SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

“Ina kwana?” Ta faɗa muryarta cikeda nishaɗi

Bai tanka ba, bai kuma juyo ba

Murmushi ta ɗanyi mai sauti sannan tace “ga abinci chan na haɗa maka”

Kamar baya son magana yace “ina azumi”

Gyaɗa kai kawai tayi tareda juyawa

Prince Sydeek juyawa yayi shima ya bi ta da kallo har ta kwashe kayan ta maida kitchen, ajiyar zuciya ya sauke tareda cewa “ta ya zan tambayeta!!” Ya ƙare da furzar da iska

Batool ta ɗan jima a kitchen ɗin kafin ta fito ta nufesa, cikin muryarta mai kama da kiɗan taushi tace “yaushe zaku shiga meeting ɗin?”

“Nan da awa uku” ya bata amsa a taƙaice

“Yau kenan za’a gabatar da seal ɗin?” Ta tambaya

Sigh yayi sannan yace “yes and the worst part babu wanda ya san inda yake, Big Madam tace bata sani ba haka zalika bana tunanin Yar ya sani shima”

Shiru Batool tayi sannan tace “Allah ya kaimu”

PRINCE YAR POV

Tsaye yake cikin shirinsa fuskarsa ɗauke da fara’a, hannunsa riƙe da wani box madaidaici silver color

“Dan Allah dai kar ka daɗe, bana son ko kallon mara cika lokaci ayi maka” cewar Princess Zairah da ke gyara masa hiram ɗinsa

Murmushi yayi sannan yace “zan dawo da wuri, ina ba shi saƙon zan fito, please make sure kun kai masa” ya faɗa

Gyaɗa kai Princess Zairah tayi sannan tace “in ji Big Madam ma kuwa, ka ga dole ya ci, bayan haka ma zamu saka masa weakening gas” ta ƙare da smile

Murmushi ya saki tareda pecking ɗinta yace “sai na dawo my queen”

RAS AL-KHAIMA INTERNATIONAL AIRPORT (DUBAI)

Prince Yar hankali kwance yake tafiya da box ɗinsa, wajen wani lobby ya tsaya tareda ɗaukar wayarsa yayi dialling number, babu ɓata lokaci aka ɗauka, sun ɗanyi magana sannan ya kashe wayar

Mintina ƙalilan wani bature ya ƙaraso cikin ash suit, wata black bag ya bama Prince Yar shikuma ya miƙa masa box ɗin ya juya fuskarsa wasai cikeda fara’a

Yayi almost ten steps ya ji anyi tapping ɗinsa a shoulder, gabansa ne yayi mugun faɗuwa sakamakon ganin wanda ya bama cocaine ɗin an saka mishi cuff a hannu tareda american securities da suka zagayeshi

Sample ɗin poison ɗinsa da aka lalata da ya amsa a hannun baturen da ya taɓa saida mawa, ya kuma siya yayi paying da huge amount of cocaine ne ya faɗi tsabar rikicin da ya hango ya tsoma kansa a rana mafi muhimmanci a rayuwarsa

“Please come with us” cewar ɗaya daga cikin turawan officers ɗin ya ɗauko card ɗinsa ya nuna masa da ke ɗauke da tambarin CIA

Cikin sauri escorts ɗin da suka taho da Prince Yar suka nufosu cikin tashin hankali suna tambayar mene ne

“Mun kama shi ne matsayin criminal da yake trading illegal products cikin ƙasarmu” shugabansu ya faɗa

“Please calmly come with us” ya faɗa yana sauke idonsa kan Prince Yar tareda handcuffing ɗinsa

Hotuna ne ke tashi ko ta ina dan hankalin kowa sai ya dawo kansu cikin airport ɗin ana ta ma Prince Yar hotuna da video as wanda ake tunanin zai gaji shugabancin ƙasarsu ai dole abin ya zama na magana, tuni wasu mutanen suka fara zaginsa suna aibata shi dama mutum ba’a rasa shi da abin faɗe dan dama ƙiris yake jira

Within minutes arrest na Prince Yar ya baza kowani lungu da saƙo na media

BATOOL POV

Wayar Prince Sydeek ce tayi ƙara

Ɗan kallona yayi sannan yace “it’s your call”

Cikin rawar jiki na karɓa tareda karawa a kunnena nace “it’s Anitha speaking” chan ƙasan murya bayan na saci kallon Prince Sydeek ka da ya ji sunan da na faɗi

“Congratulations Anitha! You have successfully complete your mission, the Prince is arrested!!” Aka faɗa

Wani ihu na kurma cikin jindaɗi sannan nace “thank you!!!” Nayi hanging call ɗin

Prince Sydeek kafeni da ido yayi sannan yace “what?”

Murmushi na saki sai da na goge number CIA tareda blocking sannan na miƙa masa nace “Prince Yar is arrested!, ban faɗa maka ba ne amma jiya na ji shi yana waya da yazo nan yana son na buɗe masa, it was then i heard him talk about zai kai wasu kaya airport, ban nutsu ba sai nayi reporting ɗinsa using your pc, sannan na ari wayarka yau da asuba dan nayi musu tuni, so right now sun kama shi trying to send illegal products, probably poison!” Na faɗa happily

Murmushi ya saki sanan yace “weldone”

Kafin na amsa muka ji knock a ƙofa, nufar ƙofar nayi tareda buɗewa

Wata maid ɗin Big Madam ce tsaye hannunta da tray na kayan abinci, sai dai ina ganinta na tabbatar a tsorace take dan hannunta har shivering yake

Dubanta nayi na karanceta sosai na kuma gane batada gaskiya, “lafiya?”

“Um..um …dama Big Madam ce tace akawo ma Prince Sydeek sannan a tabbatar ya ci” ta faɗa

Amsa nayi sannan nace “come in” na ƙare ina matsa mata dan ta shigo

Plate na ɗauka nayi serving abincin sanan na….
[11/19, 6:57 PM] Muslima????: ???? S A R K I

       *75&76*

Plate na ɗauka nayi serving abincin sannan nace “amshi ki ci, Prince azumi yake, ni kuma a ƙoshe nake kuma kinga bai kamata a maida ma Big Madam haka ba” na faɗa ina kafeta da ido

A firgice ta kalleni tace”um…am…ni bana ci, au ya fi ƙarfina” duk ta daburce

Murmushi na saki nace “kar ki damu, ai shi ya baki”

Cikin sauri ta tsugunna ta ɓalle da kuka tana faɗin “dan Allah ku min rai, wallahi babu yadda zanyi ne nima” ta ƙare cikin shasheka

“Mene a ciki?” Na tambaya

“Wallahi bansani ba, amma dai na ga sun tsiyaya abu a cikin soup ɗin da alama ba mai kyau ba ne” ta ƙare cikin shasheka

“Su wa ne?” Na tambaya

Prince Sydeek ɗan yamutsa fuska yayi sannan ya dubeta yace “leave please”

Ina son masa magana shima ya nufi ƙofa yana faɗin “follow me”

Ban so ya dakatar da interrogation ɗina ba, dan haka na ɗaure fuska cikin mota ban kallesa ba

Muna isa sashen Big Madam na fara jin kururuwar Madam da Zairah cikin tashin hankali

Murmushi na saki nace “ƴan marasa imani”

Muna shiga Madam ta nufo Prince Sydeek cikin sauri ta cakume shi tana faɗin “an tafi da ɗan uwanka, save him, dan Allah yanzu guards ɗinsa suka faɗamin zasu bar ƙasar da shi ta ruwa, hurry please!!!!” Ta ƙare cikin matsanancin kuka

Princess Zairah ma tsugunnawa tayi tana faɗin “Sydeek dan Allah ka taimakesa, blackmailing ɗinsa akayi, wallahi sharri akayi masa” ta ƙare tana kama ƙafafunsa

Murmushi na saki ina faɗin basu san waye securities na US ba cikin zuciyata, na tabbata ko babansa ne ke shugabancin US ɗin ma kanta muddin suka kama sa babu wanda zai kuma ko jin labarinsa

“Kinga sai dai fa kuyi haƙuri, nayi ma abokan mahaifinsa magana sunce babu yanda suka iya, sai in har waɗanda suka kamasa ne suka ga ba shida laifi suka sakesa, in ba haka ba sai dai a haƙura da shi” cewar Big Madam

Maida dubanta tayi kan Prince Sydeek tace “get ready nan da minutes zamu shiga senates”

Wani ihu Madam ta kurma tana faɗin “wani irin rashin imani ne wannan?, ace an kama Prince Yar amma ku tunaninku a shiga a bama Prince Sydeek throne”

Big Madam ce ta watsa mata wani kallo sannan tace “kin ɗauki kujerar wasa ne, da za’a dakatar saboda shiriritar ɗanki da yayi chan daban” ta ƙare da tsaki

Kuka Madam ta saki tana faɗin “Allah ya isa wallahi, dama nasan a masarautar nan an tsaneni ni da yarana” ta ƙare tana ficewa da sumbatu, Princess Zairah ta rufa mata baya

Sigh Big Madam ta saki sannan ta dubesa tace “Sydeek na nemo maka auren ɗiyar minister, by next week insha Allah za’a fara gudanar da hidimar biki”

Jikina ne yayi mugun sanyin da bansan dalilinsa ba yayinda zuciyata ta rasa sukuni haka zalika gangar jikina ta rasa nutsuwa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button