SARKI HAUSA NOVEL

Babu abinda ke tashi a ɗakin sai kukan Princess Zairah da shashekar Yameen
Babu ɓata lokaci aka haɗa musu gawar Madam aka kaita masarauta dan a sallaceta
SYDEEK POV
Zaune yake kan gado yana danne danne a system, wayarsa ce tayi ƙara, sai da ta kusa tsinkewa sannan ya cira
Prince Yameen kuka ya saki yana faɗin “Ammina ta mutu Ya Sydeek!”
Jikin Sydeek ne yayi mugun sanyi, kwantarwa da ɗan uwansa hankali ya shigayi kafin ya kashe wayar ya sanya akayi shelar mutuwar Madam
An ɗan ɗauki lokaci kafin aka tara mutanen da suka raka gawarta, Sydeek duk da ya so ya yaƙi zuciyarsa yaje kasawa yayi tunawa da ya dingayi itace silar rasa mahaifansa mafi soyuwa a garesa
Misalin biyar na yamma akayi naɗin sarautarsa sai dai ba’ayi wani babban shagali ba saboda mutuwar Madam dan ko babu komai she was once a queen
Bayan ya sallami mutane da ƴan jaridu ɗaki ya koma tareda tunanin kiran Anitha, fasawa yayi ya barshi a zuwan yaje anjima
Misalin takwas na dare ya shirya tsaf cikin ado da ƙamshi sannan ya kama hanyar zuwa hotel ɗin
ANITHA POV
Zaune nake kan gado cikin pyjamas ina buga game a wayata
Knocking da na jiyo ne ya sanya na miƙe na nufi ƙofar tareda buɗewa
Prince Sydeek ne ya shigo, cikin sauri na juya cikin ɗaki tareda ɗora after dress sannan na dawo
Sosai yayi kyau gwanin ban sha’awa, murmushi na saki sannan nace “barka da dare”
“Lafiya!” Ya amsa batareda ya dubeni ba fuskarsa babu walwala
Shiru na ɗanyi sannan nace “lafiya kuwa?”
Kansa ya ɗago tareda watsa min mugun kallo sannan yace “ke bakida hankali zaki dinga buɗe ƙofa da kayan bacci, inda wani ƙaton ne bani ba fa?, haka zai kallar min ke?” Ya ƙare ransa a ɓace
Kaina a ƙasa nace “yi haƙuri”
“Ki tashi ki haɗa kayanki wajen nan zaki bari, bazan iya jurewa matata tana zama a hotel ba” ya faɗa muryarsa cikeda ɓacin rai
Ɗan satar kallonsa nayi ganin yanda ya ɓata fuska ya sanya dole na miƙe na shiga haɗa kayana ina yaba baƙar takurar da zan sha in munyi aure
Kayana na haɗa sanan na ɗauko jakar ina tunanin inda zai kaini
Shi ya karɓi jakar sannan muka nufi motarsa, gidan gaba na zauna kasancewar shi ke tuƙin
A sanyaye nace “Congratulations!”
Gyaɗa kai kawai yayi batareda yace komai ba
Ya jima yana tuƙi kafin yace “Madam ta rasu”
Gabana ne ya yanke ya faɗi take naji wani tsoron Allah ya kuma shigata, Haƙiƙa rai ba a bakin komai yake ba, ban tanka ba haka muka cigaba da tafiya
Ganin kamar yana bin hanyar masarauta nace “ina zamu?”
Shiru yayi batareda nuna alamar ya ma ji mai nake cewa ba
Ganin ba kulani zaiyi ba ya sanya nace “dan Allah kar ka kaini nan, bani son kuma taka cikinta in har ba’a matsayin matarka ba, ka bari na kuma shiga cikinta da darajata da mutuncina na roƙeka” na faɗa ina haɗe hannayena
Bai tankani ba ya cigaba da tafiyarsa, tafiya mai ɗan nisa har ya wuce masarautar sannan yayi packing ƙofar wani madaidaicin gida wanda yake kusada ruwa
Bayan mun shiga tsaye nayi ina bin wajen da kallo dan ba ƙaramin kyau yayi ba, flowers ɗin sunada matuƙar ɗaukar ido
“Let’s go in” ya faɗa
A hankali na bi bayansa inata kalle kalle dan wajen ya min kyau sosa
Bayan mun shiga dubana yayi yace “ki zauna a nan”
Murmushi na saki sannan na gyaɗa kai
“Mint tea please” ya faɗa batareda ya dubeni
Miƙewa nayi na shiga kitchen sai naga akwai kusan komai na buƙata, mint tea ɗin nayi masa sannan nayi mana pancake kana na kai masa
Ya ci ba laifi sannan ya miƙe yace “zan tafi, take care!”
Har ƙofa na rakasa ina masa waving sai dai bai ɗaga min hannu ba, taɓe baki nayi da ya wuce ina faɗin “jin kan tsiya”
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, baya samun zuwa da rana amma ya kan zo da dare kowacce rana kuma muna waya da shi in ya samu sarari, a ƴan kwanakin mun samu shaƙuwa sosai tsakaninmu haɗe da fahimtar juna
Gobe ta kama ranar da zan bar nan na koma ƙasata, sosai nake jin zanyi kewarsa dan bansan iya lokacin da zai ɗauka kafin ya shawo kan Big Madam ya zo ba……
[11/22, 10:49 AM] Muslima????: 87&88
Washegari da sassafe na shirya dan da wuri zamu tashi, na so sanarma da Sydeek da wuri zamu tafi amma sanin yanada abubuwan yi da safen na office ya sanya ban sanar mishi da wuri ba ne, note na rubuta masa haɗe da address ɗina na chan sannan na ɗauki jakata na nufi waje inda chauffeur ke jirana
Ban ƙara awa guda ba a Abu -dhabi jirginmu ya ɗaga, zuciyata cikeda kewar Sydeek
VIRGINIA
Cikin shauƙin sake dawowa ƙasata cikeda nasara na sakko fuskata ɗauke da murmushi
Mom da Daddy da ke tsaye na nufa da gudu tareda hugging ɗinsu ina faɗin “i miss you ai much” ƙwalla na ɗigo min
“Welcome back Habeebty!” Cewar Mom tana rungumeni sosai
Na so fara wucewa headquarter nayi reporting dawowata amma Daddy ya hana yana faɗin nagaji, dole na bi su
Muna isa bakin gate ɗin mansion ɗinmu na lumshe ido ina faɗin “home sweet home”
Bayan mun shiga ciki ɗaki na wuce cikeda jindaɗi, an canza komai na cikin ɗakin zuwa favorite color ɗina peach and white, murmushi na saki tareda faɗawa kan Queen size bed ɗina ina faɗin “i’m back”
Na ɗauki few minutes idona a rufe ina tunanin Sydeek kafin na miƙe ina faɗin “Anitha you have alot to do”
Miƙewa nayi tareda faɗawa bathroom, within few minutes na shirya cikin white long sleeve and white trouser sai nayi rolling peach veil haɗe da ɗaukar peach jacket, sannan na sanya jewelleries na ɗauki small peach bag pack da na zuba ID card da phones ɗina sannan na fice
Mom da ke setting table ita da Maid tace “Habeebty har kin fito, ke bazaki huta ba”
“Huhhh! Mom ban gaji ba, trust me” na faɗa da smile a fuskata
“Alright je ki kira Daddynki, ya zo mu ci abinci” ta faɗa
Ajiye bag pack ɗita nayi kan sofa sannan na haura kan stairs dan kiransa, tare muka fito yana faɗin “Anitha you have to resign, bazan iya jure barinki kina gararamba ba kina mace, i can’t anymore, atleast all this years nayi respecting interest ɗinki, is high time ki duba rashin dacewar aikin gareki!” Ya faɗa worried
Gyaɗa kai nayi tareda cewa “i will think about it”
Silently muka ci abincin, banyi finishing plate ɗina ba nayi pecking ɗinsu tareda ɗaukar car keys nace “i will be going, i love you” na fice
Da kaina nayi driving kasancewar yana cikin hobby ɗina, duk chauffeurs da muke da in ba official fita ba ce i prefer driving myself
Less than 30 minutes ya kaini Langley headquarter
Cikin girmamawa aketa gaidani tareda min Congratulations har na ƙarasa cikin office ɗin shugaba
“Congratulations Anitha Aldama” ya faɗa yana miƙo min hannu
Shaking hands mukayi sannan nace “Thank you sir!”
Mun jima muna ɗan magana kafin nayi requesting ya barni naga criminal ɗin
“Zaki iya zuwa” ya faɗa da smile
Godiya nayi masa sannan na nemi securities biyu muka tafi tare
Wajen was underground, a hankali nake bin bayan security ɗin da yayi min jagora zuwa wajensa, sai da muka ƙarasa ciki tukunna aka kunna fitila take haske mai mugun ƙarfi ya gauraye wajen
Rintse idanunsu criminals ɗin suka fara yi suna kare idonsu da hannu
A hankali na ƙarasa inda Yar yake tareda ƙura masa ido, kansa a sunkuye yake ya rufe idonsa da tafin hannunsa
Murmushi na ɗan saki sannan nace “Prince Yar!”
A kiɗime ya ɗago kai ya kalleni, cikin ruɗewa ya fara bi na da kallo cikin kokonto
Murmushi na saki tareda cewa “it’s a pleasure meeting you here”