SARKI HAUSA NOVEL

“Ya zanyi?!!!” Cewar Prince Yameen da ƙwalla ke kwaranyo masa
“Fita!!!!” Ta daka masa tsawa
Hawaye ne ya gangaro masa sannan ya miƙe ya fice zuciyarsa na jin mugun zafi
Madam fashewa tayi da kuka tana faɗin “i lost it all!!!”
A fusace kuma ta miƙe ta buɗe wardrobe ɗinta tareda ɗauko wata bottle take ta kafa kai ta shanye
Cikin mintinan da basu haura goma ba ta fara tari wanda yake tahowa da gudan jini, ihu ta saki wanda ya sanya maids ɗinta suka rugo a guje
Ganin jini mai yawa guda guda na kwaranyo mata ya sanya suka fita a guje dan kiran palace doctor, sai dai ko kafin su dawo tuni ta daina motsi
Cikin gaggawa doctor ya nufeta tareda dubata nan ya duba pulse ɗinta, ganin bata mutu ba ya sanya ya fara bata taimakon gaggawa daga bisani aka wuce da ita hospital
Prince Yameen babu abinda yake a mota sai kuka ganin halin da mahaifiyarsa ke ciki
Haka suka ƙarasa asibiti da ita aka shiga emergency room da ita
BATOOL POV
Ina zaune kan gado da Junnut muna jajanta labarin Madam da ya karaɗe palace akayi mana knocking
Nice na miƙe na buɗe ƙofar
Wata maid ce hannunta riƙe da babban kwali tace “Kece Batool Bassam right?”
Gyaɗa kai nayi nace “sure”
Kwalin ta miƙo min tace “inji his majesty” sannan ta juya tayi tafiyarta
Ɗaki na dawo tareda miƙa ma Junnut box ɗin
Cikin jindaɗi ta fiddo wata white with creamy flower touches gown sai net na rolling, jewelleries da white shoe, “wow, Batool wannan duk na mene?” Ta faɗa cikin shauƙi
Sighhh na yi sannan nace “Prince Sydeek ya gayyaceni dinner, and i don’t feel like going” na faɗa
“Meyasa?” Ta tambaya cikin mamaki
“Bana son issues ne Junnut, i just want to live this palace peacefully” na faɗa a sanyaye
Gyara zama tayi tareda matsowa tace “ke faɗamin yana sonki ne?”
Murmushi nayi sannan nace “yes amma ba zai yi changing komai ba”
“Batool kina hauka ne?, ya zaki bar wannan opportunity ɗin ta zille miki, from all indication kema yana cikin zuciyarki so why will you hurt each other?, accept his love, in yaso sai ya aureki daga baya after aurensa ɗin nan da za’ayi” ta faɗa
Shiru nayi ina juya maganganunta kafin na dubeta nace ” you think it can work?”
“Meyasa ba zaiyi working ba in kuna son junanku?” Itama ta jefo min tambayar
Murmushi na saki tareda hugging ɗinta tightly
Bayan nan hira muka ɗan taɓa tana ta zuzuta irin kyan da zanyi anjima, duk da nace bazanyi kwalliya ba dan dole Junnut tace sai nayi ta
Misalin takwas bayan munyi sallar isha’i Junnut ta fara yi min kwalliya, sosai ta ke kwalliya with all her heart and might, ni da ba son hard make up nake ba duk ji na nake a takure, ta ɗau lokaci kafin tace “it’s all done!!!!” Cikin jindaɗi
Bata barni na kalla mirror ba sai da na sanya gown ɗin tayi min rolling sannan cikin dariya tace “take a look my queen!”
Dariya na saki wanda ya bayyanar da dimples ɗina sannan na ɗan bigeta kaɗan
Kallon kaina nake jikin mirror inata sakin murmushi coz ni kaina nasan ba ƙaramin kyau nayi ba and the best part of it i am ready to accept Prince Sydeek heart, a yanzu na amince zan iya fighting akan soyayyarmu, i won’t sacrifice my love over something minor
Ina tsaye aka buɗe ƙofa, wata maid ce ta shigo tana faɗin “Mss Batool kin shirya?”
Murmushi nayi sannan nace “all ready”
Waving nayi ma Junnut sannan muka fice, wata farar mota ce mai kyan gaske tazo ɗaukata
Bayan mun isa wata maid ce ta min jagora har bakin wani gate ƙarami da ke bayan building ɗin
Cikeda shauƙi da jindaɗin yanayin nake tafiya bakina ɗauke da murmushi
Table ne an haɗa shi da abubuwan ci da bottles na drink ga candles, wajen dai was so romantic
Prince Sydeek na can bakin pool yana amsa waya ya juya min baya, murmushi na saki ina yaba surarsa mai kyau da ɗaukar hankali
Ina tsaye har ya juyo, murmushi ya saki ganina sannan ya fara nufoni fuskarsa ɗauke da mabayyanin farinciki
Ɗan ƙuramin ido yayi da ya ƙaraso kafin ya ja kujera yace “have a sit”
Zama nayi ina wasa da yatsuna kaina a ƙasa
“Batool!!” Ya kira softly
Ɗan ɗago ido nayi na kallesa nan idanunmu suka sarƙe cikin na juna
“Kinyi kyau sosai” ya furta
Murmushi nayi sannan nace “thank you”
“Batool!” Ya kuma kira
Ban amsa ba kuma ban ɗago na dubesa ba
“Thank you for saving my life, kin taimakeni sama da kowa a duniya, you have walk through thorns and fire saboda ni, today ina son na roƙe ki ki bani dama na zama wanda zai zame miki katanga, garkuwa har ƙarshen rayuwarki, please accept me!!” Ya faɗa ina kallon cikin idanuna
Wasu ƙwallar farinciki ce ta tsiyayomin batareda nace komai ba
“Will you grow old with me?” Ya faɗa yana buɗe red heart shaped box tareda ciro wani diamond ring ya matso da shi kusada ni
Babu abinda nake sai hawaye dan ban taɓa tsammanin finding true love ne ya kawoni wanan masarautar ba da na sha baƙar wahala
“Please marry me!” Ya kuma faɗa
Hannuna na miƙa masa ina cewa “i will!!!”
Murmushi ya saki tareda saka min ring ɗin sannan ya miƙo min hankey ɗinsa
Amsa nayi na goge hawayena
Da hannunsa yayi feeding ɗina cake and champaigne sannan ya barni bayan na ƙoshi batareda ya ci komai ba
Mun ɗauki lokaci mai tsayi muna hira da shi cikin wasa da dariya, dan sai a yau na fuskance shi he is a simple and jovial man
Ya sani dariya sosai harda ƙwalla kafin yace “it’s getting late, muje na maida ki ko a nan zaki kwana?”
Cikin sauri na girgiza kai nace “a’a”
Murmushi ya saki yace “wai ke dodo na zama ne?”
Murmushi na saki nace “a’a muje dai ka kaini”
Da kansa yayi driving ɗina muna ta hira har muka isa
Bayan mun ƙarasa nace “thank you”
Bai tanka ba sai buɗe ƙofar da yayi ya fito shima, har ƙofa ya rakani sannan yace “get in”
Waving nayi masa sannan na shige ciki zuciyata cikeda farinciki
Ina shiga Junnut ta miƙe daga gadonta tana faɗin “ya kuka yi?”
Hannuna na nuna mata cikin jindaɗi
Ihu ta kurma sai da na toshe mata baki ina faɗin “ke dare fa yayi”
Tsalle tayi tayi dan farincikin da tayi ma zan ce har yafi nawa dan sai na zama ƴar kallo
Murmushi na saki nace “ke nutsu mana”
Dariya ta saki tareda hugging ɗina tana cewa “Congratulations Habeebty”
Mun ɗauki lokaci muna magana kafin muka kwanta
Ranar haka na kwanta cikeda mafarkin Sydeek
PRINCE SYDEEK POV
Zaune yake kan gado yana tunanin yanda zai fara auren wata yarinya ma ba Batool ba, bayan dukkan wahalar da yarinyar ta sha akansa, she risked her life just for him kuma ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba
Girgiza kai yayi yace “she deserve to be my queen”
Murmushi ya saki ganin ita ta zama queen ɗin ba ma damunta yayi ba, she was happy still after yace second wife zaiyi da ita
Da tunaninta ya kwanta, dariyarta na ta dawo masa, murmushinta da duk wani moment na su na ɗazu, da ƙyar bacci yayi gaba da shi. ……
S A R K I IS NOT FOR FREE ITS 300 NAIRA VIA 1401611541 FATIMA LAWAL SAID. ACCESS BANK OR MTN CARD TO 08167888934 THEN SHOW EVIDENCE OF PAYMENT TO 08167888934
[11/21, 3:57 PM] Muslima????: 81&82
Washegari da sassafe na tashi zuciyata fal farinciki da nishaɗi
Bayan na fito wanka na ci abinci ina zaune kan gado aka aiko Big Madam na kirana
Ban wani ɓata lokaci ba na shirya na wuce sashenta, zaune na ganta kan kujera ta ɗaure fuska ainun dan ban taɓa ganin ɓacin rai a fuskarta kamar ranar yau ba
A hankali na samu waje na zauna sannan nace “barka da safiya”