SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

Yatsina fuska yayi sannan yace ” yanzu zan koma, kaya na zo ɗiba”

“No, please we are all counting on you, nayi cancelling auren and your turbaning will be in the evening, mun tattauna da council sun amince kayi aure daga baya amma within 2 months, coz baza’a bar space ɗin empty ba, and the girls family sun ce babu komai, you can marry Batool, amma dan Allah kar ka tafi!” Ta faɗa tana riƙesa haɗe da ƙwalla

Murmushi ya saki sannan yace “shikenan, thank you ma” ya ƙare yana hugging ɗinta

ANITHA POV

Tun fitarsa take tsalle kamar ƙaramar yarinya, murmushi ta saki tareda juyawa cikin jindaɗi tace “i can’t wait to be his Queen”

Dariya ta saki sannan tace “Zairah na rantse sai na rama marin da kikayi min, i won’t forgive that disgrace” ta ƙare tana sakin smile

Wayarta ta nufa tareda kiran number Mom tace “Mommmmm!!!!”

Mom sai da ta cire wayar daga kunnenta sannan tace “Anitha me ya sameki?”

Dariya ta saki sannan tace “i’m getting married!!!”

“What?! Bakida hankali” cewar Mom itama tana dariya

“I’m serious, kinsan wanda zan aura shine zai zama S A R K I na Abu dhabi nan da hours” ta faɗa tana tsalle

“Gist me!!” Cewar mahaifiyarta cikin zaƙuwa

“Well he proposed to be day before yesterday!” Ta ƙare tana rolling eyes ɗinta

“Awwwn!! I’m so happy baby girl, kinga duk na ƙagu na ga lucky man da baby girl ɗita ke so, i will gist your father about it now!” Cewar Mom

“A’a Mom i will tell him myself idan na dawo, take care, i love you” ta faɗa tana hanging batareda ta jira amsa ba

Pillow ta janyo tareda sakin dariya tace “Oh my God!! I’m getting married!!!”……..

[11/22, 8:28 AM] Muslima????: 85&86

MADAM POV

Kwance take kan gadon asibiti hawaye na tsiyaya daga idanunta masu ɗumin gaske

Prince Yameen ne ya riƙe hannunta yana faɗin “dan Allah Ammi ki daina kukan nan haka, kina ƙara wahalar da kanki ne” ya faɗa yana sharce hawayensa

Hannunsa da ke cikin nata ta kuma matsewa sannan tace “Yameen dole nayi kuka, wannan itace ranar da na jima ina jira tsawon rayuwata naga Yar ya hau kujerar mulki sai dai babu shi a yanzu, lallai Allah abin tsoro ne, duk dubarar mutum da ganinsa shi mai dubara ne bai isa yasanya abinda Allah bai yi ba, haƙiƙa ban taɓa tunanin rana irin ta yau ba zata zo min a haka” ta ƙare tana sakin wahallalen murmushi

Yameen kasa furta komai yayi sai hawayen da ke gudana daga idanunsa ne suka ƙara yawa

Madam nisawa tayi sannan tace “Yameen nasan bazan tashi ba, ashe haka na cutar da mahaifiyar Sydeek kafin ta mutu, ashe irin wannan wahalar na ɗanɗanawa mahaifinku kafin ya bar duniya, kaicona! Na cutar da mutanen da basu taɓa nufata da sharri ba saboda son abin duniya, Yameen cikina zafi yake, ji nake kamar ƴan hanjina na katsewa saboda azaba, haƙiƙa nayi danasanin yanda na gudanar da rayuwataaa!!” Ta saki wani wahallalen kuka sannan ta ɗora da cewa “Yameen duk nice silar lalacewarku, ni na ɗaura Yar kan muguwar turba, nasan ɗan uwansa na matuƙar ƙaunarsa yakan sadaukar da komai nasa dan ya faranta ranku ku ƙannensa, amma sai na cusa muku ƙiyayyarsa a cikin zuciyarku, nayi nadama! Yanzu ina Yar yake?, babu wanda yasani, babu wanda ya san halinda yake ciki, nice sila, na cutar da ku Yameen, ku yafemin” ta ƙare tana sakin sabon marayan kuka

Yameen riƙe hannunta yayi yana faɗin “ki daina kuka dan Allah, baki min komai ba mahaifiyata”

“Yameen da na kula da tarbiyyarku kamar yanda Allah ya ɗoramin da baka kamu da wannan cutar ba, da baka sha giya ka nemi mata ba, da ƙila yanzu kana kan neman ilimi!” Ta faɗa cikin tsantsar nadama da ƙunar rai

“Ayyah mahaifiyata! Shin ya muka iya da layin ƙaddara idan ya shata?, wa ya isa ya goge rubutun ƙaddara idan ya zana?, wannan ƙaddararmu ce kuma lokaci bai ƙure mana ba, ina ji a jikina Allah zai amshi tubanmu” ya faɗa hawaye masu mugun ɗumi na sauko masa

“Ashsha! Yameen tabbas kai kanada lokacin tuba, amma ni a yanzu lokaci ya ƙure min, ta ya ma zan fara roƙon Allah ya fiya dan ni nafi kowa rashin kunya da tsageranci, ban tunasa ba sai da na zo gargada, sai da na jiyo ƙamshin mutuwa zan tuno da shi, shi ɗin abin wasa ne!?, kaico! Mai zan je nace wa ubangijina, da wani ido zan dubi bayin Allahn da zasu biyoni filin ƙiyama suna tambayata mai yasa na kashesu, nayi nadama ɗana!, na cutar da jama’a, na cutar da mijina, na cutar da ɗana, na cutar da kaina!, ashe haka zafi da radaɗin mutuwa yake! Banida tabbacin azabar da suka sha dan basu iya magana nikuma gani da bakina, kaicona!! Yameen zaka roƙa mini gafara idan na mutu kamar yanda kowanni ɗa ke roƙa ma iyayensa?!” Ta faɗa tana riƙe hannunsa tareda sakin wani kuka mai taɓa ran mai sauraro

Princess Zairah da ke gefenta fashewa tayi da kuka tana faɗin “dan Allah ki daina maganganun nan cuta ba mutuwa ba ce, ni tsorata ni kikeyi”

Kama hannunta Madam tayi sannan ta kama da Yameen da ɗayan tace “ku tuba! Ku tuba tun lokaci bai ƙure muku ba, ni tawa ta ƙare amma ku kunada sauran dama, kuyi tuba na gaskiya kar ranar mutuwarku ta zame muku ranar baƙincikinku kamar yanda ta zo min, ku yafeni dan Allah!, Zairah a raba aurenki domin jikina ya bani Yar ya tafi kenan kiyi aure wani wajen ki samu kwanciyar hankali, na cutar da ku dan Allah ku yafemin”

Prince Yameen kuka ya fashe dashi tareda ƙanƙameta yana faɗin “dan Allah ki daina cewa haka, in kika tafi wa nake da shi?, dan Allah kar ki tafi ki barni!!” Ya ƙare cikin kuka mai karya zuciya

Hannunsa ta riƙe gam tana faɗin “Yameen zan tafi ba dan na so ba, zan tafi cikeda tausayinka ɗa na, ka bi Allah ka bi manzonsa sannan ka bi yayanka, zai zame maka gata, zai riƙeka da amana, yana sonka Yameen halinka ne baya so, ka canza! Sai ku zauna lafiya, kayi aure idan Allah ya haɗaka da mai cuta irin ta ka ko kuma cikin waɗanda kukayi mu’amala da su ka nemo wata ka aura, Allah yayi maka albarka ɗana” ta ƙare tana sakin wani tari da ke tahowa da jini

Tari take babu tsayawa jini kuma bai tsaya da gudana ba, ta ɓarar da jini da dama kafin tarin ya lafa, jikinta yayi laƙwas babu kuzari sai raba ido take tana kallonsu hawaye na tsiyaya ta kwarmin idonta

Bayan likita ya sanya mata ƙarin jini, Yameen ya matsa kusada ita tareda riƙe hannunta, wani mugun sanyi ya ji tamkar an sanya hannunsa cikin ƙanƙaru dan sanyi

Sun ɗauki minti sama da talatin baka jin ƙarar komai sai shashekar Princess Zairah da ke tashi

Madam da ke kwance tana tsiyayar hawaye wata firgita tayi jikinta ya ɗauki kyarma, kafin minti goma sha biyar rai yayi halinsa

Innalillahi wa’ina ilaihi raji’un, duniya ba matabbata ba, kowa yayi ɗamara dan duniya to ya kwanceta domin babu wanda yakeda tabbacin lokacin da zata datse masa jindaɗinsa ya tafi inda babu wanda ya isa ya dawo da shi, a chan kuma ya girbi abinda ya shuka, khairan ko sharran kowanne kayi shi zaka gani a ƙoƙonka, Madam ta tafi inda babu mai cetonta sai aikinta, ta san da zata mutu a yau?, amsar itace a’a, babu wanda ya san ranar mutuwarsa ka kan ɗauki burika da dama ka ɗaurawa ranka, wasu burikansu kan sanya su shagalta su manta cewar akwai mutuwa kuma ita bata sallama, kwatsam take zuwa a bazata kuma bata maka lamuni daidai lokacin tafiyarka zatayi gaba da kai batareda ta maka lamunin lokaci ka kimtsa ba, Mutuwa! Mutuwa!! Mutuwa!!! Kina zuwa batareda sallama ba, kina zuwa batareda an shirya ba, kina zuwa batareda anyi maraba da ke ba, Mutuwa!!!! Mai yankan ƙauna, Mutuwa!!! Mai datse bururrikan da ba’a cikasu ba, Ɗan Adam!!! Ajizi ne, ya kanyi mantuwa ya shagala da Duniya!!! Duniya!!! Ba matabbata ba ce, Duniya! Rigar aro ce!! Kowa sai ya barta. Allah kayi mana kyakyawan ƙarshe

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button