SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

Kuka nake kamar raina zai fita, a zuciyata ina kaico da wannan rana da zan karya alƙawari

“Ina yake?” Cewar Prince Yar

“Nayi burying ɗinsa a. …..

[11/17, 6:58 PM] Muslima????: 67&68

S A R K I

“Nayi burying ɗinsa a…” ban kai ga ƙarasawa ba na dakata sakamakon ƙofar da aka bugo da ƙarfin gaske

Prince Sydeek ne tsaye fuskarsu babu yabo babu fallasa

A razane Prince Yar ya dubesa yace “Ya Sydeek ha.. how?!!!” Ya ƙare cikin stammering

Murmushi Prince Sydeek ya saki kafin yace “dama nayi ta neman maid ɗina ne coz ina zarginta da min sata, and i was directed here kan ta na nan, and it seems like kamar kaima kanada business da ita ko?”

Cikin daburcewa Prince Yar yace “no…ni….nim…ni…nima yanzu na ganta” ya faɗa

“Ohhh, i see” cewar Prince Sydeek

Wayarsa ya ɗaga yayi dialing sannan yace “come in”

In less than a minute wasu zabga zabgan majiya ƙarfi suka shigo sanye cikin uniform probably escorts ɗinsa ne, suna shigowa ya kallesu tareda cewa “loose her”

Kwanceni sukayi sannan na miƙe da ƙyar jikina yayi mugun tsami ga ciwuka da nakeji a gaɓoɓina haɗe da jikina

Maida dubansa kan Prince Yar da tsabar ɓacin rai ya kasa furta komai, murmushi Prince Sydeek yayi tareda matsawa gefensa ya ɗan bubbuga kafaɗarsa sannan yace “sai mun haɗu anjima little brother”

Gaba ya tasa ni shikuma yana biye da ni yayinda escorts ɗinsa suka rufamasa baya

Sai da muka fito naga ashe jama’ar da ya taho da su zasu yi ashirin all armed

Motar da aka buɗe masa ya shiga ina shirin buɗe gidan gaba yace “come in”

A sanyaye na tura kai ciki, yanda nake ji na so weak sai da na matsa kusada shi tareda jingina a jikinsa

“I’m sorry!!” Ya faɗa softly tareda riƙe hannuna ya haɗe da nasa

Hawaye ne suka gangaromin, da ƙyar na share hawayen sannan nace “how?”

“Na nemi one of his men ne na biyasa kuɗi dayawa, and ya nuna min wajen da suke ɓoye mutane idan sunyi kidnapping ɗinsu, and luckily sai na sameki a nan” ya faɗa yana murza hannuna gently

Gyaɗa kai kawai nayi batareda cewa komai ba na cigaba da hawayena wanda ya ɓata masa riga sosai

Ɗan rintse ido yayi as if yana feeling pain ɗina sannan yace “how much do they hurt you?”

“So bad, that i can’t tell!” Na faɗa cikin kuka

Shiru yayi bai ce komai ba

A ɗan firgice na miƙe nace “sunyi placing bomb a apartment ɗinka!!!”

“They can’t, akwai detector, sun faɗa dan su tsorata ki ne” ya faɗa yana kuma kwantar da ni

Tafiya kaɗan ce ta kaimu unlike zuwan da muka ɗauki mintina da dama, probably sunyi ta yawo dani kafin su isa ne

Prince Sydeek da kansa ya taimaka min muka shiga ciki

Ruwan zafi ya haɗa a bathtub ɗinsa kana ya fito yace “shiga kiyi wanka”

Ɗan zaro ido nayi ni da nake kwance da mamakin ta ya zan fara wanka a bathroom ɗin Prince

“Je ki” ya faɗa

Miƙewa nayi na nufi bathroom ɗin, the water was hot, warm and fragrance scented with few red petals in it, sosai na ji daɗin wankan, sai da na gasa jikina sosai na fito

Tsaye nayi ina tunanin kayan da zan saka coz yanda nake jin ƙyanƙyamin kayana ba zan iya maida su ba

Wani ɗan corridor da na hanga cikin bathroom ɗin na bi, wata ƴar siririyar slide door na bi, ban ɓulla ko ina ba sai a closet ɗinsa which is a huge room full of clothes wanda kusan duka are all new

Jikin mirror na tsaya inda na ga dryer da stretcher tareda mayukan gashi, bayan nayi drying kaina na shafa mai sannan na nufi wajen kayansa

Wata farar soft and comfy long sleeve na zaro na saka sannan na ɗauki wani farin gajeran wandonsa wanda ya tsaya min iya gwiwa sannan na fito

A parlor na taddasa hannunsa riƙe da bowl na ramen (indomie)

Kallo ɗaya yayi min ya kauda kansa sannan ya ajiye bowl ɗin yace “eat!” Sannan ya shige ɗaki

Sosai na ci indomie dan cutar da nake ji bata hana cikina jin yunwa ba, bayan na gama ci kwanciya nayi tareda lumshe idona ina jin yanda jikina ke ciwo hawaye na fita daga idona

Lokaci mai ɗan tsayi Prince Sydeek ya fito, a hankali yace “sit down”

Buɗe idona nayi na gansa tsaye da glass of water, miƙewa nayi na zauna, shima zaman yayi a kusada ni tareda miƙo min pills yace “pain reliever”

Amsa nayi batareda nace komai ba, sai da na shanye nace “nagode”

Ɗan tsuramin ido yayi sannan ya kauda kansa gefe yace “i’m sorry”

Ƙarar saƙon message ne ya faɗo wayarsa, ɗauko wayar yayi ya duba

Wani tashin hankali da ruɗani ne suka bayyana a fuskarsa

Ganin sauyawar yanayinsa cikin ƙanƙanin lokaci nace “mai ya faru!”

Kasa furta komai yayi sai duban wayar hannunsa da yayi da saƙo ke ta faɗowa jeri jeri

A ɗan tsorace na karɓi wayar, bansan lokacin da na saki glass ɗin ruwan ba tareda furta “innalillahi wa’ina ilaihi raji’un!!!” Slowly. ……

LITTAFINA BA KYAUTA BA NE, NA KUƊI NE, NAIRA 300 KACAL TA 1401611541, FATIMA LAWAL SAID. ACCESS BANK OR MTN CARD TO 08167888934

IDAN KIKA KARANTAMIN BOOK BA KI BIYA BA BAN YAFE BA
[11/18, 3:02 PM] Muslima????: ???? S A R K I

FUNNY PEOPLE???? KE BA KI SUBSCRIBING BOOK ƊINA BA AMMA KIN KIRANI KINA MIN PREACHING ALHALIN KE ƊIN BAKI GUDUN SHIGA HAƘƘIN MUTANE????

69&80

PRINCE SYDEEK POV

Kallonta yayi da narkakkun idanunsa kamar zai furta wani abu sai kuma ya fasa ya amshi wayarsa ya shige ɗaki

Zama yayi bakin gado tareda folding hands yana mamakin mai yayiwa ɗan uwansa Prince Yar a duniya wanda ya cutar da shi da har yake neman ganin bayansa haka

Dafe kansa yayi da ke mugun sara masa sannan yace “mai nayi maka haka Yar!!!!”

Abin na baƙanta ransa, yanzu ace mahaifinsu ko kwana biyar bai rufa ma amma suke ta tada fitina iri iri haka gwanin ban kunya

Tunaninsa ɗaya yanzu ta ya Prince Yar ya samu access to kuɗinsa har yayi masa yasa mai yawa irin haka batareda ya barshi da ko kwabo ɗaya ba dukkanin asusun bakinsa bayan wanda yake ajiya a fixed accounts wanda ba’a taɓa iya cirarsu har sai lokacin da aka ɗiba na ajiyarsu sun cika, furzar da iska yayi yace “i will end you and your evilness with my very own hands” ya faɗa yana miƙewa a fusace tareda dukan madubi ya tarwatse yayinda kwalbar ta shiga hannunsa jini ya fara tsiyaya

BATOOL POV

Cikin sauri na miƙe jin ƙarar glass, da sauri na shiga ɗakin

Tsaye na gansa ya juyawa ƙofa baya, hannunsa na dama na ɗigar da jini

Da hanzari na ƙarasa nace “mai ya faru da kai, meyasa zaka ji ma kanka ciwo” na faɗa a ruɗe

Bai tankani ba sai kallona kawai da yayi ya kauda kansa daga duban nawa tareda komawa bakin gado

Ƙarasawa nayi kusada shi nace “ina first aid box?”

Nuni yayi min da wata drawer batareda ya furta komai ba

Miƙewa nayi na ɗauko sannan na gyara masa ciwon, bayan na gama na dubesa nace “i think i can help”

Kallona yayi yace “how?”

“Zan iya hacking account ɗinsa maybe, ina pc ɗinka?” Na faɗa ina kallonsa

Dubana yayi na tsawon sakanni sannan ya min nuni da ita ƙasan pillow ɗinsa

Ɗaukowa nayi sannan na jona hotspot, tareda sanya flash

Tsawon minti sha biyar ina ta trying suna faɗamin access denied, furzar da iska nayi cikin takaici

A hankali yace “you can’t, kije ki huta, i will handle the case” ya ƙare sounding caring

“Let me try once again” na faɗa batareda na kallesa ba

Luckily ina ƙara trying a na biyun coz last one digit na bvn number ɗinsa ce nayita contemplating a kai suka ce min ACCESS ALLOWED

Wani irin farinciki ne ya ziyarceni, har fararen haƙorana suka bayyana sannan nace “bani account number ka”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button