Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

Ad

_____

Prince Sydeek ɗan jinjina kai yayi sannan yace “baka gani akwai hatsari na sake masa kuɗi dayawa haka”

“No, bakomai fa mutumin is trustworthy” cewar Prince Yar

“Fine, you can go” ya faɗa

Miƙewa Prince Yar yayi yana faɗin “a huta lafiya”

Sosai nakejin kamar na shaƙesa ya faɗamin zancen da sukeyi a kai amma sanin babu hali na ja na zauna inata saƙe saƙe

Prince Yar ne da ya kai ƙofa ya juyo ya dubeni yace “ke kije side ɗina wajen Zairah kice nace ta baki sabon set na kayan cin abinci, ki dinga masa amfani da su sannan ki kula kar su fashe coz they are expensive” ya faɗa yana ficewa bai ma jira amsata ba

Duban Prince Sydeek nayi sai naga ya lumshe idonsa

Gyaran murya nayi nace “abincin fa?”

Bai tanka min ba sai miƙewa da yayi ya koma bedroom ɗinsa

Taɓe baki nayi nace “kayiwa kanka” na jawo abincin na ci nayi nak sannan na nufi kitchen

Bayan na wanke na kuma gyara abinda na ɓata na nufi sashen Prince Yar

A parlor na taddata ana mata gyaran farce, tsugunnawa nayi nace “barka da safiya”

Bata amsa min ba sai kallo da ta fara aikomin wanda ke nuni da tana tsananin bege na

Kaina na sadda ƙasa inata addu’ar Allah ya kareni daga sharrinta sannan nace “dama Prince Yar ya aikoni ki bada kwanuka”

Bata tanka ba kuma bata daina kallona ba har aka gama, bayan angama ne ta dubeni tace “biyoni”

Gabana na mugun faɗuwa na bi bayanta har muka kai ɗakinta, hannu ta ware tana faɗin “zo gareni”

Nufarta nayi inata addu’a, rungumeni tayi tsam a jikinta tana ta goga boobs ɗinta jikin nawa, mun jima a haka kafin ta sakeni tana maida numfashi

Ta jima zaune a kan gado sannan ta miƙe ta nufi wani ɗaki dake cikin bedroom ɗin, ta ɗan jima sai gata ta dawo da kwanukan masu yawa wanda suke ɗaure cikin silk material, dubana tayi tace “dukkan abinda yake buƙata tun daga spoon har knife kiyi masa amfani da wannan, amma kada ki sake ki ɗanɗana da cokali a kwanon da yaci” ta faɗa

Kaina a ƙasa na kasa bata amsa ina tunanin dalilin haka

Tsaki ta ɗanyi sannan tace “nace miki hakane saboda baki kai matsayin da zakuyi sharing da shi ba, so ki riƙe wannan”

Murmushi nayi sannan nace “nagode sosai, Insha Allah zan kiyaye”

Gyaɗa kai tayi sannan tace “in kin samu time ki dinga shigowa ko wasa nayi da ke” ta ƙare da smile

Murmushi nayi nace “toh” na ƙare ina ɗaukar kayan masu nauyi

Na juya zan fita kenan naji hannunta a kan waist ɗina, shafa buttocks ɗina tayi tace “kizo anjima” cikin raɗa

“Toh” nace ina mai jin tsanarta, banda iskanci maye na taɓamin bombom, haka na bar wajen ina yaba kwartanci na wannan mata

Bayan na koma kitchen ɗin na jera komai inda ya dace sannan na dawo parlor na zauna kallo

Misalin sha biyu ya fito cikin jallabiya, ganin kamar fita zaiyi na miƙe ina faɗin “mai za’a dafa da rana?”

Bai ko kalleni ba ya fice

Tsaki na ja bayan fitarsa nace “kayiwa farar fuskarka mai kama da aljanu”

Bayan ya samu kamar minti goma da fita na miƙe na nufi hanyar bedroom ɗinsa, na murɗa ƙofar kenan. …..

WE WILL SOON EXHAUST OUR FREE PAGES

FREE PAGES NA GAF DA ƘAREWA

KU NEMENI TA 08167888934 DAN SUBSCRIBING

S A R K I IS NOT FOR FREE
[11/9, 06:05] Mss Flower: 🤍 S A R K I

By Mss Flower🌸

SIMILARITIES AND RESEMBLANCE OF STORY/LIFESTYLE IS COINCIDENTAL

FEW FREE PAGES REMAINING AFTER THIS PIECE

NUMBER ITA CE 08167888934, TA NAN ZA KI TUNTUƁENI DAN KI BIYA ACCESS FEE

𝐇𝐈𝐒 𝐐𝐔𝐄𝐍𝐂𝐇🥀

          *17&18*

Ina murɗa ƙofar sai naji ta a rufe gam, cigaba da murɗawa nayi amma a banza, tsaki na ja nace “mara gaskiya akwai, i will make sure na saka maka ankwa in har kai mai laifina” na ƙare ina hissing na bar wajen

Ganin babu abinda zanyi ne ya sanya na kwanta a doguwar kujerarsa tuni kuwa bacci yayi gaba da ni

Ina cikin bacci kawai naji zubar ruwan sanyi a jikina, a firgice na farka

Wani kallon wulaƙanci ya fara bi na dashi fuskarsa na a yatsine, duk da zuciyata da ta hassala bai sanya na nuna a fuska ba sai murmushi nayi, tau ya zanyi aikinmu ya gaji haka wani zubin ma a mahaukaci kake zuwa kayita tsince tsince a bola dan samun bayanai

A ƙyama ce kuma a sanyaye yace “mai yasa kika kwanta min a kujera?”

A raunane idona na kawo ruwa nace “dan Allah kayi haƙuri banyi tsammanin bacci zai kwasheni ba”

“Daga yau kada ki kuma zama a inda nake ko taɓa wani abu nawa, har ta kayan gidana make sure kin saka gloves kafin ki taɓa musamman kitchen utensils” ya ƙare yana hissing ya bar wajen

Wasu hawayen takaici ne ya gangaromin, ba wai dan naji zafin zancensa ba kawai yanda naga yake ƙyamata ta kamar wani sabon tutu ya baƙanta raina

Tsaki na ja sannan nace “make sure kinsa gloves yen yen yen yen, murya kamar aku kuturu”

Toilet na masu aiki na shiga na ɗauro alwala nayi sallah sannan na shige kitchen

Ban wani ƙware a girki ba especially arabian ones, so sai nayi deciding making simple one da Mom ke yawan yi, Lentil stew nayi, consisting of slow-cooked lentils with a sprinkling of burghal and caramelized onions, sanan na haɗa masa zesty cabbage salad da zaiyi going da abincin (Arab dishes ne, don’t ask me mene na lissafo)

Murmushi na saki bayan na gama coz by mere looking abincin zaiyi daɗi, banyi tasting komai ba na juye masa a kwanukan da na ɗauko ɗazu, sannan na jeresu kan dining nayi covering na fice da niyyar bazan sake shigowa ba sai gobe

Ficewa nayi na nufi side ɗinmu, ina ƙoƙarin buɗe ƙofa naji Salamat ta kwashe da dariya cikin shewa tace “wallahi in dai zaka cika alƙawari zaka sameta”

Taɓe baki nayi na tura ƙofar, cikin sauri ta kashe wayar, kallonta nayi sai naga tayi min murmushin marasa gaskiya

Ban tankata ba na samu waje na zauna

Tasowa tayi ta dawo inda nake sannan tace “Batool inaso muyi magana da ke”

Dubanta nayi sannan nace “ina jin ki”

“Kafin nan dai amshi wannan” ta ƙare da miƙomin wani jewellery case

Buɗewa nayi, sarƙa da ƴan kunne masu kyau matuƙa kuma wanda kallo kawai ya isa ka gane tsadaddu ne

“Na meye?” Na tambaya

“Prince Yameen yace na baki” ta faɗa da smile a fuskarta

Kallonta nayi nace “dalili?”

“Yana son ki ne” ta ƙare da murmushi

Wani mugun kallo na watsa mata sannan nace “ke ba son shi kike ba?”

“Son shi nake” ta bani amsa

“Meyasa kike haɗani da shi toh” na tambaya

“Saboda son da nake masa ya sanya ina son abinda yake so” ta faɗa tana riƙe hannuna

Tsaki na ja na janye hannuna tareda miƙewa

Cikin hanzari ta miƙe tace “dan Allah ki amince da shi ko na kwana ɗaya ne” ta faɗa

Harara na watsa mata sannan nace “bakuda hankali daga ke har shi”

Cikin fushi tace “gara ki je da ƙafarki da son ranki” ta faɗa

“Idan na ƙi fa?” Na faɗa ina kwaɗa mata case ɗin

“Wallahi tallahi bilahilazim Prince Yameen bai taɓa son abu ya rasa shi ba, dole ya sameki Batool dole ya shiga hole ɗin da kike rufewa, na miki alƙawari” ta faɗa tana wular da case ɗin kan gadonta haɗe da ficewa cikin fushi

Dafe goshi nayi nace “ya rabbb nagaji da case ɗin Yameen da Zairah ɗin nan, Allah kayi min maganinsu” na ƙare ina shigewa toilet dan wanka zuciyata fal tunanin abinda Salamat tace

WILL IT HAPPEN❓BATOOL AND PRINCE YAMEEN?😂🤣 LET’S HOOK IN PAID GROUP. HAHAHHAAA

CONTACT 08167888934 TO SUBSCRIBE

S A R K I IS NOT FOR FREE
[11/9, 06:05] Mss Flower: 🤍 S A R K I

By Mss Flower🌸

SIMILARITIES OR RESEMBLANCE OF STORY/LIFESTYLE IS COINCIDENTAL

PLEASE IDAN BA KI SHIRYA PAYMENT BA KAR KI BIYONI, DON’T WASTE OUR PRECIOUS TIME IDAN KUMA KUƊIN NE YA MIKI TSAURI KI NEMI RAGI BUT KAR KI BIYONI DAN KI MIN ASARAR LOKACI NA ROƘEKI🙏

Ad

_____

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button