SARKI HAUSA NOVEL

“I’m talking!” Ta ce
“Eh..Eh yana ci sosai” na bata amsa
“Fine, kar ki manta da ƙa’idojin, zaki iya tafiya” ta faɗa
Gyaɗa kai nayi sannan nace “toh, nagode” na miƙe
Ina fita Prince Yar ya biyoni, tsayawa nayi da ya kirani har ya ƙaraso inda nake
Da murmushi yace “sorry about my mother, tana son Prince Sydeek ne dayawa shiyasa kika ga ta rikice” ya faɗa
Murmushi nayi sannan nace “ai bakomai wallahi”
Gyaɗa kai yayi yace “kije, sai mun haɗu” ya faɗa yana komawa ciki
Ɗaki na koma na sha baccina, ranar da wuni bacci nayi sallah kaɗai ke tadani sai after magrib na miƙe na nufi sashen Prince Sydeek duk da nasan bawani abun zanyi masa ba
Zaune na gansa kan kujera yana kallon window ya bani baya, “barka da dare” na faɗa duk da nasan ba zai amsa ba
Bai amsa ɗin ba kuwa, ganin yanayin na sanyi ne ya sanya nace bari na haɗa masa tea ko zai sha
Kitchen na nufa na haɗa masa tea da ya sha kanumfari da citta na matsa lemon sai tashin ƙamshi yake, kiwi salad nayi masa sannan na fice
Zaune na gansa kan kujera ya bar window ɗin, ajiye masa nayi kan center table sannan nace “ga tea da salad”
Banza yayi nikuma na miƙe na koma kitchen dan gyara inda na ɓata, bayan nagama na fito
Idanunsa lumshe nagani hannunsa riƙe da cup ɗin, kiwi salad ɗin ma ya ci dayawa, murmushi na saki sannan na koma bayan kujera na zauna ina jiran ya gama
Ya ci salad ɗin dayawa sannan ya shanye cup ɗin duka ya miƙe ya bar wajen, nima tattare kayan nayi duka na wanke sannan na fice daga part ɗin
Ina ƙoƙarin shiga part ɗinmu wata maid tace “ke ce Batool ko?”
“Eh” na faɗa ina mata kallon sani
“Yawwa, tun ɗazu nake nemanki, Princess Zairah ta aikoni kije yanzu” ta ƙare tana juyawa
Tsaki na jaa sannan na wuce na bi bayanta muka shiga
Ɗakin Princess Zairah ɗin na nufa fuskata babu walwala
Zaune take kan kujera ana mata gyaran gashi, cikin sauri ta waiwayo da ta hangoni ta madubi sannan ta cewa mai gyaran gashin ta fita
Miƙewa tayi da dariya tace “Batool ina kika shige, tun rannan baki kuma zuwa ba”
“Ina nan” na bata amsa ina mazewa
“Well, come here” ta faɗa tana ƙoƙarin rungumeni
Hankaɗata nayi dan abinsu ya fara isa ta, sannan nace “mai zan miki?”
Murmushi tayi tace “let’s romance” tana ƙara ƙoƙarin rungumoni
Cikin fushi na kama hannunta haɗe da murɗewa sannan nace “ni ba ƴar iska ba ce, kinyi na farko kinyi na ƙarshe ki fita a sabgata wallahi ko na miki tozarcin da baki taɓa tunani ba”
Wani mari ta ɗaukeni da shi tana faɗin kalmar “ni?!” Irin abin ya bata mamaki
Tana sauke hannunta nima na wanka mata sannan nace “ke ɗin, banza jahila mara tsoron Allah, in kinyi da wata kinci riba ni wallahi asara zakiyi dan sai na miki abinda baki zato ba” na ƙare ina nufar ƙofa
Wani ihu ta saki ta taho a guje tareda rufe ƙofar sai huci take
Tsai nayi ina kallonta ina jiran abinda take shirin yi da ta kulle ƙofa
Nufoni ta fara yi tana faɗin “na rantse da Allah sai nayi abinda nakeso da ke kuma sai na ci uwarki” ta ƙare tana damƙoni tareda ja na har kan gado
Dariya na saki sannan nace “tau, yanzun mai zaki yi?”
Bata tanka ni ba sai wurgani da tayi kan gado ta haye kaina, tana ƙoƙarin haɗe bakinmu
Naushi na sakar mata a ciki, sannan na hankaɗata ƙasan gado na cakumi wuyanta na hau girgizata, sai da naga ta jigata sai haki take sannan nace “wallahi idan kika cigaba da takuramin sai na shayar da ke giyar mamaki” na ƙare ina wancakalar da ita sannan na take hannunta na wuce
Cikin kuka da shaƙewar murya tace “na rantse da Allah Batool sai na kasheki, wallahi da hannuna zan kasheki, bazaki wulaƙantani ki ci bulus ba, wallahi sai na kasheki!!!!” Ta faɗa cikin karaji
Tsaki nayi nace “tsinanniya shege ka fasa, ni da ke aga wanda zai ci riba, a ga wanda zai ji kunya” na faɗa ina ficewa
Murmushi na saki sannan nace “welldone Anitha, daga yanzu ki ci uwarsu, duk wanda ya takaki ki taka shi” na faɗa sannan na ƙarasa ficewa daga apartment ɗin ina miming waƙar Alesia Cara
Da farinciki na kwana daren yau dan ina kyautata zaton na gama maganin Princess Zairah…..
S A R K I IS NOT FOR FREE, ITS 300 NAIRA TO 1401611541 Fatima lawal said, access bank AND THEN SEND SCREENSHOT AFTER
Or mtn recharge card to 08167888934
S A R K I IS NOT FOR FREE
[11/9, 06:05] Mss Flower: ???? S A R K I
By Mss Flower????
SIMILARITIES OR RESEMBLANCE OF STORY/LIFESTYLE IS COINCIDENTAL
TAU!!! ALLAH YAI DARE GARI YA WAYE, ANYI NA KYAUTA KUN YABA, KUN AMINCE MSS FLOWER???? TA IYA, TAU! MAI KIKE JIRA KIKA KAI YANZU BAKI YANKI TICKETI BA, GARZAYO, MA ZA HANZARTO KAR AYI BABU KE, KEMA KINJI SALON TUN YANZU NA DABAN NE, ALBISHIRINKI, WASA FA KAWAI MUKAYI BAKIN RUWA BA MU TSUNDUMA CIKIN KOGIN BA HAR WA YAU, KAR NA CIKA KU DA KAUƊI KUNSAN DALILIN DA YA SANYA YAKE NA KUƊI?, ANSA KIKE JIRA?, TAU! DALILI NE MAI ƘARFI WANDA KE SANYAWA A LEƘA GINDIN SURUKA, BA FA ZAN FASA BA!, IN KINA SON SANIN DALILIN BIYONI A PAID GROUP, BAR GANIN SUN BIYA DAYAWA ZAKI SAMU A BATI, WALLAHI IN KINYI HAKA BA MASOYIYAR BA CE BA, FAƊI KAWAI KIKE A BAKI
???????????? ????????????????????????????
LAST FREE PAGE
*29&30*
“Ya rabbb! Guide me through!” Na faɗa
Sai da na watsa ruwa sannan na fito jikina duk a sanyaye
Salamat da ke zaune tana chat ta kalleni kawai sai ta kwashe da dariya
Banza nayi da ita na fara shiri, sai dai har na gama bata daina dariya ba, da mamaki nace “lafiyarki kuwa?”
Cikin dariya tace “bazaki taɓa ji daga bakina ba”
Tsaki na ja na yafa mayafina na fice dan nasan ba hankali ne ya isheta ba
Tafiya nake sai dai hankalina gabaɗaya baya tare da ni, gabaɗaya tunanina ya dugunzuma kan yanda zan taimakawa Prince Sydeek nima na fice daga masarautar tun abu baiyi tsamari ba
“Batool!!” Cewar Prince Yar
A firgice na maida dubana kansa idona sunyi waje tsabar tsorata, na kasa motsi sai binsa da kallo nake
Da murmushi ya ƙaraso sannan yace “weldone Batool ƴar bincike, kin iya wasa, sai dai ke baki san ba’a taɓa buga wasa da ni a ci riba ba, tun ranar da na fara haɗuwa da ke nayi suspecting you ain’t an ordinary maid, kinsan meyasa?, you were so bold and brave, that’s the reason na samu kusanci da ke coz i’m hundred percent sure zaki iya aikin da nakeso, and you did it PERFECTLY!!!” yayi emphasizing perfectly ɗin tareda ƴar dariya
Shiru nayi ina kallonsa cikeda takaicinsa
“Mai kika zo bincike akai?” Ya tambaya cikin shaƙiyanci
Ni dai shiru nayi masa ina binsa da kallo kawai
“Daga ina kike, wa kikewa aiki, mai kika zo bincike akai?” Ya faɗa cikeda izgilanci
Kauce masa nayi na fara tafiya dan bansan mai zance ba, bani son kuma tsawaita maganar ka da raina ya hassala nayi wata ɓaram ɓaramar
“Dakata!!” Ya faɗa cikin ɗaga murya
Tsayawa nayi sai dai ban juyo ba, da zai barni da damuwar da nake ciki ma da ta isheni a halin yanzu
“Zan baki shawara, kin burgeni sosai tun farkon ganina da ke, maganar gaskiya kinyi daidai da irin tsarin macen da nakeso, sai dai duk yanda nake mararin abu idan naga yana neman zamar kin barazana kauda shi nakeyi baki ɗaya, shawarata gareki ki zuba ido har lokaci ya riski Sydeek idan kinyi haka kin tsira kin kuɓuta”
Cikin jarumta na waiwayo shi a fusace sannan nace “mai kake son nayi, na taimaka wajen kisan kai, na rantse da Allah duk wata hanya da zan bi dan na taimaka masa sai na bi ta, sai in har Allah ne yayi bashida rabon wuce kwanakin nan”