SARKI HAUSA NOVEL

A fusace na kalleta nace “ke wace irin mahaukaciya ce, angayamiki kowa ɗan iska ne irinku, toh wallahi har abada ba zai taɓa samuna ba nafi ƙarfinsa” na faɗa ina zama kan gado
“Hmmm, Batool wallahi sai Prince Yameen ya sameki, he can go to any limit akan abinda ya keso musamman mace” ta faɗa tana taɓe baki
Tsaki na ja kawai dan takaici kaɗai take bani
Bacci na kwanta, bani na tashi ba sai bayan la’asar
Tsaye naga Junnut tana murmushi, murmushin na maida mata sannan nace “kin dawo” ina ƙoƙarin tashi zaune
Zama tayi kan gadon sannan tace “na dawo, ina kika tafi ne kwana kusan uku duk hankalina ya tashi”
Murmushi nayi mata sannan nace “aiki ne yayi min yawa, ya kike?”
“Lafiya, tashi ki sallah toh, bari na samo miki abinci” ta faɗa tana miƙewa
Bayan nayi sallah naci abinci, zama nayi muka ɗan taɓa hira da Junnut har akayi magrib sannan ta fice
Bayan nayi isha’i fita nayi zuwa wajen da ke ɗebemin kewa na zauna ina shilla ƙafata, idona ne ya sauka akan apartment ɗin Prince Sydeek, ɗan jim nayi sannan nace “ko ya warke?”
Ina zaune a nan sai naji alamun an zauna a kusada ni, ɗan juyowa nayi sai na gan Prince Yar ne
Murmushi yayi min sannan yace “kina ta jindaɗi kin dawo ko?” Ya ƙare da ɗaga gira cikin sigar wasa
Murmushi nayi nima har sai da haƙorana suka bayyana
Tsai yayi yana kallona kafin ya sauke numfashi sannan yace “Batool mai nayi ne baki sona?”
Da mamaki nace “ni?”
Bai tanka ba sai shiru da yayi na wasu lokuta
Ganin shirun yayi yawa nace “nan yafi ko ina a masarautar nan daɗi”
Dariya ya ɗanyi sannan yace nan dai kika gani, tashi na kaiki wani wajen da yafi nan
Cikin zumuɗi na miƙe dan gaskiya ni inason kallon abubuwan ƙayatarwa
Wata siririyar hanya muka bi mai ɗan duhuwa, tafiyar minti uku sai gashi mun ɓulla cikin wata flower garden, flowers ne masu ɗaukar hankali
Cikin jindaɗi da tsantsar farinciki na dinga bin wajen da kallo, hannu ya sanya ya min nuni da wani ɗan ƙaramin pond
Nufar wajen nayi ina aiyyana kyawunsa
Ɗan tsugunnawa nayi ina wasa da ruwan har ya ƙaraso inda nake
“Ina son na ganki cikin farinciki” ya faɗa da smile
Miƙewa nayi nayi murmushi batareda nace komai ba na fara ƙoƙarin matsawa da wajen dan yana gaf dani
Hannunsa ya ɗora a waste ɗina, kallon ido cikin ido mukewa juna sannan ya matso da bakinsa saitin nawa
Kauda kaina gefe nayi tareda gumtse bakina
“Batool meyasa?” Ya faɗa weakly
“Ni bana so” na faɗa batareda na juyo ba
Murmushi ya ɗanyi mai sauti sannan yace “ko dai bakya so na?”
Shiru nayi ban amsa masa ba
“Na ƙara miki lokaci” ya faɗa tareda cikani
Bamu kuma tsawaita lokaci a wajen ba muka fice, wata maganar kirki bata kuma haɗamu ba haka na wuce sashenmu cikeda tunanin maganganun Prince Yar
“Na faɗawa Prince Yameen kindawo, yace kije yana nemanki” shine abinda Salamat tace ina shigowa
“Ya zo ya ɗaukeni” na faɗa ina shigewa toilet
Ruwa na ɗan watsa sannan nadawo na kwanta kan gado
Wayata na ciro daga cikin pillow dan ita ba da kayan aiki na haɗata ba sannan na turama Mom text kamar haka I MISS YOU MOM, I’M HEALTHY BUT IN NEED OF YOUR PRAYERS
Minti ɗaya da turawa sai ga reply ɗinta tana faɗin SWEETHEART CAN WE PLEASE TALK?
Miƙewa nayi na fita sannan na kirata, sosai naji damuwa a muryarta, sai da na bata assurance lafiyata ƙalau sannan ta bama Daddy wayar muka gaisa, kana mukayi sallama
Ɗaki na koma sannan na kwanta baccina batareda na bi ta kan surutan da Salamat keyi ba….
WAI NI KO DAI DAGASKE PRINCE YAR SON BATOOL YAKE NE?
[11/12, 5:14 PM] Muslima????: Washegari bayan nayi sallah baccina na koma, bani na farka ba sai wajen takwas harda rabi
Wanka na shiga sannan na shirya zuwa kitchen dan cikina har kukan yunwa yakeyi
Salamat dake zaune kan gado tace “Batool dan Allah inason muyi magana da ke”
“Yunwa nakeji bari na dawo” na faɗa ina ƙoƙarin fita
Cikin sauri tace “ga snack ki ci, dan Allah ki zauna yanzu”
Karɓa nayi sannan na zauna ina ci nace “ina jinki”
“Kinga na matsa miki ko?” Ta tambaya a raunane
“Sosai” na bata amsa ina a taƙaice
“Batool dan Allah ki taimakamin ki amince da Prince Yameen, ke kaɗai ce zaki iya taimakona, wallahi Babana bashida lafiya yana a kwance gashi kuɗin da ake buƙata dan yi masa aiki mai yawa ne, tau shi Prince Yameen yayi min alƙawarin muddin na shawo masa kanki zai amince ya bani kuɗin, kinji dalilin da yasanya nake ta takura miki, naga kinada kafiya da wuya na iya shawo kanki shiyasa na fito miki gaskiya” ta faɗa tana ƙoƙarin tsugunnawa
“Salamat, yanzu duk kusan da kuke da Prince Yameen ɗin ba zai iya taimaka miki ba, tau yanzu ke mene ribarki dan Allah, kin basa kanki kin buɗe masa ƙafarki yanzu taimakonki ba zai iya yi ba saboda Allah, kin ci riba kenan?” Na tambaya
“A’a” ta faɗa a sanyaye
“Idan nace miki zan kwanta da shi Salamat na miki ƙarya, wallahi ban taɓa zina ba kuma bantaɓa marmarinta ba, in dai sai ta wannan hanyar zan taimaka miki wallahi bazan iya ba dan banida iko” na faɗa ina miƙewa
“Batool dan Allah” ta faɗa tana rushewa da kuka
Cikin tausayawa nace “kiyi haƙuri, Allah zai kawo miki wata mafitar” na faɗa ina ficewa cikeda tsantsar mamakin rashin mutuncin Prince Yameen, ya gama tanɗe zumarta amma ba zai iya taimaka mata ba sai in ta nemo masa wata macen
Kitchen muka haɗu da Junnut, nan ta bani plate na dawo ɗaki
Tsaye naga Salamat, kallona tayi cikin rashin gaskiya
Ganin yanayinta nace “mene?”
“Babu komai” ta faɗa tareda ficewa da sauri
Taɓe baki nayi nace “Allah ya sawwaƙa”
Hannu na saka dan ɗauko wayata sai dai babu ita babu alamunta, har katifar na zazzage amma babu ita, Salamat ce ta faɗomin a rai
Cikin sauri na miƙe na nufi sashen Prince Yameen, ban ko yi sallama ba na banka ƙofar ɗakin
A firgice Salamat ta kalleni tareda ɗan ja baya, yayinda Prince Yameen ya saki murmushi yana faɗin “welcome my warrior woman”
Rai ɓace na dubi Salamat nace “ke bani wayata” ina miƙa mata hannu
Prince Yameen ne ya ɗago wayar yace “ga ta, in kinaso kizo da dare ki amsa” ya ƙare yana miƙewa haɗe da shigewa ɗaki
Ƙurawa Salamat ido nayi nace “kina daf da kawomin wuya” na ƙare ina ficewa fuuu dan ba kaɗan ba raina ya ɓaci
Ko da na koma ɗaki tunanin yanda zan amshi wayar nake batareda wani tashin hankali ya haɗani da Prince Yameen ba, dan yanzu bayan wayata mai nake da shi a masarautar nan, idan na rasata bansan lokacin da zan ɗauka ba ban gana da mahaifana ba, dan bansan lokacin barina wajen nan da ya zamemin cage ba.
[11/12, 5:15 PM] Muslima????: LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI, NAIRA 300 KACAL TA ASUSUN 1401611541, FATIMA LAWAL SAID, ACCESS BANK, SAI KI YI SCREENSHOT ZUWA 08167888934, KO KUMA KATIN MTN ZUWA 08167888934
S A R K I
*41&42*
2 days after
Misalin takwas na dare, zaune nake ina tunanin yanda zan samu wayata, dan na tabbata yanzu hankalin mahaifana ya tashi ainun
Nayi saƙa nayi warwara yafi cikin carbi, chan zuciyata ta amince min kan naje na amsa
Miƙewa nayi tareda saka after dress, Junnut da ke karatu ta dubeni tace “ina zaki haka naga ranki a ɓace?”
Yatsina fuska nayi nace “abu zanyi”
Ɗan tsuramin ido tayi sannan tace “toh ki dai yi addu’a akan komai”, ta ƙare tana maida kanta bisa littafin hannunta
Gyaɗa kai nayi sannan na nufi waje, ɗan dandamalin nan na zauna ina ɗan nazari