SARKI HAUSA NOVEL

“Koma mene, Batool is gone, let’s face the future” ta faɗa
Murmushin takaici ya saki sannan yace “zan nemota and auran da za’ayi gobe cancel it, babu wadda zan aura sai ita” ya faɗa
“Bazan taɓa approving ɗin Batool ta zama queen ba!!” Ta faɗa ranta ɓace
“Then ki zama sarkin masarautar nan ko kuma ki ɗaura Yameen, i’m leaving!!!!” Ya faɗa a fusace yana juyawa
“Sydeek!!!” Cewar Big Madam a tsorace
“Selfish woman!” Ya faɗa yana ficewa a fusace
Ɗaki ya koma zuciyarsa na ta azalzalarsa, tunaninsa ina take ina ta shiga, ta ya zai fara nemanta
Ƙwalla ce ta cika masa ido yana faɗin “i’m sorry” tareda maida ƙwallar
ID card ɗinta ya duba, da mamaki yace “Anitha Aldama?”, duk da ya ga launin ƙwayar idonta ya canza sai ya bari a zuwan hoto ne ya sauya
Amma mamaki ya shigayi na yanda akai sunanta ya canza daga Batool zuwa Anitha yakeyi, sighing yayi tunawa da yayi cewar ita ɗin ƴar bincike ce, wato harda sunanta ta canza kuma harda shi a waɗanda ta rufe
Murmushi yayi tareda furta “Anitha!!”, cije lips ɗinsa kuma yayi sannan yace “i will find you Anitha, i promise”
PRINCE YAR POV
Tafiya yakeyi cikin wani dogon kogo, da securities a bayansa, sai da sukayi tafiya mai mugun nisa sannan suka bi stairs wanda yayi leading ɗinsu wani underground prison
Mutane ne daban daban amma tsilli kowanne wajensa daban, wani wajen aka buɗe tareda hankaɗasa da ƙarfin tsiya har sai da bugu da bango sanan security ɗaya yace “rot in here!!”
Haka suka fice tuni wajen ya ɗauki mugun duhu domin underground ne ga shi babu fitila, kuka Prince Yar ya saki yana faɗin “what have i done to myself!!!” Ya ƙare cikin karaji
Maƙocinsa ya sheƙe da dariya sannan yace “cry hard man, coz nan shine grave ɗinmu, we are never ever going out!!” …..
[11/21, 7:45 PM] Muslima????: 83&84
PRINCE SYDEEK POV
Washegari da sassafe ya tashi, duk da baiyi baccin arziƙi ba daren, da tunanin Batool ya kwana wanda ya hana mishi saƙat cikin ransa
Bayan yayi wanka, shiryawa yayi cikin fararen kayansa da suka sha adon silver design, mint tea wanda Batool ta sabar mishi ya zauna yana sha duk da bai jin daɗinsa kamar nata
Yana nan zaune Big Madam ta shigo bakinta ɗauke da sallama
“Wa’alaikhi salam” kawai ya furta sannan ya kauda kansa daga dubanta
Zama tayi kan kujera sannan tace “Sydeek ka fahimceni mana, dukkan abinda ka ga ina yi saboda kai ne, ina son ƙarawa mulkinka ƙima ne, wata maid bata cancanceka ba, please ka daina fushin nan yau ranar ɗaurin aurenka, you suppose to be happy” ta ƙare cikin rarrashi
Murmushi ya saki sannan yace “kenan bakiyi cancelling wedding ɗin ba, let’s see waye zai aura wata yau” ya ƙare yana kurɓe cup ɗin
Cikin tashin hankali Big Madam ta miƙe tana faɗin “Sydeek please don’t do this”
Wani mugun kallo ya watsa mata sannan yace “bazan taɓa sadaukar da farinciki guda ɗaya da na taɓa samu ba saboda wani ƙudiri naki chan daban, yes as i said! Idan bazaki approving Batool ba yau zan bar masarautar nan forever, zaki iya zama a throne ɗin ko ki ɗaura Yameen” ya ƙare yana ɗage kafaɗa haɗe da shigewa ɗaki
Big Madam tsaye tayi tana mamakin rashin fahimta irinta Sydeek, ga yarinyar da in ya aureta zai ƙara ƙima, sarautarsa ta ƙara daraja amma yake liƙe ma ƴar aiki
Sydeek bai jima a cikin ɗakin ba ya fito hannunsa ɗauke da wayoyinsa, ta gaban Big Madam yazo wucewa
“Sydeek! Ina zaka yau fa bai kamata ka fita ba” cewar Big Madam
Wani mugun kallo ya watsa mata sannan ya wuce batareda ya tanka mata ba
A mota ya zaro ID card ɗin Batool tareda latsa number waya da ke jiki, zuciyarsa cikeda addu’ar Allah yasa a cira wayar
Bugu biyu aka ɗauka sai dai muryar baturen namiji yaji
“Hello who is talking?” Aka tambaya
Nisawa Prince Sydeek yayi sannan yace “Anitha Aldama lost her ID card, ina son kaimata ne!” Ya faɗa yana addu’ar Allah yasa ya samu address ɗinta
“Okay, she’s my princess, bari na kirata yanzu tayi min sending address nata sai na turo maka, thank you so much!” Ya faɗa tareda hanging
Five minutes later sai ga address na emirate palace hotel haɗe da room number inta da new phone number an turo masa, murmushi ya saki sannan yace “i’m coming for you!”
Tafiyar mintina ce ta kaishi hotel ɗin, knocking yayi bayan ya ƙarasa ƙofar zuciyarsa na harbawa da gudu dan tsoron ya ga wata fuska ba wadda yake nema ba
Minti biyu ta buɗe ƙofar bakinta ɗauke da smile tana faɗin “who is the..” kasa ƙarasawa tayi sakamakon fuskar wanda bata taɓa tunani ba
Prince Sydeek da ke binta da kallo cikeda mamakin canzawarta coz she is no longer the arabian girl he know who always wear abaya, wannan sanye take cikin jeans and t shirt ta bazo gashinta irin na turawa without hair tie, sannan eye balls ɗinta are so different
Anitha ganin sun tsaya na mintina tayi gyaran murya sannan tace “how do you find me?”
“Zan iya shigowa?” Ya tambaya
“Uhm…. come in” ta faɗa tana bashi hanya
Bayan ya zauna kafeta yayi da ido
Ɗan turo baki tayi tace “what?”
“Kin canza sosai especially there” ya faɗa yana pointing eye balls ɗinta
“Well….this is the real me, i’m Anitha not Batool, sorry!” Ta faɗa tana ɗage gira ɗaya
Murmushi yayi sannan yace “meyasa kika tafi batareda kin faɗa min ba?”
“For the best” ta faɗa slowly tana rolling eye balls ɗinta
ID card ɗinta ya zaro haɗe da ajiye mata sannan yace “we are destined to be together, don’t ever run away again”
Ɗago idanunta tayi tareda sauke light blue lens ɗinta cikin nasa sannan tace “i’m sorry, we can’t be together”
Prince Sydeek miƙewa yayi tareda dawowa inda take ya kama hannunta yace “why, bakya sona ne?”
Shiru Anitha tayi tareda sadda kanta ƙasa
“I’m talking!” Cewar Sydeek yana kuma matsa hannunta
“Well i..i. ..i do love you, but your grandma doesn’t approve me” ta faɗa coldly
“I love you Anitha, i’m ready to sacrifice my throne for you, we can live together somewhere else” ya faɗa yana matsa hannunta
Hawaye ne suka ɗigo mata sannan tace “your father was counting on you”
“But i can’t let you go!” Ya faɗa so worried
“Okay!, i will wait for you, Sydeek kayi ƙoƙari kayi winning grandma ɗinka tayi approving ɗina, only then i can marry you” ta faɗa tana maida ƙwallar da ke ƙoƙarin zubo mata
Sighhh Sydeek yayi tareda cewa “alright i will”
Murmushi tayi sannan tace “idan ta amince sai kazo gidanmu ayi aure”
Kallonta yayi sannan yayi knodding
“What can i serve you?” Ta faɗa
“I’m hungry!” Ya faɗa slowly
Tashi tayi tai ordering kayan sandwich, bayan ankawo ta haɗa da kanta tareda haɗa masa mint tea ta bashi
Sun ɗauki lokaci suna hira sannan ya dubeta ido cikin ido yace “Batool kar ki ƙara guduwa please!”
Murmushi tayi sannan tace “it’s Anitha, bazan gudu ba”
“Thank you” ya faɗa
“Yau ɗaurin aurenka, da naɗin sarautarka, you have to go!” Ta faɗa slowly
“No, ke kaɗai zan aura, that’s a promise” ya faɗa yana matsa hannunta
“Still ya kamata ka tafi!” Ta faɗa blushing
Murmushi yayi sannan yace “okay zan dawo anjima” ya ƙare yana miƙewa tareda ficewa
Cikeda nishaɗi ya koma palace ɗin, ko da ya isa bai tadda jama’a kamar yanda yayi zato ba, dan yayi tsammani jama’ar ɗaurin aure zasu cika wajen dayawa
Ɓangarensa ya shiga, zaune ya tadda Big Madam
Cikin sauri ta miƙe tareda sakin ajiyar zuciya tace “na ɗauka bazaka dawo ba”