SARKI HAUSA NOVEL

Ban tanka masa ba na wuce, sai da na kai gate nace “tsinanne sai na saka maka curve da yardar Allah” na shige ciki
Daren ranar baccin baƙinciki nayi idan na tuna abinda ya wakana tsakanina da Prince Yar, a wani ɓarin kuma na kan saki murmushi idan na tuna cewar Prince Sydeek ya samu lafiya…..
Dan Allah kar ki karantamin book in baki biya ba. Contact 08167888934 to subscribe
[11/12, 5:15 PM] Muslima????: LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI, NAIRA 300 KACAL TA ASUSUN 1401611541, FATIMA LAWAL SAID, ACCESS BANK, SAI KI YI SCREENSHOT ZUWA 08167888934, KO KUMA KATIN MTN ZUWA 08167888934
DAN ALLAH KAR KI KARANTA MIN LITTAFI IN BAKI BIYA BA
S A R K I
*43&44*
next day
Kamar yanda na kwana da batu ɗaya na Prince Yar da cutar da yayi mini dan ba dan shi ba tabbas da nayi sati a gidanmu, tau haka na tashi da batun
Ina zaune bisa gado inata saƙa da warwara wata maid ta turo ƙofar, da murmushi tace ” Big Madam tace in kin shirya kije”, ta ƙare tana ajiye tray da ke ɗauke da kwanukan abinci
Wanka na shiga nayi sannan na maida kayana, kana na zauna cin abinci
Bayan na idar na tashi na nufi inda nake kyautata zaton zan sameta, zama nayi cikin mutuntawa na gaisheta
Da murmushi tace “Batool kin tashi lafiya”
“Alhamdulillah” nace a taƙaice
“Yawwa, Masha Allah” ta faɗa
Ɗan tsuramin ido tayi sannan ta nisa kana tace “Batool na tambayeki?”
Gyaɗa kai nayi sannan nace “eh”
“Ya akayi Sydeek ya sha poison?” Ta tambaya her eyes focused on me
Sai da na ja dogon breath sannan nace “i’m sorry, i poisoned him but it wasn’t my intention, i was deceived” na ƙare sounding guilty
“It’s okay, daga yanzu ina son ki fahimci players da zamuyi wannan game ɗin are very dangerous opponents, they are all friendly and nice but deep down they are so devlish, monsters and wicked hearts, so you have to be extra careful, don’t ever show them your true self, and mind you suna watching each and every step ɗinki, they may harm you if you got caught” ta faɗa
Ajiyar zuciya na saki coz sai yanzu na fuskanci dangerous situation da na saka kaina, i regreted coming to this palace
“Kina ji na?” Ta tambaya
Gyaɗa kai nayi sannan nace “i will be careful”
Hannu ta saka ta ɗauko envelope sannan ta miƙo min tace “da fari ki ajiye min wannan, dan Allah amana na baki, kada ki salwantar min da ita, ko ki mata riƙon sakainar kashi, ki kimlaceta kamar yadda kike kimlace jikinki” ta faɗa
Da hannu biyu na amsa sannan nace “Insha Allah, zan yi yadda kika ce” na faɗa
“Yawwa, kada ki manta kar ki sake ki nunawa Yar kina hayyacinki kuma dukkan abinda ya sanya kiyi kiyi shi sai ki kauce wanda zai cutar da Prince Sydeek”
“Insha Allah” na faɗa
Wasu awarwaron zinare ta ɗauko tareda miƙo min tace “ga wannan tukwici ne nayi miki”
Cikin fara’a na dinga godiya
Da murmushi tace “bakomai, zaki iya tafiya”
Sai da na soke wasiƙar sannan na fice daga wannan side ɗin
Ina gaf da shiga sashenmu naji wata ta riƙeni, juyowa nayi na kalleta tareda cewa “lafiya?”
Nuni tayi min da Prince Yar da ke chan nesa tace “ya na kiranki”
Wani abu ne ya tokaremin maƙogwaro take wani haushinsa ya kamani, mazewa nayi dan dole sannan na nufesa fuska babu yabo ba fallasa
Fuskarsa ba fara’a yace “ina kika je tun jiya?”
“Sashen big Madam” na basa amsa a taƙaice
“Big Madam!!” Ya maimaita
Kallonsa nayi, take na ga wani tsantsar tsoro ya bayyana fuskarsa
Sai da ya ja ajiyar zuciya sannan yace “mai tace miki?”
“Cewa tayi ko me ka sakani kar nayi” na bashi amsa, ina kallonsa ƙurr
Murmushi ya ɗan saki sannan yace “daga yanzu kome kukayi da ita ki zo ki faɗamin” ya ƙare yana wucewa
Da kallon tsana na bi bayansa har dai ya shige sannan na nufi ɗaki
Ina shiga Salamat ta yunƙuromin tana faɗin “dama Batool bakida mutunci, abinda kikayiwa Prince Yameen kinsan mai ya ja min?”
Banza nayi mata batareda na kulata ba na zauna kaina
A fusace ta ƙaraso gaban gadona sannan tace “kije ki basa haƙuri”
“Mai yayi miki ne?” Na faɗa cikin gajiyawa
“Ya ce zai zare duk tallafin da yake bani, kije ki basa haƙuri” ta faɗa ranta a ɓace
“Bazan bayar ba, tashi a kaina” na faɗa ina ƙoƙarin kwanciya
Saukar hannunta naji a bakina tana faɗin “ke mara kunya ko, to yau zan nuna miki ƙarshen rashin kunyarki” ta faɗa tana janyoni daga kwancen
Dafe bakina nayi dake min zugi, take raina ya soma ɓaci matuƙa, hannu na sanya ina ƙoƙarin raba jikina da nata sai kawai naji ta sakar min duka
A fusace na fizge jikina sannan na sharara mata mari haɗe da kama jelar gashinta da tayi kitso take reto a bayanta na damƙe na hau jijjigata ina faɗin “dan ubanki bazaki fita harkata ba ko, dan kina ƴar iska dole sai na zama irinki, wallahi idan baki fita sabgata ba kin daina dangantani da wanan soloɓiyon sai na miki mugun lahani!!” Na ƙare ina kai mata duka a kafaɗa
Ihu ta saki, daidai nan Junnut ta shigo ɗakin da gudu, da ƙyar ta raba tsakaninmu
Salamat da ke ta haki idanunta na zubar ƙwalla tace “wallahi sai na rama abinda kikayi min, baki sanni ba har yanzu ne kawai ji na kikeyi” ta ƙare tana ficewa
Junnut zama tayi kusada ni tace “haba! Batool ya zakiyi haka da hankalinki”
“Yarinyar ce ta kaini bango, in ban koya mata darasi ba bazata fita harkata ba, wai wannan yarinyar har tazo ta cakumeni da faɗa, wallahi da baki shiga ba sai na kwantar da ita in yaso daga ranar bata kuma ɗaga ido ta kalleni ma” na faɗa ina huci
“Kiyi haƙuri kinji, duka watarana sai labari ita duniyar ma gabaɗaya ba matabbata ba ce, ki dinga innalillahi wa’ina ilaihi raji’un, zuciyarki zatayi sanyi” ta faɗa tana riƙe hannuna
Gyaɗa kai nayi sannan nace “nagode “
NIGERIA
Zaune yake kan kujera a parlor yana kallo
Ayya ce ta fito daga kitchen hannunta riƙe da bowl, miƙa masa tayi tace “ungo”
Yatsina fuska yayi yace “Ayyah ni fa na gaji da cin wannan faten waken”
“Kai dallah amshi bakaga ina haɗa maka da ganyayyaki ba ne, idan baka ci ba jininka da ya ƙone ya dawo taya zaka samu kuzari ka koma” ta faɗa
“Ni fa naji sauƙi” ya faɗa batareda ya amsa ba
“Amma ai baka murmure ba, ka koma a haka ai wallenka za’a gani, Sarki maza ka ci ka ƙoshi” ta ƙare tana zama haɗe da kai spoon bakinsa
Amsa yayi yana yatsina fuska haka har ya cinye duka
“Wai ni sai yaushe zakayi aure, ya kamata ka ajiye iyali fa” cewar Ayyah
Taɓe baki yayi yace “tukunna”
“Bari dai Alhaji yazo sai na faɗa masa ya samo maka mata tunda na kula kai tsoron mata kakeyi” a faɗi tana ƙoƙarin tashi
Da sauri ya riƙo hannunta yana faɗin “no, i have someone in mind, ina jiran right time ne, please Ayya kar ki masa wannan maganar” ya faɗa yana langaɓe kai
“Wace kakeso Iyyeh?” Cewarta tana gyara zama
Ɗan murmushi yayi sannan ya lumshe ido yace “wata da tafi kowacce mace kyau, tafi kowacce kirki” ya faɗa yana blushing
Ayya miƙewa tayi tana faɗin “kai dai sarki wani zubin bakada kunya wallahi” ta ƙare tana shigewa ɗaki
Murmushi yayi mai ɗan sauti sannan yace “yaushe zan kuma ganinki?, i am eager to see you and hold you in my arms” ya faɗa yana lumshe sexy sleepy eyes ɗinsa…..
[11/13, 9:10 AM] Muslima????: LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI, NAIRA 300 KACAL TA ASUSUN 1401611541, FATIMA LAWAL SAID, ACCESS BANK, SAI KI YI SCREENSHOT ZUWA 08167888934, KO KUMA KATIN MTN ZUWA 08167888934