SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

BATOOL POV

Ganin ya gama cin abincin ya naɗe hannayensa yana kallona ya sanya nace “what?” A ɗan sanyaye

“I want to figure out something” ya faɗa a sanyaye

“What?” Na tambaya cikin mamaki

Hannu ya ɗora kan lips ɗinsa yace “shhhhh”

Shiru nayi, ya jima yana kallona sannan ya ɗauke kansa daga dubana

“Why?” Na tambaya

“Why what?” Ya faɗa cikin rashin fahimta

“Na faɗa maka komai gameda Prince Yar amma still kana ƙara jansa a jiki, baka jin tsoro?” Na ƙare ina kallonsa

Murmushi ya ɗanyi sannan yace “he is my brother” a taƙaice ya miƙe

“But…” ban kai ga ƙarasawa ba ya ɗaga min hannu sannan yace “spend the night here” ya shige cikin ɗaki

“Huhhh, kaima you don’t deserve the throne bakada ƙarfin zuciya, you are weakling” na faɗa ina zama daɓas kan kujera

Na ɗan ɓata mintina sannan na miƙe na rufe ko ina kana na kwanta kan doguwar kujera, duk da akwai wuta a ɗakin still sanyi nake ji sosai

Har na fara bacci naji ƙarar buɗe ƙofa, rufe idona nayi inda Allah ya taimakeni gashina ya bazu kan fuskata zan iya leƙe ma ba’a ganni ba dan fitila kashe take

Prince Sydeek tsugunnawa yayi gaban kujerar sannan ya rufamin blanket ɗin

Tsuramin ido yayi kafin ya sanya hannunsa ya ɗagemin gashina zuwa baya, hannuna ya riƙe da hannunsa dake so warm and soft sannan yace “thank you for saving me”

Bansan meyasa nayi hakan ba amma sai na tsinci kaina da riƙe hannunsa gam na matse ina feeling warmness ɗin hannunsa

Chuckling ya ɗanyi a hankali kusada fuskata yace “sleeping beauty cikani”

Cikasan nayi da sauri batareda na buɗe idona ba

Murmushi yayi mai ɗan sauti sannan yace “thank you”, har ya miƙe sai ya dawo yayi pecking goshina sannan ya fice. ….

[11/14, 9:11 AM] Muslima????: S A R K I

     *49&50*

Bayan wucewarsa na kuma jan bargo na ƙudundune ina mamakin abinda ya aikata a yanzu, tau me hakan yake nufi, farinjinin nawa ya ruɗesa ne shima ko kuwa

Sanin babu mai bani amsar nan sai shi kuma bazan sameta cikin daren ba na ja idona na rufe na barwa ranakun gaba

Washegari misalin bakwai na tashi, bayan na yi ƴan gyara gyarena, na wuce kitchen na haɗa masa abinci mai sauƙi sannan na fice sashenmu, chan nayi wanka, na ci abinci sannan na shantake hira da Junnut kasancewar yau bata je kitchen ba bata ɗan jindaɗi, munyi hira da ita mai tsayi kafin na tashi na haye gado dan bacci. Na ɗauki awanni ina bacci har azahar ta gota bansan inda nake ba, ina cikin baccina mai cikeda mafarkin Mom, Junnut ta hau tadani tana faɗin “ke ki tashi, tun ɗazu akayi azahar fa”, miƙa nayi bakina ɗauke da addua sannan cikin bacci nace “wai har azahar tayi”, Junnut da ta koma gadonta tace “sai dai kuwa in wata za’a sake miki”

Ban kuma tankawa ba na faɗa toilet tareda ɗauro alwala, bayan na gabatar da sallah wanka na faɗa sannan na shirya cikin doguwar riga mara nauyi, na yane kaina da lulluɓi sannan na nufi sashen Prince Sydeek inata tararrajin na barshi da yunwa, bakina ɗauke da sallama na danna kai ciki, zaune na tadda shi tareda Prince Yar suna game ta dice

Cikin girmamawa nace “barkanku da rana”, Prince Sydeek bai ko ɗaga kai ya kalleni ba, Prince Yar ne ya gyaɗa kai sannan ya min smiling shima ya maida kansa kan game ɗin, taɓe baki nayi a zuciyata ina faɗin “miskilin banza”, na ɗauki mintina masu ɗan tsayi a nan babu wanda ya kuma tankani cikinsu, ganin tsayuwar bazata kai min ba nace “mai zan kawo muku?”, Prince Yar ne yace “mun ci abinci ba jimawa”, gyaɗa kai nayi sannan na koma bayansu na tsaya. Sun ɗauki lokaci mai tsayi suna wasan kafin Prince Yar yace “wannan maid ɗin taka na burgeni, tanada nutsuwa da sanin ya kamata”, Prince Sydeek ya ɗauki kusan minti ɗaya baiyi magana ba sannan chan ya ja numfashi yace “ko na bar maka ita ne?” Daidai lokacin ya cinye wasan, murmushi Prince Yar yayi sannan yace “shit!!! Na yarda ka fini iya wasan nan” sai kuma ya ɗora da cewa “zaka bani ne?”, taɓe baki Prince Sydeek yayi yace “har sai an tsaya ja in ja, in kanaso tafi da ita sashenka mana”

Wani malolon baƙinciki ne ya tokaremin a wuya, lallai ashe ni ɗin ban san Prince Sydeek ba, yau shine dariya gobe kuka, ji yanda yake wani neman nesa da ni bayan jiya ya lulleɓeni da bargonsa mai laushi haɗe da pecking goshina ya kuma damtse hannuwana

“Ina so, amma ba kyauta zan amsa ba, mu buga game in ka ci dice mai lamba shida ka cinye zan kuma baka kyauta mai tsoka, idan kuma ni na cinye zaka bani waccan yarinyar duk da ba yanzu ba”, murmushi Prince Sydeek yayi sannan yace “ka maida yarinya tana jinta kamar ita ɗin kayan gabas ce, ko da yake muje zuwa”, dariya Prince Yar ya saki sannan yace “ina ƙaunarka Yayana, sai dai fa kasani na iya wasan nan sosai, kuma ban taɓa faɗuwa ba”, murmushi Prince Sydeek ya saki sannan yace “bana fara wasa har sai na tabbatar da cewa ni ne zanyi nasara” daidai lokacin ya wurwura dice ɗin sannan ya kife, Prince Yar hakan ce ta kasance shima ta ɓangarensa

Zuciyata bugawa take da ƙarfin gaske, dan i can’t imagine nakoma aiki under this heartless and shameless person ɗin ba, Prince Sydeek kuwa zagin da yasha ba ɗan kaɗan ba ne cikin raina, Prince Yar ne ya fara cira hannunsa nan ɗigo biyar suka bayyana, Prince Sydeek ya ɗan ɗauki sakanni kafin ya ɗaga ɗigo shida su bayyana, ajiyar zuciya na sauke wadda ta fito sarari har saida dukkaninsu suka kalleni, Prince Sydeek ɗauke kansa yayi yayinda Prince Yar ya tsuramin na mujiya alamun yana karantar yanayina, Prince Sydeek ne yayi gyaran murya cikin cool husky voice ɗinsa yace “ina jiran gift ɗina, maganan maid ɗin kuma ka ɗauka na baka, dama ba na damu da aikinta ba ne” ya ƙare da smile a fuskarsa, ƴar dariya Prince Yar ya saki sannan yace “wasa fa nake maka, ni mai zanyi da wata maid bayan inada mata” ya ƙare da murmushi

“Haka fa!” Prince Sydeek ya faɗa fuskarsa babu yabo ba fallasa, hira suka kuma taɓawa akan business kafin Prince Yar yace “dama na amso takaddun company da muka siya, so zuwa anjima idan na dawo zan kawo maka” ya faɗa yana miƙewa, gyaɗa kai Prince Sydeek yayi sannan yace “have a nice day”, da murmushi Prince Yar yace “thank you”, ko da yazo ta inda nake sai da ya ɗan dakata ya kalleni na sakanni kana ya wuce waje

Nayi tunanin kamar jiya Prince Sydeek zai tankani bayan fitar Prince Yar, sai kuma naga saɓanin haka dan ko kuma kallon inuwata baiyi ba, ya miƙe ya shige bedroom ɗinsa, gabaɗaya jikina ne yayi sanyi dan banyi tsammanin haka daga garesa ba, nima zama nayi a kujera inata saƙa da warwara duk akan lokacin da zan bar hargitsatsiyar masarautarnan, ganin babu abinda zanyi sai na kishingiɗa tuni sabon bacci yayi gaba dani. Ba ni na tashi ba sai gaf da asr, bayan nayi sallah kitchen na faɗa na haɗa masa mash potato sannan na ɗora da pepper soup, parlor na taddasa bayan na fito, cikin girmamawa nace “barka da yamma”, ɗan kallona yayi sannan ya ɗauke kansa kana ya amsa da “barka”, daganan babu wani zance da ya kuma shiga tsakaninmu har bayan magrib

Bayan nayi sallah nayi masa setting table, ina ƙoƙarin nace yazo ya ci, akayi knocking a ƙofa, nufar ƙofar nayi na buɗe, ina leƙawa dan ganin waye aka fizgoni, a ɗan tsorace na kalli Prince Yar da ya kafeni da ido, ƙasa nayi da kaina, “guduna kikeyi ko?” Ya tambaya, girgiza kai kawai nayi batareda na furta komai ba, “kiyi haƙuri Batool akan abinda na so aikata miki, sonki ne da sharrin shaiɗan amma bazan kuma ba sai ranarda kika zama halaliyata, kinji” ya faɗa yana zuba min idanunsa masu ɗauke da tsantsar nadama, gyaɗa kai nayi sanan nace “bakomai ya wuce”, murmushi yayi sannan yace “takaddun da zan bawa Prince Sydeek yanzu ki tabbata kin ɗauko min su zuwa gobe, no matter what ki kawo min su” ya faɗa yana kallon tsakiyar idona, gyaɗa kai nayi nace “zan kawo”, murmushi ya saki sannan ya cikani ya shige ciki, binsa nayi da kallo zuciyata sai bugu take saboda firgicin da na shiga

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button