SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

Murmushi na saki ko da na ƙarasa inda yake

“Ina zaki?” Ya jefomin tambaya

“Tare zamu, abincinka na ɗauko maka” na faɗa da light smile a fuskata

Bai kuma cewa komai ba ya shige nima na shige gidan gaba

Bayan mun fito muna gaf da shiga ciki ya ɗan dakata sannan ya juyo ya kalleni yace “kada ki taɓa nuna akwai shaƙuwa ko wani abu a tsakaninmu, ina tsoron kada a cutar da ke dalilina” ya faɗa yana wucewa

Wani sanyi naji ya ratsani da tausayinsa ashe duk hakan da yake min kulawa ce yake bani, ni bansani ba sai aukin jin haushinsa nakeyi, ganin yayi min nisa ya sanya na bi sa da sassarfa

Bai samu shiga ɗakin ba kasancewar likita na ciki, jugum ya zauna daga shi sai Big Madam itama da ta rafka tagumi a parlorn, a hankali na ƙarasa kusada shi nace “ka ci abinci”

Bai tankani ba sai ya dubi Big Madam yace “ya jikin nasa”

Nisawa tayi tace “Sydeek jikin nasa tsananta ya kuma yi” ta faɗa a taƙaice

Jikina ne yayi sanyi nima dan nasan tashin hankalin da yake ciki ai ba ƙarami ba ne da zan tursasa shi cin abinci, dan haka nakoma ƙasan carpet na zauna ina addu’ar Allah bawa mahaifin nasa lafiya

Anjima sosai sannan Prince Yar ya shigo, wani mugun kallo ya watsawa Prince Sydeek da kansa ke sunkuye, idanunsa ne ya sauka a kaina, ɗauke kansa yayi sannan ya zauna kusada Prince Sydeek yana faɗin “ya jikin nasa?”

Prince Sydeek bai ko ɗago ba bare ya tankasa dan haka sai ya ja baki yayi shiru

Lokaci mai tsayi sai ga Madam da Princess Zairah sun shigo, Princess Zairah bata ko zauna ba ta fara min kallon wulaƙanci da ƙasƙanci, taɓe baki tayi tace “ke kuma fa?”

Cikin rashin fahimtar zancen nata nace “eh?”

“Dallah malama tashi ki fita, banda hauka mai zai kawoki nan sashen sarki kina maid ɗin cikin gida” ta faɗa a hassale

Rintse idona nayi dan wani baƙinciki da ya taso min ji nake zan iya shaƙeta

“Batool get out!!!” Cewar Prince Yar

Jiki a sanyaye na miƙe zan fita sai kuma Prince Sydeek yace “Batool go back!!”

Tsaye nayi dan sai na rasa umarnin wa zan bi cikinsu

“Bari taje wajen, kada ya zama hayaniya please” cewar Prince Yar

“Go back!!!!” Prince Sydeek ya daka min wata gigitacciyar tsawa

“Amma…” Prince Yar ya fara magana kenan Prince Sydeek ya ɗaga masa hannu yace “my words stands!!”

Shiru akayi na ɗan sakanni kafin Madam tace ” wai kai toh ubanmu ne ko kuwa kaine sarkin da zamu bi umarninka?”

Wani mugun kallo ya ɗago ya watsa mata sannan ya maida kansa ƙasa nan kowa yayi tsit

Komawa nayi na rakube nima sai yanzu nake jin dama ban biyo sa ba, kallon wulaƙanci da harara kawai Madam da Zairah ke watsomin…..

SARKI IS NOT FOR FREE, KU CIGABA DA KARANTAWA KYAUTA KUNA MIN TANADI RAN GOBE ƘIYAMA
[11/15, 12:41 PM] Muslima????: LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI, NAIRA 300 KACAL TA ASUSUN 1401611541, FATIMA LAWAL SAID, ACCESS BANK, SAI KI YI SCREENSHOT ZUWA 08167888934, KO KUMA KATIN MTN ZUWA 08167888934

IN HAR KINA KARANTA MIN BOOK BA KI BIYA BA, KIN SHIGA HAƘƘINA

S A R K I

           *53&54*

Wajen shiru ya ɗauka baka jin komai sai ƙusƙus na Madam da Zairah da lokaci lokaci suke jifana da harara

Hankalina gabaɗaya na tattaresa kacokam na ɗora kan Prince Sydeek da kansa ke a duƙe wanda inada tabbacin da wuya in ya zuba ruwa a bakinsa tun safiya har yanzu

Misalin bakwai da rabi da mintina Prince Sydeek ya tashi

Big Madam da fuskarta ke bayyanar da tashin hankali tayi maza ta kalleshi tace “ina zaka?, yana iya tashi fa yanzu”

A sanyaye yace “zanje sallah yanzu zan dawo” ya ƙare yana ficewa

Prince Yar ma miƙewa yayi ya bi bayansa batareda kowa ya kulasa ko ya kula kowa ba

Tashinsu babu jimawa likita ya fito tareda faɗin “yana neman mahaifiyarsa da Prince Sydeek”

Big Madam cikin sauri ta miƙe ta nufi ɗakin, Madam na ƙoƙarin bin ta masu jire ƙofar suka dakatar da ita

An ɗauki lokaci mai tsayi kafin wata daga cikin nurse ta kuma leƙowa tace “Batool kizo ana nemanki” idonta akan Zairah dan ƙila tayi tunanin ita ce Batool ɗin

Zaro ido nayi cikin mamaki nace “ni kuma?” Ina nuna kaina, tau ni mana an hana matarsa da sirikarsa shiga sai ni karan kaɗa miya

“Eh” kawai ta faɗa ta koma ciki

Miƙewa nayi zan nufi ɗakin ina ta mamakin abun

Da hanzari Zairah ta riƙoni tana faɗin “wallahi in har kin shiga ɗakin nan sai bayan na saka ƙafata”

Tsai nayi ina kallonta dan na gama fuskantar ita yin abun kunya ba damunta yake yi ba

Ɗaya daga cikin guard ɗin ne ya zare mata ido yace “ko ki daina ɗaga mana hankali ko ki fice, his majesty baya son hayaniya a nan”

Ba dan ranta ya so ba ta fancakalar da hannuna, taɓe baki nayi sannan na shige ciki

Zaune naga Big Madam bakin gadon tana share ƙwalla da hankey yayinda his majesty ke kwance idansa rufe amma suna tsiyayyar da ƙwalla alamun idonsa biyu

Gabaɗaya ji nayi dukkan jijiyoyin jikina sun tsinke wani masifaffen tausayinsu ya shigeni, tabbas duk wani mai imani a halin da ya ga uwa da ɗa ɗin nan duk taurin zuciyarsa dole tayi sanyi

A hankali ya fara tari cikin rashin kuzari, tarin da yake jini ne ke fallatsowa daga bakinsa, hawaye na fita daga idonsa kana kallonsa zaka shaida yana cikin tsananin ciwon da kai baka isa ka misalta ko hasaso shi ba, fuskarsa tayi fari fayau alamun rashi jini ƙarara

Wasu hawaye ne masu ɗumi suka fara saukomin, jiki a mace na ƙarasa kusada Big Madam da ke riƙe da hannunsa tana hawaye, dafata nayi cikin sanyin murya nace “mai zai hana a kaishi inda Prince Sydeek yayi treatment ɗinsa tunda naga kusan abu ɗaya ne”

Hawayenta ta share sannan tace “ba ɗaya ba ne Batool, shi ya jima yana shan poison sama da shekara biyar, ashe shi yayi sanadiyyar tsinka jijiyoyin ƙafarsa har ya maida sa gurgu, a yanzu ba shida magani sai dai jiran lokaci domin gabaɗaya kayan cikinsa sun lalace sun ƙone, hanjinsa da dama sun ruɓe” ta faɗa cikin kuka ƙasa ƙasa mai matuƙar tsinka zuciya

“Innalillahi wa’ina ilaihi raji’un” shine kaɗai abinda nake maimaitawa dan gabaɗayana na karaya jikina kuwa ji nake kamar an min ɗan banzan duka

Ta jima kafin ta numfasa sannan tace “Batool miƙomin wancan akwatin”

Ɗan ƙaramin akwati ne wanda aka yi shi da zallar azurfa a jiki dan ɓareren tambari ne na masarauta sannan aka buga hatimi aka rubuta S A R K I, gani kaɗai ya isa ya fahimtar da kai babu wanda ya isa ya mallaki wannan ɗin sai mai mulkin babbar masarauta irin wannan ɗin, cikin girmamawa harda rissinawa na miƙa mata

“Riƙe shi a wajenki, bansan meyasa ba amma ke kaɗai ce wadda zan iya yarda da ita, kinga wannan ɗin seal ne na kujerar mai martaba, ko da mai martaba ya bar wasiyyar cewa Sydeek shi zai gaje shi, bai isa ya hau gadon mulki ba muddin ba shida wannan ɗin, ki a dana waje guda da wasiƙar da na baki” ta faɗa a sanyaye

Wani nauyi ne babba naji kamar ta ɗora min a kaina, wace ni a masarautarnan ta su da har zasu tsunduma ni cikin wannan cakwakiyar, haƙiƙa matsayi ne kuma girmamawa ce a gareni ko dan aminta da ni da sukayi, ajiyar zuciya na sauke sannan nace “ji nake kamar bazan iya ba”

Shiru ta ɗanyi sannan ta juyo da dubanta kaina tace “Batool taimaka min za kiyi, akan mulki Yar da Mahaifiyarsa zasu aikata min komai dan su karɓi wannan seal ɗin, amma in har yana wajenki bazasu taɓa tunani a kanki ba, dan Allah!!!” Ta faɗa a sanyaye

“Insha Allah zan karesa da dukkan iyawata” na faɗa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button