SARKI HAUSA NOVEL

Ina ajiyewa aka turo ƙofar, Prince Sydeek ne ya shigo, wani farinciki ne ya kamani ko ba komai Yar zai ji kunya
Nuni na yi masa da ɗakinsa, ɗan kallona yayi sannan ya wuce ciki
Yana gaba na bi bayansa tareda laɓewa
“Lafiya kake min bincike a pc?” Cewar Prince Sydeek da ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallon Yar
Yar da murmushi ya ɗago sannan yace “na shigo nemanka sai maid ɗinka tace ka fita, so ina neman takaddun wannan building ɗin da ka sai min ne coz zanyi renovating ɗinsa sai kuma wani mutumi ya haƙiƙance wajensa ne shine na shigo dubawa kuma sai naga pc ɗinka a kunne that’s why na kashe maka”
“A’a wani takaddu kuma?, bayan wanda na aiko maid ɗina ta baka” cewar Sydeek yana kallonsa
Da mamaki Prince Yar yace “takaddun wajen kuma, yaushe ka aikota?”
“Zo mu je parlor” cewar Prince Sydeek
Da sauri na koma na zauna ina yaba rashin mutunci irin na Prince Sydeek ashe takaddun Yar ɗin ne ya ajiye na kai masa
“Ke!!!” Cewar Prince Sydeek
Miƙewa nayi ina raba ido sannan nace “na’am”
“Ina takaddun da kika fita da su?” Ya tambaya
“Ya. ..ya. …yana wajensa” na ƙare ina nuna Prince Yar
Prince Yar cikin tashin hankali ya nufeni tareda shaƙeni yace “yaushe kika kawo min takadda kika ce inji Prince Sydeek” muryarsa har karkarwa take saboda ɓacin rai
Ni da na ji shaƙa ina ƙoƙarin raba hannunsa da wuyana ina faɗin “bansan kawo maka yake son ayi ba” na faɗa idona sunyi jaa dan wahala
Prince Sydeek ne cikin kwanciyar hankali yace “kisan kai zakayi saboda kuɗi?”
Saki na Prince Yar yayi tareda wucewa ya zauna kan kujera yana dafe da kai
“Wai lafiya, mi kayi da takaddun?” Inji Prince Sydeek da ɗan smile a fuskarsa
“Na ….na…..na ƙona” ya faɗa
“Why?” Prince Sydeek ya tambaya
Prince Yar miƙewa yayi ya fice batareda ya tanka ba
Murmushi mai ɗan sauti Prince Sydeek yayi sannan ya miƙe ya shiga ɗakinsa, jim kaɗan ya fito
Ni da na zabga tagumi ina mamakin ƙullin Prince Sydeek naji yace “tashi muje”
Zumɓur na miƙe na yafa mayafina kana na bi bayansa…..
WALLAHI BAN YAFE BA, DA KE MAI MIN SHARING, DA KE MAI KARANTAWA DUKANKU ALLAH YA SAKA MIN
IDAN KE MAI TSORON ALLAH CE KI YI SUBSCRIBING 300 VIA 1401611541, ACCESS BANK. FATIMA LAWAL SAID OR MTN RECHARGE TO 08167888934, SAI KI TUROMIN SHEDA TA 08167888934
[11/16, 1:02 PM] Muslima????: ????S A R K I
LITTAFIN KUƊI NE DOMIN KARANTAWA TA HALATTACIYYAR HANYA KI TURA 300 TA 1401611541, FATIMA LAWAL SAID. ACCESS BANK OR MTN CARD TO 08167888934, THEN SHOW EVIDENCE TO 08167888934
IN KIKA KARANTA BA KI BIYA BA ALLAH YAYI MIN SAKAYYA
*57&58*
Sai da na kulle gidan sannan na ƙarasa mota, har muka shiga ciki bai tankani ba
A parlor na zauna ina ta saƙa da warwara duk akan haɗuwarmu da Prince Yar, na tabbata dole yayi min rashin mutunci mai aji dan yanda na fuskanceshi sam bai iya controlling kansa in yana fushi ko ransa ya ɓaci, tau bare yanzu an taɓa masa dukiya ne abinda yafi ƙauna a duniya
Ina nan zaune sai ga su Princess Zairah da Madam kana ganin fuskarsu kasan ransu a ɓace yake ainun, Madam kallo ɗaya tayi min ta shige cikin bedroom ɗin
Princess Zairah tsai tayi a kaina tana watsomin kallon tsana kana ta nisa tace “wallahi na tsaneki, ke tunda kika zo masarautarnan na fuskanci abubuwa warware mana su ke, wallahi muddin da saninki ko sa hannunki akan zaluncin da akayiwa mijina sai na tozartaki na wulaƙantaki mafi munin wulaƙanci da tozarci” ta ƙare da jan tsaki haɗe da shigewa rai ɓace
Tabbas idan nace zuciyata batayi rawa ba nayi ƙarya, ba wai na tsorata ainun ba amma tabbas naji tsoro duk da kasancewata mace mai jarumta
Ban gama samun nutsuwa ba Prince Yar ya shigo, kallo ɗaya nayi masa na duƙar da kaina domin tabbas ransa a tsananin ɓace yake, babu fara’ar da ya saba, fuskarsa fidda baƙincikin da yake ciki take yayinda idanunsa ke nuni da ƙaguwar da yayi dan ɗaukar fansa
Kallona yayi sosai sannan ya wuce ciki batareda ya furta uffan ba
Wani irin kaɗawa hantar cikina tayi domin wannan ne karo na farko da ya taɓa min irin haka duk kuwa fushin da yake yi dani, lokaci mai tsayi kafin naji ƙarar buɗe ƙofa
Prince Sydeek ne ya fito cikin saurin masifa, tsantsar tashin hankali ya bayyana kan fuskarsa
Cikin sauri na miƙe na bi bayansa ina faɗin “lafiyarka kuwa?”
A ruɗe yace “zan nemo native doctor ne, jikinsa yayi tsanani” ya ƙare da ficewa a guje
Waje na samu na zauna tareda rafka tagumi ina tunanin duniyar nan da na shigo, sai a masarautar nan na tabbatar mulki mugun abu ne, in har ka haushi bakada zaman lafiya, daɗin daɗi kan abin tsoron shine ƴa ƴanka na maka fatan mutuwa dan su gaji kujerarka haka zalika matanka burinsu ka shura dan ɗan cikinsu ya hau gadon mulki, duk sunyi makkuwar cewa ita duniyar ba mattabata ba ce, RIGAR ARO ce, kowa sai ya barta babu wanda za’a bari, ko mutum na so ko bai so wallahi shima sai yaje inda ake zuwa, kaje ka karɓi hukuncin abinda ka aikata walau mai kyau ko akasinsa
Ina tsaka da wannan tunani naji an zabga ihu, take sautin kukan mata ya fara tashi daga cikin ɗakin
Miƙewa nayi dan shiga ciki na gano abinda ke faruwa sai kuma na fasa nayi zamana gudun matsala
Kuka ne kawai ke tashi daga na jinin sarautar har ma’aikatan da ke ciki ko ba’a faɗi man ba nasan lokaci ne ya cimma his majesty, wasu hawaye ne suka gangaromin tuno halin da Prince Sydeek zai shiga idan wannan mummunan labarin ya riskesa
Mintina talatin guards suka fara kiciniyar kulle dukkan ƙofofin cikin sashen mai martaba, mu na ciki bazamu fita ba haka na waje bazasu shigo ba
Bayan awa biyu sai ga Prince Sydeek ya shigo hankalinsa a matuƙar tashe bayansa wani tsamurmurin dattijon balarabe riƙe da akwatu, tabbas yanayinsa ya nuna ya ji zancen mutuwar to amma yana cikin ruɗu da tashin hankali dan kamar bai gasgata hakan ba
Miƙewa nayi na bi bayansu zuciyata na bugawa da mugun gudu na tsoron irin karɓar da zaiyi ma wannan rashin da yayi
Jikinsa ne yayi mugun sanyi yayi laƙwas ganin an rufe mahaifin nasa da farin ƙyalle, jiki babu ƙwari ya ƙarasa tareda yaye mayafin, rintse idonsa yayi kana yace “innalillahi wa’ina ilaihi raji’un”
“Sydeek ya tafi ya barmu, mutuwa bata kyauta mana ba” cewar Madam tana fashewa da kuka
Hannu ya ɗaura ya dafe kansa tareda zubewa ƙasa daɓas ya kifa kansa kan gwiwoyinsa
Wasu hawaye ne suka kwaranyo min masu ɗumi, haƙiƙa Prince Sydeek na tsananin bani tausayi bani son ganin damuwarsa duk ƙanƙantar ta
Prince Yar ne yace “ya kamata a shaidawa mutane ya rasu dan jama’a su fara zuwa”
“Ka sanya a busa trumpet” cewar Madam
Yana share hawaye ya fita, mintina ƙalilan sai ga tashin ƙara ta karaɗe ilahirin masarautar wanda na tabbatar ana shaida mutuwar sarkin ne
Prince Sydeek wata zabura yayi ya nufi gawar mahaifinsa yana faɗin “Abbu ka tashi dan Allah, Abbu ka tashi ka faɗa masu baka mutu ba” ya ƙare yana jijjiga mahaifin nasa har ƙyallen da aka rufe masa fuska ya yaye, kyakyawar fuska mai ɗauke da murmushi ta bayyana
Big Madam ce ta riƙe hannun Prince Sydeek tana faɗin “a’a Sydeek ka daina kai namiji ne, kayi haƙuri, addu’a yake buƙata a halin yanzu” ta ƙare itama cikin kuka
“A’aaaa bai mutu ba, Abbu ya na da rai suma yayi” ya ƙare ƙwalla na ɗigo masa
Cikin hanzari Big Madam ta share masa tace “a kull na kuma ganin hawayenka bayan kai ne zaka zama shugabanmu”