SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

“Amsar mene?” Na faɗa coldly

Ƙarasowa yayi gaf dani har ina jin bugun zuciyarsa sannan ya rage tsawonsa ya kawo bakinsa saitin nawa yace “na proposal ɗin da nayi miki”

Yawu na haɗiya dan gabana ne ya dinga mugun faɗuwa, shiru nayi sai raba idanu nakeyi

Bakinsa ya matso da shi wajen nawa yana ƙoƙarin haɗesu, kauda kaina nayi gefe guda zuciyata ta tsananta bugawa

Ɗan murmushi yayi sannan ya ɗaga jikinsa yace “kinyi rejecting ɗina kenan”

Kaina na saka ƙasa na ƙi ɗagowa na kuma ƙi furta komai

Murmushi ya sakeyi mai ɗan sauti sannan ya ɗago haɓata, muka fara kallo ido cikin ido sannan yace “bazan haƙura da ke ba, i will try to win your heart” ya faɗa

Jiki a sanyaye na maida kaina ƙasa

Ƙofa ya nufa ya murɗa handle ɗin sannan yace “zan turo miki kayan da zaki saka, later” ya ƙare yana ficewa

Sighing nayi tareda zubewa kujera nace “ya rabbb this people zasu ɓata min lokaci ne, why does everyone love me, Anitha mai yasa kike da farinjini haka” na ƙare ina buga goshina da hannu

Prince Sydeek bai shigo ba har sai after asr lokacin ina ta kallon wani indian film

Cikin sauri na miƙe ina faɗin “sannu da zuwa”

Bai tankani ba ya nufi hanyar ɗakinsa

“Ehm, Prince anjima akwai family dinner Prince Yar yace na faɗa maka” na faɗa ina kallonsa duk da bai juyo ba

Juyowa yayi sannan ya min kallon ƙasa da sama yace “make sure you bath, sannan ki saka gloves” ya ƙare yana hissing ya shiga ɗaki

Banyi wasting time ɗina wajen yin dinner ba coz nasan yau da family zai ci, lol ko nayi ɗin ma kuma ba ci yake ba, so i hurried back to our building

Ina zuwa Junnut ce ta tareni da dariya a fuskarta

Dariya nayi mata nace “what’s so good?”

Huge box ta ɗauko tareda ajiye min tace “look, i’m told Prince Yar ya aiko miki, na outfit ɗin dinner” ta ƙare tana buɗe box tareda zaro wata sea blue gown dake glittering with white shiny stones

“Wow” na furta dan ba ƙaramin kyau tayi ba

“Tayi kyau ko, the gifts sunyi kyau and they are expensive, kalla wanan high hill white shoe ɗin, dagani mai tsada ne” ta faɗa cikin jindaɗi

Murmushi nayi mata sannan nace “sunyi kyau sosai” coldly

Ɗagowa tayi ta ƙuramin ido sannan tace “is something wrong?”

Slight smile nayi sannan nace “no”

“Wait ɓangaren Prince Sydeek kike, meyasa Prince Yar ya kawo miki kayan dinner” ta tambaya cikin mamaki ta kuma kafeni da ido

Yatsina fuska nayi dan banida abin ce mata, beside meyasa ma zata dinga tuhumata duk da she is nice and kind ban cika son mutum yake ƙoƙarin cusa kansa personal issues na ba

“Batool!!!” Ta faɗa as in tana saurarona

Ban kai ga buɗe baki ba Salamat ta shigo cikin jindaɗi

Da gudu ta rungume Junnut tace “i’m so happy”

Junnut dariya tayi tace “why?”

Dariya ta kuma yi tace “kalli kayan da Prince Yameen ya bani, i will be his special maid tonight zasuyi family dinner” ta ƙare tana tsalle

Taɓe baki nayi dan i see nothing about dinner, mene dan zasu ci abinci sai an yi sabon kaya ma dai banda ƙarya da iyayi

Dariya Junnut tayi tace “zan shirya ku, kuyi kyau sosai”

Taɓe baki Salamat tayi sannan tace “no, side ɗin Prince Yameen zani akwai make up artist da zata zo tayi min kwalliya, kisan komai shi yana son nasa yafi nakowa, so he is showing up with me dan haka dole nayi kyau” ta ƙare tana fari

Murmushi Junnut tayi tace “gaskiya kam, i can’t wait to see you”

Hira ce muka zauna muna ɗanyi har akayi magrib, bayan magrib Salamat ta wuce sashen Prince Yameen

Junnut ce ta takura sai na shirya, ba dan naso ba na saka gown ɗin, tayi fitting ɗina sosai nayi kyau, sannan nayi rolling da white silky veil

Junnut ce ta dage sai nayi make up, so dan dole na saka kwalli duk da ba san shi nake ba, most of time Mom ke matsamin shima sai zamu event haka

Sosai nayi kyau, na zarga long stone necklace ɗita

Junnut sai yaba kyauna takeyi har ta fara bani dariya, after that na saka takalmina wanda suka ƙara fito da ni

Junnut ce ta shafamin light pink lipstick dan dole, sosai nayi kyau

Miƙewa nayi na dubeta nace “am i good to go”

Gyaɗa kai tayi cikin jindaɗi tace “kinyi kyau”

A haka na fita da murmushi, ina barin wajen na saka hannu na goge lipstick ɗin nace “wa zan yi ma kwalliya”

Ko da na ƙarasa part ɗinsa tsaye na gansa cikin shigar larabawa komai na shi fari ne sai adon silver, sosai yayi kyau har na shagala da kallonsa

Juyowa yayi ya kalleni, ya ɗan tsuramin ido na seconds masu ɗan tsayi sannan ya zauna kan kujera ya fara danne danne a waya

Misalin ƙarfe tara da kwata ina zaune inata kallon news ɗin dole dan shi ya saka nikuma tsoron canzawa nakeyi duk da ba kallon yakeyi ba

Ɗagowa yayi ya dubeni sannan ya miƙe tsaye yana faɗin “follow me” chan ƙasan maƙoshi

Ɗaukan keys na apartment entrance ɗin nayi wanda yake kan center table nabi bayansa, sai da nayi locking wajen na cimmasa zuwa parking lot ɗinsa da yake danƙam da manyan latest new cars

Wata arniyar Bugatti La Voiture Noire two-off model (mutum biyu ke da ita???? bear with me) Chauffeur ya buɗe, gidan baya ya shiga yayinda nima Chauffeur ɗin ya buɗemin gaba

Tafiyar minti bakwai ce ta ƙarasa da mu wani babban building da yafi kowanne building haɗuwa, kyawu da tsaruwa da idona ya taɓa gani

Ni na buɗe masa ƙofa, ina buɗe masa kuwa yayi gaba, bin bayansa nayi ina kallo sabuwar baƙauyiya coz the arts are just beyond imagination, babu abinda ake sai hidima maids keyi suna ta wuce da varieties of food

Da gani kuma special maids ne a ɓangaren coz uniforms ɗinsu are so different from ours, sai kalle kalle nake har yayi nisa

Tsayawa yayi tareda karkato attention ɗinsa ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallona, idona ne suka sauka akansa, smile na saki a kunyace sannan na ƙarasa wajensa da hanzari

Kafeni yayi da idonsa ko da na ƙaraso, shiru nayi na sadda kaina ƙasa

“Focus!” Ya furta yana wucewa

Binsa nayi har muka ƙarasa ciki

Ko da muka ƙarasa wajen mutane sun hallara, it was a huge royal dinning table with almost 20 chairs, mutanen da ke wajen are very few, daga wata tsohuwa wadda nake tunanin kakarsu ce, sai wanda nake tunanin shine sarkin masarautar amma yana kan wheelchair ne instead of dining one, sai Madam, Prince Yar, Prince Yameen, Princess Zairah, wata young beautiful last at her age of early 20’s sai kuma special maids da ke tsaye suna serving

Prince Sydeek wajen mahaifinsa ya fara zuwa ya gaishesa, sannan ya gaida wannan tsohuwar ya samu waje ya zauna

Madam cikin ɗan murmushi tace “Prince ba mu gaisa ba”

Ɗan ɗaga kai yayi ya kalleta sannan yace “sannu”

Serving ɗinsa na fara ƙoƙarin yi, hannuna ne ya sauka akan kafaɗarsa wani kallo ya ɗago yayi min

Saurin janye hannuna nayi dan bansan dalilin da yasa jikina ya ɗauki rawa ba, na ɗebo red stew zan saka kenan yace “bana san wannan!!” Cikin faɗa

Saboda tsoratar da nayi bansan lokacin da na juye serving spoon ɗin a jikinsa, a firgice ya miƙe dan zafinta har tururi take

Nan da nan wajen ya ruɗe kowa ya fara ƙoƙarin bashi taimako, Madam ce cikin ɓacin rai ta daka min tsawa haɗe da cewa “bakida hankali ne, mahaukaciyar ina ce ke”

Nan ta fara surfa ruwan bala’i, babu abinda nake sai hawaye ina faman basu haƙuri duk na ɗimauce dan wajen da ya ƙone har fatar tayi mugun jaa…..

WALLAHI IDAN BAKI JI KUNYAR ƁATA MIN LOKACI BA, BA ZAN JI NAUYIN ƁATA MIKI RAI BA. IDAN BA PAY ZAKIYI BA KAR KI NEMENI DAN ZANYI BAƘANTA MIKI, NAGODE

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button