SARKI HAUSA NOVEL

Murmushi ya saki sannan yace “hypnosis powder, zan saki under hypnosis kinga dole ki bi umarnina da dukkan abinda nake so” ya ƙare da murmushi
“Hypnosis!!!” Na maimaita cikin tashin hankali
Murmushi ya saki sannan ya shafa fuskata yace “kar ki damu Batool, ba zan cutar da ke ba, after all i am fun of you”
HYPNOSIS
Hypnosis wani abu ne da kan sanya mutum fita daga hayyacinsa, a sanya shi yarda da abinda ba gaskiya ba ne, wani lokacin har ganin abun yakeyi ya faru a gaske, akan iya maida mutum ya zamto raƙumi da akala idan anyi amfani da hypnosis, ya kan rasa ra’ayin kansa, ya manta ƙudurin da yake da shi, wani zubin ya manta karen kansa, mutum kan zamto kamar hoto a wani zubin bayada ikon gudanar da komai face abinda aka umarcesa. Abu mafi muhimmanci bashida wani sirrin kansa duk abinda aka tambayesa babu ɓata lokaci yake faɗin iya saninsa ga wanda ya sa shi a hyypnosis
Cikin tashin hankali na hau girgiza kai yayinda na ga ya zuba garin a cikin wuta ya kuma saka mask ya rufe hancinsa
Hankalina gabaɗaya ya tashi burina bai wuce na rufe hancina ba amma babu dama domin a ɗaure nake, wasu hawaye ne suka zubomin, cikin rauni nace “dan Allah Prince Yar ka ƙyaleni, zanyi abinda kakeso ba sai ka sanyani hypnosis ba” na ƙare hawaye na kwaranyo min
“No, kar ki damu, hypnosis is the best” ya ƙare yana kawo kaskon saitin hancina nan baƙin hayaƙin ya fara shiga hancina
Wasu sabbin hawayen ne suka zubomin na hau jijjiga kai ina faɗin “please stop it”
“I’m your master, bakida maƙiyi kamar Sydeek!, kin taimakeshi ya ha’ince ki, yana kallonki lokacinda aka ɗauke ki, amma ya kasa taimaka miki, maƙiyinki ne!!!” Ya faɗa
“Nooooooo!!!!” Na ƙwalla uban ƙara daidai lokacin kaina ya hau dukan ganga yana barazanar tarwatsewa
“Sydeek maƙiyinki ne!!!” Ya faɗa cikin tsawa
“A’aaaa, ka ƙyaleni!!!” Na ƙare ina fashewa da wani gigitaccen kuka
“Batool Sydeek maƙiyinki ne, bakida wani gida da ya wuce wajena, bakida kowa bayan ni, ki riƙe wannan!!” Ya faɗa
Gabaɗaya jikina ne yayi laƙwas yayinda tunanina ya tsaya cak waje guda babu abinda nake face bin Prince Yar da ido sai hawaye da ke gangarowa kan kuncina
“Prince Sydeek maƙiyinki ne, kar ki so kowa, kar ki yadda da kowa, kar ki bi umarnin kowa sai nawa!!” Ya ƙare yana shafa gefen fuskata
Kallonsa kawai nakeyi cikin ruɗu
“Sydeek maƙiyinki ne, kin taimakesa ya cuce ki, ya bamu ke!” Ya faɗa yana gyaɗa reassuring
“Prince Sydeek?!!” Na faɗa cikin tsananin firgici
Gyaɗa kai Prince Yar yayi yace “tabbas”
“I saved him!!” Na faɗa cikeda dissappointment
“He cheat you!” Cewar Prince Yar
“Ba zai yi haka ba, he is a good person” na faɗa ina girgiza kai yayinda hawaye suka ɓalle a fuskata
Hannu ya sanya ya sharemin sannan ya ajiye kaskon ya tallabo fuskata yace “ya kamata ki ɗauki fansa ko Batool?”
Shiru nayi ƙwalƙwalwata ta cunkushe wani ɓangaren na gasgata min hakan yayinda wani na faɗamin ƙarya ne
Murmushi Prince Yar ya saki sannan ya saka hankey ya gogemin duka hawayena yace “ki daina kuka kinji, you are beautiful when you smile”
Gyaɗa kai nayi kawai batareda nayi murmushin ba
“Good girl!” Ya faɗa yana gyara min gashina da ya bazu a fuskata
“Zan sha ruwa” na faɗa cikin sanyi
“Da me?” Ya tambaya
“Hamburger!” Na faɗa a taƙaice
Murmushi yayi yace “bari na bada a siyo miki kinji Batool”
Gyaɗa kai nayi kawai
Prince Yar fita yayi ya ɗan jima sosai gashi ya dawo hannunsa riƙe da leda
Da murmushi yace “nadawo”
Gyaɗa kai nayi kawai
Warware min hannuna yayi sannan ya zaro hamburger ya bani da jarkar ruwa
Ruwan na fara sha sannan naci hamburger ɗin
Bayan na gama ya dubeni yace “Prince Sydeek mugu ne ko?”
Girgiza kai nayi sannan nace “nima bansani ba”
Murmushi yayi yace “with time”
“Na kwance ki?” Ya tambaya
Da sauri na ɗaga kai nace “eh”
Murmushi yayi yace “will you be a good girl?”
Gyaɗa kai nayi
Wani ɗaki ya kaini nan ciki sannan yace “ki kwana a nan, zuwa jibi zan maida ki ɓangarenku”
A sanyaye ba dan naso ba nace “toh”
Murmushi yayi sannan yayi pecking goshina yace “bari na je”
Sai da yayi locking ƙofar da key sannan ya wuce
Zama nayi a kan gado ina jin kaina a ƙulle, is like my memory is closed, tunani nakeson yi amma na rasa taƙamaimai tunaninma mai zanyi
Kifa kaina nayi a kan gadon na fashe da kuka ina faɗin “أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ غَضَبِهِ وَعِقَابِهِ، وَشَرِّ عِبَادِهِ، وَمِنْ هَمَزَاتِ الشَّيَاطِينِ وَأَنْ يَحْضُرُونِ” (prayers when someone is unrest, or in fear”
Na jima ina maimaita addu’ar kafin naji nutsuwa na saukarmin kaɗan kaɗan, a haka bacci yayi gaba da ni……
[11/12, 5:14 PM] Muslima????: LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI, NAIRA 300 KACAL TA ASUSUN 1401611541, FATIMA LAWAL SAID, ACCESS BANK, SAI KI YI SCREENSHOT ZUWA 08167888934, KO KUMA KATIN MTN ZUWA 08167888934
S A R K I
*35&36*
Washegari ban tashi da wuri ba dan sai wajen shida da rabi, a gaggauce nayi alwala na fara sallah sannan na zauna ina lazimi
Na jima kan praying mat ina adduo’i kafin na ɗaga, bansan dalili ba amma tabbas ina jin wani abun da bazan iya cewa gashi ba, ji nake kamar anyi locking brain ɗina bana iya tuna wasu abubuwan
Abu ɗaya ne yafi tsayamin a rai wanda da tunaninsa na kwana kuma na tashi shine kokwanto akan gasgata zancen Prince Yar, wai cewar Prince Sydeek ya bayar da ni wajensu bayan na taimaka masa
Wasu hawaye ne masu mugun ɗumi suka saukomin nace “in dai ta tabbata hakane, bazan iya yafe maka ba Prince Sydeek”
Jingina nayi na ɗora kaina bisa gadon hawaye na fita daga idona, na jima a haka kafin nace “Mom, Daddy yaushe ne zan kuma maganinku, i’m tired of this place” na ƙare wasu hawaye masu zafi na zubomin, haka bacci ya ɗaukeni
Ina cikin bacci naji an buɗe ƙofa, buɗe idona nayi na zuba ma ƙofar ido
Da murmushi ya turo ya shigo, hannunsa riƙe da leda
Kallonsa kawai nakeyi ina jin wani iri gameda shi, tabbas nasan shi mugu ne amma why do i feel like shi kaɗai ne wanda nakeda shi a duniya, like we are bind together, ya kamata naji na tsanesa kamar jiya da ranakun da suka gabata amma a yanzu bani jin tsanarsa chan dayawa sai haushi da kuma tsoronsa
Murmushi yayi min tareda rage tsawonsa, daidai fuskata yace “Batool kin tashi lafiya”
Wani mugun kallo na watsa masa sannan na maida kaina ɗayan ɓarin
Murmushi ya saki sannan yace “ga abinci ki ci, bari na zo” ya ƙare yana ficewa
Ko kallon inda abincin yake banyi ba har ya dawo shi da wani mutumi da hannunsa ke ɗauke da tray na jiya da kuma igiya
Wani malolon baƙin ciki ne ya tokaremin maƙoshi, ɓata fuska nayi sannan na watsa masa kallon banza
Murmushi yayi yace “Batool ya kamata ki karɓi dose ɗinki ko?”
“Mai kayi min?, mai yasa kakeson cutar dani ne haka, kar ka kunna min wannan abun yana cutar da ƙwaƙwalwata” na faɗa ina ƙwalla
Murmushi yayi yace “komi zaiyi daidai kinji” ya ƙare yana patting bayana
Mutumin ɗauremin hannayena ta baya yayi haɗe da ƙafafuna, babu abinda nakeyi sai hawaye har ya gama domin ko gwada ƙwatar kaina banyi ba, which is so unlike me, ni da nakeda jarumta, kafiya sai gashi na zama wata lusara sai yadda akayi da ni coz the hypnosis is controlling my mind and brain babu yanda na iya dan dole na tsaya kamar yanda Prince Yar ya umarceni
Bayan ya gama ɗaureni ya fita, yayinda Prince Yar ya saka mask ɗinsa sannan ya zuba powder ɗin ya kawota daidai fuskata