SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

Gabana na faɗuwa na ƙarasa wajen, tsaye na gansa a parlor yana ƙarewa ko ina kallo

Gabaɗaya parlorn a hargitse yake, an birkice komai hatta kujeru a jirkice suke an yayyaga ƙasansu

“Innalillahi wa’ina ilaihi raji’un” kawai na furta

Prince Sydeek juyowa yayi ya ƙureni da ido kafin ya wuce hanyar ɗakinsa da sauri

Nima cikin saurin na rufa masa baya ƙirjina na dukan uku uku

Nan ɗin ma a birkice yake komai an hargitsa

Tsantsar tashin hankali ne a ƙwayar idonsa amma hakan bai sanya ya rasa nutsuwa ba, a hankali ya fara bin takaddun da ke baje a ƙasa yana dubawa

Ya ɗauki lokaci a hakan kafin ya zauna tareda dafe kansa yana faɗin “innalillahi wa’ina ilaihi raji’un”

Jiki a sanyaye na matsa kusada shi na tsugunna nace “meya faru?”

Ɗago idanunsa yayi ya zuba a kaina sannan yace “meyasa kika hanani kwana a nan jiya?”

A sanyaye nace “hankalina ne bai kwanta da hakan ba, saboda furucin da Prince Yar yayi min daren jiya na tabbatar za’a zo nan ɗin”

“Sun kwashe min komai, basu bar min takaddun komai na ba, zan iya rasa komai nawa” ya faɗa a sanyaye

Shiru na ɗanyi nace “a ina kake ajiye su takaddun masu muhimmanci?” Na faɗa

Idanunsa ya maida kan wani ƙaramin safe batareda yace komai ba

“Suna waje na” na faɗa idona a kansa

Cikin mamaki yace “kamarya?”

“In dai iya na chan ɗin ne duka na kwashe su jiya bayan fitarka” na faɗa da murmushi a fuskata

Wani sihirtaccen murmushi ya saki wanda ya bayyanar da wushiryarsa mai matuƙar kyau, dimples ɗinsa masu kyawun gaske sannan ya sanya hannu ya rungumeni

Wani baƙon yanayi ne ya ziyarceni, gudun zuciyata ya ƙaru sosai

Cikin sanyin murya yace “da me zan saka miki?, kin min abinda baki ba zai iya gode miki ba”

Murmushi na saki sannan na fara ƙoƙarin janye jikina daga nasa

“I’m sorry, i was over excited, i don’t mean to harass you” ya faɗa a sanyaye

Murmushi na saki sannan nace “it’s okay” ina miƙewa tareda ficewa har lokacin zuciyata bata daina bugu abnormal ba, fuskata kuma sai fidda murmushi ta ke

Ɗaki na koma na ɗauko mishi jakar, bayan ya amsa ficewa yayi daga palace ɗin baki ɗaya

Nima da ƙyar na gyare wajen, na wahala sosai kafin na gama

Bayan na gama sashenmu na koma cikeda nishaɗi

Bacci na kwanta ko da na koma

Bani na kuma fitowa ba sai ƙarfe bakwai kasancewar na san da wuya in yana nan

Tun daga gate na ga an gyara ƙofarsa, ajiyar zuciya na sauke ina faɗin “Allah dai ya ƙara tsarewa”

Na ɗora ƙafata kenan kan first step da zai sadani da cikin ɗakin aka rufamin kaina da bag tareda ɗaukata sukutum

Ihu na ƙwalla, ban kuma yin wani ba aka toshe min baki sannan aka fara gudu da ni, ina ji ina gani aka turani cikin mota sannan aka ja ta da gudun bala’iiiii…….
[11/17, 2:31 PM] Muslima????: 63&64

????S A R K I

PRINCE SYDEEK POV

Tsaye yake jikin cotton yana kallon harabar apartment ɗinsa hannunsa riƙe da cup na mint, ya jima a tsaye a wajen yana jiran zuwanta domin tayi masa abinci

Cup ɗin hannunsa ne ya saki sakamakon ƙarar Batool da ya ji tana gaf da shigowa ɗakinsa, ƙara ce mai nuni da neman taimako ko agaji

Cikin hanzari ya nufi ƙofar zuciyarsa na bugawa da ƙarfin gaske gudun kada wani abu ne ya sami Batool ɗin wanda yakeda tabbacin in hakanne to tabbas shine sila

Yana fitowa bai sameta ba sai dai warin takalminta, da gudu ya bi hanya amma ko kafin ya kai wata mota ta wuce da gudun bala’i wanda ya tabbatar masa Batool ɗin aka sanya a ciki

Dafe kansa yayi yace “ya rabbb why is this all happening”, cikin tashin hankali ya nufi parking lot ɗinsa bai tsaya jiran chauffeur ba kawai ya tada mota da nufin bin bayan waccan da gudun bala’i, sai dai ko da ya karyo kwana motar tayi ɓatan dabo babu ita sama ko ƙasa

Wani wawan burki ya ja dan har ya kusa buguwa da pole, dafe kansa yayi tareda kifawa kan steering motar yana faɗin “innalillahi wa’ina ilaihi raji’un, ya Allah kada ka basu ikon cutar da yarinyar nan” ya faɗa yayinda idanunsa suka kaɗa sukayi jazur

Rai a matuƙar ɓace ya fizgi motar ya juya yana faɗin “muddin wani abu ya sameta, Yarrr! I will end you with my two hands”

BATOOL POV

Munyi tafiya mai mugun nisa kafin akayi parking, yanda suka ɗaukoni haka suka kuma ɗaukata, babu jimawa na ji anyi wurgi da ni har na bugi bango

Wata ƙarar azaba na saki dan na ji zafin buguwar

Wani ƙato ne ya yaye min jakar da suka rufemin fuskata sai a lokacin na ga inda suka kawoni, wani ɗaki ne wanda ya sha ƙura babu komai a cikinsa sai yaloluwar katifar da aka wullani kanta, akwai haske amma ba tarr ba dan da wuya ka iya karatu da fitilar ɗakin

“Dan Allah mai nayi muku, mai yasa zaku kawoni nan?” Na faɗa cikeda tsoro dan fuskar waɗannan har sun fi ban tsoro sama da waɗanda sukayi kidnapping ɗina a farko

Wani daga cikinsu ne ya zare min ido yace “ke kika kuma furta kalma guda sai na zubda haƙoranki a wajen nan”

A ɗan tsorace nace “mai nayi muku ne dan Allah, wa ya sanya ku kawoni nan?”

Ban ankare ba naji saukar wani abu mai tauri da mugun zafi a fuskata, sai da nayi suman wucin gadi kafin na fahimci cewa mari ne ɗaya daga cikinsu ya wanka min

Cikin fusata rubɗeɗen ƙirjinsa har sama yake hancinsa ya kuma buɗewa tsabar bala’i sannan yace “ba ya ce kar ki kuma magana ba?, wallahi kika kuma cewa kanzil sai na ɓallaki take a nan shegiya” ya faɗa yana hura hanci

Tsit nayi na koma bango na raɓe ina tsiyayar hawaye, dan ba ƙaramin zugi gefen fuskata keyi ba

Ɗaya daga cikin su huɗun ne ya ja kujera ya zauna wanda bai yi magana ba tun shigowarmu ya zauna tareda ƙureni da ido, kashemin ido yayi sannan yace “wallahi fa yarinyar nan ta min dagani zaƙwai ce, ko na haye ne?” Ya faɗa idonsa kan wanda ya mareni

Murmushi ya saki yace “ka bari Madam ta shigo mu ji, in ta amince sai mu ɗana kawai kafin mu aikata barzahu, ko ya kuka gani?” Ya ƙare yana kallon ƴan uwansa

Dariya suka sheƙe da ita suna faɗin “tabbas” in chorus

Wani mugun tsoro ne ya cikani, tabbas daganin waɗan nan babu imani a zuciyarsu dan ko fuskarsu ta nuna hakan zasu iya aikata abinda suka faɗi, wasu hawaye ne suka saukomin a fili nace “Ya Allah save me!!!” Na ƙare ina fashewa da kuka

A haukace wanda yace kada na kuma magana a farko ya miƙe ya zare belt ya hau laftamin yana faɗin “dan uwarki ba a kiran sunan Allah a nan, ya taimakeki mu kasa kasheki ko, toh wallahi sai kin mutu dan uwarki!!”

Yayi min mugun dukan da ba’a taɓamin irinsa ba a rayuwata, na galabaita ainun, jikina yayi jaa wani wajen kuma zubda jini yake, babu abinda nake sai kuka da kiran sunan Allah

“Kai Madam ta ƙaraso fa” cewar ɗaya daga cikinsu da ke duba waya

Tare suka fice suka barni ƙanƙame da jiki ina ta faman kuka

Mintina ƙalilan naji buɗe ƙofa, ban ɗago kaina ba sai kuma ƙanƙame jikina da nayi

Tafi aka fara da dariya, jin dariyar mace na ɗaga kaina na sauke akan fuskarta

Dariya take babu ƙaƙƙautawa tana tafi, sai da ta lafa sannan tace “the brave and smart Batool is here crying, ouchhh that sucks!!” Ta faɗa tana nufoni

Cikin rawar murya, raina na matuƙar tafarfasa nace “why?” Muryata har shivering take dan ɓacin rai

Dariya ta saki sannan tace “you thought we are all dump, you start the bad play thinking you are smart, yanzu zamu nuna miki ke baki iya ba Batool, Prince Yar ke kaɗai ya sanarma zai tura part ɗin Prince Sydeek but you saved him!, huh! Batool we set a trap mu gano asalin wanda kike tare da shi and you fall sweetheart!!” Ta faɗa tana shafa gefen fuskata da na tabbata yayi jaa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button