SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

Prince Sydeek a sanyaye yace “na zaɓi mata da kaina”

Big Madam haɗe fuska tayi tace “ƴar gidan wace”

Idonsa ya maida kaina sannan yace “ga ta”

A zabure Big Madam ta miƙe tana faɗin “sam bazan taɓa amincewa ba, nasani Batool tayi namijin ƙoƙari akanka ta bada gudummawa ainun amma hakan ba zai sanya ka aureta ba, abinda tayi bai wuci mu biyata da kuɗi da zinare mai auki ba, dan haka ka daina wannan tunanin”

Kaina na sadda ƙasa ina jin wata ƙwalla na taruwa a idona

Prince Sydeek bai tanka ba, sai wayarsa da ya zaro ya fara latse latse, ya ɗauki mintina kafin ya ɗago ya kalli Big Madam yace “Batool ce zaɓina”

Rai ɓace ta miƙe daga kujera tace “kai meyasa bakada hankali ne, na me zaka auri wadda ba kowa ba, kuma ba ƴar kowa ba, baku dace da ita ba, ka daina wannan batun tun kafin zukata su ɓaci, lokaci yayi tashi ka je tun baka makara ba ina tafe” ta faɗa

Prince Sydeek bai tanka ba ya miƙe tareda ficewa

Big Madam dubana tayi tace “Batool ina ajiyar da na baki?”

Hannu na sanya na fiddo case ɗin tareda takaddar daga cikin jakata

Murmushi tayi tareda amsa ta ɗora kan wani soft pillow

“Batool!!” Ta kira sunana

A sanyaye kamar mara laka nace “na’am”

“Kinyi tunanin zama matar Sydeek ne naga jikin yayi sanyi dan nace a’a” ta faɗa cikin kulawa

Cikin sauri na girgiza kai tareda faɗin “ki gafarceni ban taɓa wannan tunani ba”

Murmushi ta ɗanyi mai sauti sannan ta sanya hannu ta janyo ni tace “zauna”

Zama nayi kan kujera idona na a ƙasa

“Batool! Prince Sydeek zagaye yake da maƙiya duk da ina tunanin yanzu za’a samu sauƙi domin an tafi da babban cikinsu wanda yake fuskantar ƙiyayyar jama’a da dama saboda shi, amma yana buƙatar ƙarfi wanda zai ƙara ma kujerarsa ƙarfin mulki kuma hakan ba zai samu ba sai in ya samu mata daga babban gida, dan haka zai fi kyau idan kika cire tunani ko nace mafarkin aurensa daga ranki, na yanke shawara idan ƙura ta lafa zan yi miki kyakyawar sallama, gara ki koma gida hakan zai fi mana kwanciyar hankali”

Murmushi na saki dan ko bata faɗa ba ai ni lokacin tafiyata yayi ko da son ranta ko babu, dubanta nayi nace “toh”

Murmushi ta saki tace “yawwa, Allah ya saka miki da alkhairi, ɗauki wannan” ta ƙare tana nuna min pillow ɗin tareda miƙewa

Gaba tayi na bi bayanta har muka shiga mota, ba mu zarce ko ina ba sai sashen da aka ware na mai mulkin wannan masarautar

Idona ne ya sauka akan Prince Sydeek da fuskarsa ta cika da annuri da kwarjini, haƙiƙa yau ya ƙaramin kyau ainun, kuma sai na ji inada burin cigaba da zama da shi har abada ko da a matsayin maid ɗin ta sa ce amma ina muna duniya biyu ne mabanbanta, dole na tafi na barsa batareda ya san wacece ni ba, batareda ya san ƙasata ba, batareda ya san komai dangane da ni ba, dole na tafi na barsa sai dai tabbas nasan zanyi kewarsa, hawaye ne suka zubomin

Big Madam ce tace “ke lafiyarki kuwa”

Sai a lokacin na dawo hayyacina

“Kai ma wancan takaddar” ta nuna min wanda nake tunanin shine magatakarda

Jiki babu ƙwari na miƙa masa

Gyaran murya yayi tareda fara karanto takardar kamar haka IDAN HAR KUN KARANTA TAKADDAR NAN NA SAN NA KWANA BIYU CIKIN ƘASA, NI SARKI ABDULRAHMAN MUHAMMAD INA JIN WANAN ƘASAR TAWA HAR CIKIN RAINA DAN HAKA NA ZAƁI SYDEEK A MATSAYIN MAGAJINA DOMIN SHINE WANDA ZAI IYA RIƘETA DA DUKKAN ƘOƘARINSA BATAREDA ƘUDURIN CUTAR WANI BA, BATAREDA AN SAMU TANGARƊA BA KO LALACEWA. SYDEEK SHINE ZAƁINA A MATSAYIN S A R K I INA KUMA FATA KU AMSHESA KU NUSAR DA SHI INDA YAYI BA DAIDAI BA DOMIN INA DA YAƘININ ZAI ZAME MUKU ABIN ALFAHARI, FATAN ALKHAIRI

Bayan ya gama karanta wannan takadda hawaye ne ke ta gudana daga idanuwan masu sauraro, cikin ƙanƙanin lokaci kowa yayi na’am da wannan zaɓi suka yanke sati mai zuwa za’a yi naɗi haɗi da ɗaurin aurensa

PRINCE YAR POV

Hawaye yake kuma ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba ganin suna ta lulawa cikin ruwa da mugun gudu kuma babu wanda ya biyo bayansu

Cikin hawaye ya dubi wani da ke tsaye kansa yace “ina zaku kaini?”

Murmushi yayi yace “inda ba’a dawowa, wajenda ba zaka kuma haɗuwa da wani ba har ƙarshen rayuwarka”

Cikin kaɗuwa yace “dan Allah na roƙeka ka taimakeni zan baka arziƙi da dukkan abinda na mallaka, ka kuɓutar dani” ya faɗa cikin tashin hankali

Hannu ya sanya ya zabga masa mari sannan yace “kai wani irin daƙiƙi ne, kanada ƙwalwar ƙirƙirar poison mai mugun haɗari amma bakada ƙwalwar fahimta, wa ya faɗa maka zan fifita kuɗi akan ƙasata, ka cutar da ƙasata kaine silar rasa manyan mutane da ƙasata tayi dalilin tsinannen poison ɗinka, toh ƙasata ta fiye mini komai harta da rayuwata, dan haka ka daina tunanin kuɓuta, you will rot in prison” ya ƙare yana tofa masa yawu……
[11/20, 12:37 PM] Muslima????: ???? S A R K I

77&78

Jikina a sanyaye muka koma apartment ɗinsa bayan sun tashi meeting ɗin

Ina ƙoƙarin shigewa ɗaki naji yace “Batool!”

Tsayawa nayi batareda na juyo ba dan ji nake zan iya fashewa da kuka

“Zauna muyi magana” ya faɗa a taƙaice

Komawa nayi na zauna kamar yanda ya umarta sai dai kaina na a ƙasa ban iya ɗagowa na kallesa ba

Shiru ne ya biyo baya kafin ya nisa yace “Batool zaki aureni?” Ya faɗa yana stammering

Ɗago kai nayi na kallesa sai ya kauda kansa gefe

Murmushi na ɗanyi sannan nace “kayi haƙuri ni ba tsarar aurenka ba ce, ni maid ɗinka ce ta ya zan aureka, kafi ƙarfina dan Allah ka bar wannan batun” na faɗa ina miƙewa haɗe da shigewa ɗaki

Zubewa nayi kan gado tareda sakin kukan da ban san na mene ba, a haka har bacci yayi gaba da ni

Misalin huɗu na shirya na nufi sashenmu, zaune na tadda Salamat da Junnut kan gado ɗaya suna haɗa kayan Salamat cikin jaka

“Sannunku” na faɗa ina dubansu

Da murmushi Junnut tace “wato kun samu sarauta ganinku sai an yanki ticket” ta ƙare da dariyar wasa

Nima dariyar na saki sannan nace “wane ni, gyaran kaya kukeyi ne?”

Hawaye ne suka gangaro kan fuskar Salamat, sharewa tayi sannan ta ƙaƙalo murmushi tace “Batool tafiya zanyi”

Cikin mamaki nace “meyasa, ba kya son a zubda cikin ne?”

Murmushi tayi tace “an zubar ai, idan har ban tafi ba na tabbata sai mun kuma haɗewa da Yameen, kuma yanzu ya tsaneni cewa yake ni na shafa masa hiv” ta ƙare da sakin kuka

Cikin tashin hankali nace “Hiv ce da ke Salamat?”

Share hawayenta tayi sannan ta girgiza kai tace “bani da ita, da muka je zubda cikin an gwada ni, ina tunanin wata sabuwar maid da ya samu ce ta shafa masa shine yake ɗoramin laifi dan bai san banida ita ba, kinga gara na gudu tun wuri” ta faɗa a sanyaye

Gyaɗa kai nayi sannan na miƙe na buɗe kayana da suka rage a nan na zaro bangles na zinare da Big Madam ta bani na miƙa mata nace “ga wannan kinyi amfani da shi, Allah ya ƙara haɗamu a darussalam ina miki fatan alkhairi a rayuwa”

Miƙewa tayi ta rungumeni tana faɗin “Batool ki yafe min dan Allah, na so cutar da ke, na zalunceki dan Allah ki yafemin” ta faɗa cikin kuka

Hawaye naji nima na ƙoƙarin sakkomin dan tabbas lamarin Salamat ya bani tausayi, tau ina amfanin wannan rayuwa ta ba wa ƙato budurcinta, ta maishe shi tamkar mijinta gashi a ƙarshe ya sakata cikin shara harda ƙazafi

Junnut itama ta so wa tayi gamida rungumemu hawaye na zubar mata, mun ɗauki lokaci mai tsayi kafin muka rabu

Ni da Junnut mukayi mata rakiya har wajen motar da ake zuwa cefane inda nan zata hau ta fiddata daga masarautar

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button