SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

Rintse idona nayi ina jin ƙwalwata da kaina na bugu da masifar ƙarfi, wasu hawaye ne masu zafin gaske suka gangaromin, a hankali nace “please save me!!” Na faɗa a galabaice coz ina fara shaƙar abin nakejin duk wata gaɓa ta jikina a ɗaure, ga rashin ƙarfi da kuzari

Murmushi ya saki sannan ya fara shafa kaina yana faɗin “bazan cutar da ke ba, ni kaɗai zaki yarda da shi, ki bi umarnina, Prince Sydeek maƙiyinki ne, kinji Batool”

Cikin ruɗu na sauke idona da sukayi jaa a fuskarsa, ina kokwanton abinda yake faɗa

“Baki yarda ba?” Ya tambaya cikin sanyi

Girgiza kaina da yayi min dummmm nayi sannan slowly nace “eh”

“Kin manta ne Batool, yana tsaye, kin ma nemi taimakonsa amma sai yayi miki dariya ya wuce, ki tuna mana, crack your brain” ya faɗa yana kuma turo min kaskon sosai har ina jin turirin garwashin a fuskata

“A’a!!” Na faɗa ina girgiza kaina domin yaƙi ne babba mind da heart ɗita suka fara, mind ɗina ta fara haskomin hotonsa tsaye yana kallona yayinda zuciyata ta dinga ƙaryatawa, kuka nake domin ba ƙaramin tashin hankali nake ciki ba, wani irin yanayi ne mai wuyar fasaltawa, kaina ciwo yake kamar zai tarwatse yayinda zuciyata ke bugu da ƙarfin gaske, kwanyata ihu da ruri take, ɓangaren dama na ƙaryata furucin Prince Yar, yayinda ɓangaren hagu ke haskomin Prince Sydeek tsaye yana min dariya yayinda ƙaratan suka ɗaukeni suna ƙoƙarin sani a mota, ina miƙa masa hannu yana min dariya

“Think Batool, you can fight this war, think!!!!” Cewar Prince Yar

Jikina karkarwa kawai yake, yanayin da nake ciki ba dan ina musulma ba da sai nayi fatan Rabbi ya karɓi raina, domin matsananci kuma mawuyacin hali nake a yanzu

“Sydeek is your enemy!!!” Cewar Prince Yar cikin karaji

Ihu na kurma mai tsananin ƙara, daidai lokacin na zube sumammiya

UNITED STATES

VIRGINIA

A zabure wata matashiyar mata wadda kallo ɗaya zakayi mata kasan jinin larabawa ce ta miƙe tana faɗin “innalillahi wa’ina ilaihi raji’un” hawaye na kwaranyo mata

Wani dattijon bature da ke zaune bisa gado yana danne danne a system ya ture system ɗin, tareda matsawa kusada matar ya kwantar da ita kan ƙirjinsa yana faɗin “it’s alright”

Cikin kuka tace “na kasa samun sukuni, i’m disturbed, something is telling me Anitha is in danger”

“Shhhh, ki daina kuka komai will be alright i promise, nothing will happen to our girl” ya faɗa yana rungumeta sosai

Ƙara cusa kanta tayi a ƙirjinsa tana faɗin “what if she is gone, bazan iya rayuwa in na rasa Anitha ba, wallahi mutuwa zanyi” ta ƙare cikin matsanancin kuka

Cikin tashin hankali ya fara buga bayanta yana faɗin “i will find our girl no matter what, and she is alright insha Allah, let’s keep praying”

Gyaɗa masa kai tayi tana ta sauke ajiyar zuciya

Ya jima yana rarrashinta kafin ta samu kwanciyar hankali

Miƙewa tayi ta nufi toilet ta ɗauro alwala sannan ta fara salloli, ta jima tana sallah kafin ta fara addua’a wadda dukkaninta akan Anitha ne

Ta jima a wajen kafin nan bacci ya fara ɗaukarta, bata yi nisa ba ta farka a firgice tana faɗin “Anitha!!!”

Cikin sauri mijin ya sauko tareda rungumeta yana faɗin “kina ƙara sakani cikin damuwa, nima ina cikin tashin hankali, zuciyata na gaf da bugawa, dan Allah ki daina tsorarani haka”

Cikin kuka ta kuma shigewa jikinsa tana faɗin “mafarkinta nayi tana kuka da neman taimakonmu”

Gyaɗa kai yayi yace “let’s pray for her” ya faɗa yana janyota zuwa gado

“أُعِيذُكُمَا بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّةِ مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لَامَّةٍ”

shine addu’ar da take ta maimaitawa da zarar Anitha ta faɗo mata a rai har bacci yayi gaba da ita

ABU-DHABI PALACE

A firgice na farka bayan ruwan sanyin da naji an shafamin, babu abinda nakeyi sai sauke ajiyar zuciya

Janyoni yayi tareda rungumeni a jikinsa yana faɗin “sannu!” Cikin kulawa

Kwantar da kaina nayi a kafaɗarsa ina jin yana kaina ke sarawa duk da ya min sauƙi sosai

“Kina jin yunwa?” Ya tambaya yana shafa bayana

Cikin sanyi nace “kaina ciwo”

Bai tanka ba, ya fara ƙoƙarin cire min rope ɗin

Bayan ya cire ya buɗe nan ya zaro pita bread da nutella haɗe bread yoghurt ya ajiye min yace “bari ki ci abinci sai na baki magani”

Gyaɗa kai kawai nayi batareda nace komai ba

Da kansa ya dinga ɗebowa yana sa min a baki har naci rabin pita bread sannan nace “na ƙoshi”, na maida kaina kan kafaɗarsa coz right now i’m so in need of shoulder to lean on

Hannu ya sanya ya ɗan riƙeni yana min sannu

Mun ɗauki lokaci mai tsayi kafin ya janye jikinsa yace “bari na kawo miki magani”

Gyaɗa kai nayi

Fita yayi bai jima ba sai gashi ya dawo da magunguna, ɗaya na ciwon kai, ɗaya na saka bacci

Duk da nasan ɗaya na buƙata haka na haɗiyesu coz yanda nake jina tabbas inada buƙatar hutu, ƙwalwata ta huta itama…..

[11/12, 5:14 PM] Muslima????: LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI, NAIRA 300 KACAL TA ASUSUN 1401611541, FATIMA LAWAL SAID, ACCESS BANK, SAI KI YI SCREENSHOT ZUWA 08167888934, KO KUMA KATIN MTN ZUWA 08167888934

S A R K I

          *37&38*

Firgigit na tashi yayinda jikina ke ta ɓari sanadiyyar mafarkin Prince Sydeek da nayi yana bi na da wuƙa

Kuka na fashe da shi tareda kifawa kan gadon ina faɗin “Prince Sydeek mai nayi maka, mai ya sanya ka cutar dani bayan taimaka maka nayi, Allah zai saka min kuma wallahi ba zan taɓa yafemaka ba” na ƙare ina sakin kukan da ke fitowa daga zuciyata

Na jima a wannan yanayi sannan naji an turo ƙofa

A firgice na ɗaga kaina ina kallon ƙofar, ganin Prince Yar ne na saki ajiyar zuciya da ta fito fili

Murmushi ya saki sannan yace “bad dreams?”

Gyaɗa kai nayi sannan na kallesa cikin ido nace “dan Allah ka maidani palace, ni na gaji a nan” na ƙare ƙwalla masu ɗumi na saukar min

Murmushi yayi sannan ya zauna kan gadon yace “insha Allah, in kika ƙarasa dose ɗinki gobe zan maidaki” ya faɗa da murmushi

Gyaɗa kai nayi sannan nace “toh” ba dan raina na so ba, sai dan bana marmarin saɓa umarninsa

Dubana yayi sannan yace “kinyi sallah?”

Girgiza kai nayi nace “a’a”

“Je kiyi, sai kizo ki ci abincin rana” ya faɗa da smile a fuskarsa

Bayan na kammala komai na idar da sallah na zauna kan dadduma tareda jingina da gadon

Prince Yar fita yayi, lokaci ƙanƙani ya dawo hannunsa ɗauke da takeaway pack

Buɗewa yayi tareda ɗaukar spoon ya fara bani a baki

Ƙura masa ido nayi ina aiyana irin kirkin da yake min, ko bakomai yana kulawa dani sosai

Murmushi yayi yace “Batool ki ci”

Murmushi nayi sannan na amsa

Cikin fara’a yace “you are beautiful when you smile”

Ɗan tsura masa ido nayi sanan na ɗauke kaina fuskata babu alamun wani reaction

Sai da na gama cin abincin tasss sannan yace “Batool i’m sorry” cikin murya mai matuƙar rauni

“Mai ka yi?” Na faɗa a sanyaye

“Na cutar da ke” ya faɗa kansa a ƙasa

Hannu na saka na tallabo fuskarsa sannan na girgiza kai nace “baka yi min komai ba, dan Allah ka daina cewa haka” idona na kawo ƙwalla

Murmushi kaɗan yayi min sannan ya ɗora hannunsa bisa hannuna ya lumshe idanunsa

Kallonsa nakeyi ina jin wani iri gameda shi, ta wani ɓarin kamar ƙiyayya, wani wajen biyayya, wani ɓarin shaƙuwa ce zance ko soyayya, na kasa fahimta, kaina ya cushe, ƙwalwata ta cunkushe, ba ma zan iya tunanin ba dan bansan yanda akeyinsa ba, dan dole na tsaya a haka ina bin fuskarsa da kallo

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button