SARKI HAUSA NOVEL

Bayan mun rakata ɗaki muka dawo munata jajanta batun Salamat
Junnut dubana tayi tace “ya kamata ki dawo ɗaki, kinga yanzu ni kaɗai ce na rage” tana saka pity face
Murmushi nayi sannan nace “Junnut kwanakin da basu wuce na mako ba ne kawai suka rage min a masarautar nan nima, amma zan dawo yau har ranar da zan tafi” na faɗa ina murmushi
“Kamarya Batool, meyasa zaki tafi?” Ta faɗa cikin rashin sukuni
Ban bata amsa ba kawai nayi murmushi nace “bari na kwaso kayana na dawo” na miƙe ina ficewa
A hanyar zuwa na ga Prince Yameen ya fito a bige yana bin maids da gudu suna tsere masa suna dariya, shima dariyar yake yana faɗin “dan kunga inada Hiv, toh ni ba zan daina ba, ba zan daina ba” ya faɗa yana tangal tangal yana binsu su kuma suna darewa
Duk da a bige yake na tabbata ya samu matsala ko yana cikin depression, girgiza kai nayi ina ƙoƙarin wucewa
Da gudu ya nufoni yana faɗin “ke. ..ke. ..ke ce ƴar dabar da kike guduna ko..ko…toh yau zan ga ƙar…..ƙarshen iskancinki yarinya. …a nan zamuyi da ke. ….gaban bishiya da mutane” ya ƙare da dariya yana ƙoƙarin yaga min riga
A fusace na hankaɗasa tareda kifa masa mari sannan na bi takan yatsun hannunsa na murje nayi gaba
Idona ne ya sauka akan Prince Sydeek da ke murmushi yana kallona, kaina na sadda ƙasa sannan na ƙarasa tareda raɓewa ta gefensa na shige ciki ban tankasa ba
Kayana na haɗo, ina fitowa parlor na ganshi tsaye ya harɗe hannayensa a ƙirji
Kaina a ƙasa nace “akwai abinda kake buƙata?”
Shiru yayi tareda tsura min ido sannan yace “ina zaki?”
“Zan koma sashenmu ne” na bashi amsa
“Ban amince ba” ya faɗa yana juya baya
“Wanda muke tsoron ya rigada ya tafi, meyasa zanyi ta zama a nan, dan Allah ka barni” na faɗa
Bai tankani ba ya wuce ɗakinsa, nima na wuce sashenmu
SYDEEK POV
Zaune yake kan gado yana tunanin Batool, sosai yake jinta tsaye cikin zuciyarsa, damuwarsa da tunaninsa duk sun tattara akan ta ina zai fara furta mata kalmar yana sonta, yana son yayi rayuwa da ita, duk da ya tambayeta ko zata aureshi ta shashantar da zancen bai cire ran zasuyi rayuwa ba
Lumshe idonsa yayi yace “ta ya za’ayi ki zama tawa ne?” Ya faɗa yana dafe kansa
PRINCESS ZAIRAH POV
Tsaye take kan Madam da ke ta rawar sanyi, ɗan yatsina fuska tayi sannan tace “wai babu yanda za’ayi a fiddo Yar ne?”
Madam hawaye suka gangaro mata sannan tace “babu Zairah, sun ƙi taimaka mana”
Zama tayi daɓas tareda fashewa da kuka tana faɗin “ya zanyi yanzu, duka burina ya rushe, Allah ya isa tsakanina da duk wanda da saka hannunsa a kama mijina”
Haka ta fice tana kuka wiwi kamar jiniyar mota
FIVE DAYS LATER
BATOOL POV
Yau kwana biyar kenan ban sanya Prince Sydeek a ido ba, ba dan komai ba sai dan son yakicesa da nake sonyi daga raina, shiyasa tunda ya koma sashen sarki ban kuma sanya shi a ido ba nayi nesa da shi, duk da ya turo a zo ɗaukata har sau uku ina zillewa
Zaune nake ina linkin kayana naji knock, tashi nayi na buɗe
Matashiyar budurwa ce da murmushi a fuskarta tace “Big Madam na nemanki yanzu”
Veil kawai na yafa sannan na bi bayanta
A babban parlor ɗinta na taddasu ana ta shirye shiryen kaya wanda nakeda tabbacin na aure ne
Da murmushi a fuskarta tace “Batool dama ina son zaɓa ubangidanki kaya ne, tau ban san wacce kala zaifi son sanyawa ba ranar ɗaurin aurensa da naɗin sarauta” ta ƙare tana yaye min mayafin da aka rufe kaya masu yawa na sa
Murmushi nayi sannan na zaro farare da akayi musu adon silver nace “wannan zai so ta”
“Yawwa, dan Allah ki taimaka masa da shiri mai kyau, ina son yayi kyau sosai” ta ƙare da fara’a
Murmushi nima na saki kana na ɗaga mata kai
Da ni akayi ta shirye shiryen har muka kusa kammalawa
Big Madam ce ta dubeni tace “Batool kinga ke tashi kije sashensa dukkan abinda kika ga bai dace ba ko ya kamata a canza sai ki sanarmin dan kar mu makara ko” ta faɗa
Gyaɗa kai nayi sannan na miƙe muka fita ni da wasu maids ɗin
Sosai naga sashen ya ƙara haske da alamu ma an canza furnitures dan ba irin wanda na tarar ba ne lokacin da late sarkin ke nan ba
A hankali na fara tafiya ina duba abubuwan sai dai banga na canzawa ba, idona ne ya sauka kan wani ɗaki da ke ɗauke da manyan frames na nature, tura kai nayi ciki ina faɗin “wow!!!” Dan sosai drawings ɗin sun tafi dani
“Sunyi kyau?” Naji sautin muryarsa
Da sauri na ɗaga kaina na kallesa sai kuma na sauke kaina ƙasa tareda juyawa
“Batool!!” Ya kira sunana
Tsayawa nayi cakk ina jin yanda zuciyata ta fara bugawa da ƙarfin gaske
A hankali ya tako har inda nake tareda ɗora hannayensa ya zagaye cikina ya ɗora kansa kan kafaɗata
Zuciyata ce ta fara bugawa da mugun gudun da ban taɓa jin irinsa ba, yayinda duk wata gaɓa ta jikina tayi sanyi
“I am hungry!, na daɗe ban ci abinci ba, tun ranar da kika gudu” ya faɗa slowly
Tattaro ɗan ƙarfin da yayi min ragowa nayi na cire hannunsa tareda cewa “bari na dafa maka” nayi gaba
Biyoni yayi har kitchen ɗin duk da tarin maids da ke ciki bai bi takansu ba
Cikin kunya na dubi maids ɗin nace “excuse us”, nan suka wuce dukkaninsu
A sanyaye nace “mai zan dafa maka?”
Bai ansani ba sai kallona da ya cigaba da yi
Wucewa nayi na fara ƙoƙarin haɗa masa pasta salad
“Batool!!!” Ya kirani
Dakatawa nayi batareda na juyo ba
“Ke nakeson na aura, ya zanyi?” Ya faɗa cikin damuwa
Ɗan ɗago kai nayi na kallesa sannan na juya na cigaba da aikina
Takowa yayi kusadani ya kuma ɗaura kansa kan kafaɗata yace “Batool Big Madam zata ji haushi in banyi auren nan ba, kin amince na aureki daga baya, one week after wannan wedding ɗin?” Ya faɗa
Hawaye ne suka gangaromin domin sai nake ji kamar bazan iya rayuwa batareda shi ba, amma kuma tafiya ta zame min dole domin bana jin zan iya ma rayuwar gidan sarauta, i’m not used to it, abin akwai takura musamman sarauta irin ta su ma larabawa, ni baturiya ce ina son freedom, ba zan so in yi rayuwa babu walwala ba sai na dinga bin wasu customs da traditions
Juyo dani yayi idanunsa na bayyanar da tsoro yace “please!!!!”
“Prince. ……..
[11/20, 3:52 PM] Muslima????: 79&80
“Prince please…” ban kai ga ƙarasawa ba ya ɗora hannunsa saman lips ɗina yace “Batool ni ba zan amshi rejection ba”
Shiru nayi batareda na kuma cewa komai ba
Haka na ƙarasa abincin yana tsaye yana kallona
Bayan na gama parlor muka koma wanda yake private parlor ɗinsa ne, kan centre table na ajiye masa ina shirin fita yace “Batool kina bani hard time”
“I’m sorry” na furta calmly
“Let’s meet here tonight, zaki iya yi min kwalliya?” Ya tambaya his eyes on me
Wani iri naji jikina ya ɗauka, kaina a ƙasa nace “toh”
Bai kuma cewa komai ba ya fara cin abincinsa nima na fita nayi tafiyata
MADAM POV
Tana zaune a ɗaki ta zabga tagumi Prince Yameen ya shigo idanunsa sun kaɗa sunyi jajawur
“Lafiya na ganka haka?” Cewar Madam
Zama yayi kan cushion tareda jingina kansa jikinta hawaye suka ɗigo masa
“Wai lafiyarka kuwa, ko kewar ɗan uwan naka ne?” Ta tambaya hankalinta a ɗan tashe
Kuka ne ya kufce masa ya kifa kansa kan cinyarta sai da yayi mai isarsa sannan ya ɗago yace “inada HIV”
Cikin tashin hankali tace “me kace?”
“Ina da HIV” ya kuma maimaitawa cikin kuka
Hannu ta sanya ta hankaɗesa tace “gashi nan ai garin iskanci ka kwasowa kanka jaraba, Yameen meye amfanin bin ƴan aiki da ka dingayi, yanzu wace riba ka samu, ka cuceni, yanzu ai dole na jingineka a gefe na zuba maka ido dan babu wanda zaiyi na’am da kai ko da ka tuba ka daina bin mata” ta faɗa hawaye masu ɗumi na zubar mata