” na ba shi amsa a taƙaice

Hannu ya sanya ya fizgoni jikinsa ya rungume ya hau sakin ajiyar zuciya, ya ɗau lokaci mai tsayi a haka kana ya raba yace “i miss you Batool”

Murmushi na saki sannan nace “nima haka, dama akwai abinda nakeson faɗa maka” na faɗa ina janyewa daga jikinsa

“Ina jin ki” ya faɗa yana saita nutsuwarsa

“Uhm.. dama Prince Sydeek ne naga ya canza min gabaɗaya” na faɗa a sanyaye

“Share shi Batool, na so prolonging wasanmu yanda zai bani nishaɗi amma yanzu is late, i just have to get rid of him kafin na samu kujerata ko na nakasashi” ya ƙare yana sighing

Wani irin tsoro ne ya kamani jin zancensa, ta maza nayi nace “mai zaka yi masa toh yanzu?”

“Yanzu zan fara wasan daka ma dukiyarsa wawa kafin na kashe shi dan gaskiya i need his money” ya faɗa cikin kwanciyar hankali

Gyaɗa kai nayi alamar gamsuwa

Miƙewa yayi yana faɗin “ina pc ɗinsa zan ɗauki bank details ɗinsa”

“Tana ɗaki” na faɗa a taƙaice, yana miƙewa na janyo wayarsa cikin sa’a babu password, lalube nayi har na gano abinda nake buƙata, sai da na haddace digits ɗin sannan na ajiye wayar

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button