SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

“Tun kafin su shigo nayi hakan gudun abinda zasu iya aikatawa, and you were busy shiyasa ban ba ka on time ba” ta faɗa idanunta kan hannunta da take wasa da shi

Kallonta yayi yana mamakin ƙwalwarta, like she is brainy, gifted and brave, ita ce macen da ya taɓa ji ta burgesa a tsawon rayuwarsa, calmly yace “thank you”

Murmushi kawai tayi batareda tace komai ba, shiru motar har suka isa shopping mall

Batool ce ke bayansa yayinda ya shige gaba, ji tayi kamar ana kallonta

Juyawa tayi, caraf idonta ya sauka kan wasu matasa da suke sanye cikin cikin kayan sanyi baƙaƙe sun ɗaura facing cap tareda rufe rabin fuskarsu da face mask

Wani tsoro ta ji ya shigeta zirrr lokaci guda, “auzubillah” ta furta tareda shigewa ciki da sassarfa

Prince Sydeek da ke tsaye yana kallonta ya girgiza kai sannan yayi gaba

Binsa tayi a baya yana ta ɗaukan perfumes kala kala

Dubanta yayi yace “ki ɗauki abinda kikeso” sannan ya cigaba da harkar gabansa

Basket ta ɗauka ta shiga lodar biscuits da chocolates sannan ta ɗibi pack na pad guda biyu

Bayan sun gama siyayyar suka je payment Prince Sydeek kallonta yayi ganin junks ne ta kwaso kawai ya girgiza kai

Idanunsa ne ya sauka kan ledar pad ɗin, ɗauka yayi out of curiosity ganin abinda aka rubuta ya dire shima da ƴar kunya a fuskarsa

Batool kam wata masifaffiyar kunya ta ji ta rufeta kamar ta nitse, bayan sunyi payment suka fito

Batool ganin waɗan da ta gani ɗazu suna ta raɓe raɓe jikin building da ya ƙone kusada shopping mall ɗin gabanta sai da ya kuma yankewa ya faɗi

Gani tayi ɗaya daga cikinsu ya zaro bindiga ya saita Prince Sydeek da ke tsaye yana amsa waya

A guje ta nufesa tareda hankaɗasa ta shiga, nan bullet ɗin yayi piercing

PRINCE YAR POV

Prince Yar da ke kwance kan gado Princess Zairah na gefensa kwashewa yayi da dariya tareda cewa “yanzu na san wancan tsinannen ya mutu ko yana gaf da mutuwa” ya ƙare da sakin smile

Princess Zairah murmushi ta saki tace “ka ga dole wannan tsohuwar ta bada seal ko tana so ko bata so, and for that Batool girl da ta zame mana obstacle da hannuna zanyi maganinta” ta ƙare tana kwanciya jikin Prince Yar

“Ya sace min duka kuɗin da na mallaka, ni kuma zan ƙwace dukkan abinda ya mallaka yanzu, zan ƙwace throne ɗinsa sannan na ƙwace ransa” ya faɗa yana sakin smile

“Throne ɗinka dai da yake son sacewa” cewar Princess Zairah

Murmushi ya saki yana faɗin “for sure”

“Ka san mai nake so idan ka hau kujerarka?” Ta faɗa

“Komai kikeso shi za’ayi my queen” cewar Prince Yar

Murmushi ta saki sannan tace “inason na zama in charge of accepting and posting kowacce maid a masarautarnan”

“Wai shikenan?” Cewar Prince Yar suprised ganin buƙatarta ba wata abu ba ce

Dariya tayi tace “shikenan”

“Kinsamu” ya faɗa yana janyota jikinsa

Wayarsa ce tayi ƙara, dubawa yayi tareda faɗin “Prince Sydeek is no more” yana ma Princess Zairah murmushi sannan yayi picking call ɗin. …..

[11/19, 10:17 AM] Muslima????: 73&74

LITTAFIN KUƊI NE, 300 NAIRA VIA 1401611541, FATIMA LAWAL SAID. OR MTN CARD TO 08167888934

????S A R K I

BATOOL POV

Bullet ɗin piercing jikin window yayi sakamakon hankaɗani da Prince Sydeek yayi na tsugunna

A firgice na ɗago kai ina kallon wajen, sai dai mutanen sunyi ɓatan dabo dalilin jama’a da sukayi caaa haɗe da securities jin ƙarar bindiga

Hankali a matuƙar tashe ya janyoni yana faɗin “are you alright?” Ya ƙare yana dudduba jikina cikin tashi hankali

Murmushin ƙarfin hali nayi, tau na ƙarfin hali mana na tsallake rijiya da baya, na tabbata da ba dan ya tureni ba yanzu wani batun ake ba wannan ba

Chauffeur ɗin cikin tashin hankali ya zagayo yana mana sannu tareda buɗe mana mota muka shiga

Period kuwa ɓallemin yayi, Allah ya taimakeni bana rushing sai dai ya tsaya a inner wears ɗina, har muka ƙarasa babu wanda yace kanzil

Tunanina ya ta’allaƙa kan yanda za’ayi na kama Prince Yar cikin ƙanƙanin lokaci domin abinda yake yi ya fara isata haka, it’s high time ayi ending problem ɗinsa

Bayan mun ƙarasa gida, ɗaki na wuce na gyara jikina sannan na fito

Zaune na taddasa a parlor kamar yanda na barsa ya lula duniyar tunani

“Please zan iya amfani da pc ɗinka?” Na tambaya

Ɗan ƙureni yayi da ido sannan yace “sure” ya ƙare da nuna min ɗakinsa

Ɗakin na wuce, kan bedside drawer ɗinsa na hangota, idona ne ya sauka cikin drawer da ta buɗe kaɗan, takadda na gani kamar drawing hakan ya sanya na janyo drawer na buɗe

Drawings ne nawa, wani ina dariya, wani smile, wani harara ga su nan dai birjik duk nawa, mamaki ne ya cikani ganin abinda ban taɓa tsammani ba a wajen mutumin da ban ko taɓa mafarkin hakan daga garesa ba, mene hakan?, me hakan yake nufi?, me ya sanya yake zana hotunana?, dukkan wanan tambayoyin na hau tambayar kaina sai dai bani da mai amsa min su

Murmushi na saki sannan nace “he is a good architect” na ƙare ina maida masa ina blushing tareda ɗaukar pc ɗin na fita

Parlor na koma sannan na shiga cite ɗinmu, na jima a kai sannan na saki ajiyar zuciya nace “Alhamdulillah!, ya Allah make this work”

“What?” Ya tambaya

Murmushi na saki kawai tareda miƙewa na nufi ɗaki

PRINCE YAR POV

Ihu ya kurma tareda jefar da wayar yana faɗin “bunch of idiots”

Princess Zairah a zabure ta tashi tana faɗin “what?”

“They failed!!!!” Ya faɗa yana buga bango

Hankali tashe Princess Zairah tace “amma sun ƙware, ta ya sukayi failing?” Ta faɗa hankali tashe

“Gobe za’a fara voting for throne, Sydeek yana da kuɗi, and he has the seal, ya zanyi idan na rasa komai!!!” Ya ƙare yana zubewa ƙasa

“We can’t loose, dole muyi wani abu, dole mu san abun yi!!” Ta faɗa cikin tashin hankali

“Gobe ina da appointment da wani wanda muke business da shi, idan na dawo zani sashen Prince Sydeek kafin nan make sure kun basa abu da zaiyi weakening ɗinsa ina, nikuma zan ji da shi” ya faɗa cikin ƙunar rai

Princess Zairah fita tayi zuwa sashen Madam, yayinda Prince Yar ya zauna ya na ta saƙa da warwara

PRINCE SYDEEK POV

Kwance yake kan gado yana latse latse a wayarsa

Ɗayar wayarsa ce da ke gefe ta ɗauki ƙara, a hankali ya ɗauka ya kara kunnensa yana faɗin “Ma”

Sun jima suna magana da big Madam kana ya kashe fuska babu walwala alamun zancen bai masa daɗi ba

Bayan ya ajiye wayar, bedside drawer ɗinsa ya buɗe yana janyo drawings ɗin Batool, wanda take smiling ya tsura ma ido yana faɗin “why do i feel secured and happy idan kina kusa da ni, you have done alot for me Batool, yau kin kusa karɓar min bullet, kina so na ne ko kuma kina aiki ne a matsayinki na maid ɗi ta?, i need to know, ba zan amshi tayin Big Madam ba na ɗaukar wata chan daban a matsayin mata alhalin kina sona, in har kina so na, kece zaɓina Batool nima” ya faɗa da smile a fuskarsa

Da wannan tunanin yana rungume da drawing ɗinta yayi bacci

Washegari ta kama ranar da za’a shiga meeting na senates dan fidda wanda zai gaji kujerar his majesty

Prince Sydeek tsaye yake jikin window yana kallon yanda bishiyu ke kaɗawa a harabar apartment ɗin nasa, doguwar ajiyar zuciya ya sauke sannan yace “ya Allah ka zaɓa min abinda yafi alkhairi”

Batool da ta fito itama tsaye a bayansa ta furta “Ameen ya rabb”

Juyowa yayi ya zuba mata ido, sosai tayi masa kyau fiyeda kowacce rana, sanye take cikin abaya fara tass tayi rolling coffee veil wanda ya dace da adon jikin rigarta, wani iri ya ji zuciyarsa nayi, kamar kwaɗayin ya sanyata cikin jikinsa ya ji ɗumin jikinta, ɗan basarwa yayi tareda kauda kansa gefe

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button