SARKI HAUSA NOVEL

SARKI HAUSA NOVEL

Kwance nake kan gado ina danne danne a wayata, number Prince Sydeek na danna sai dai har ta katse bai cira ba kamar ko yaushe tun bayan tahowata

Tsaki na ja ina faɗin “kar ka ɗaga ɗin, nima bazan kuma kiranka ba”

Mom ce ta shigo ɗakina tace “Habeebty Daddynki yanada baƙi yace ki kai musu ruwa da snacks sannan kiyi setting table”

Turo baki nayi sannan nace “Mom wai babu maids ne, why me?” Na ƙare ina miƙewa ina zumɓure zumɓure

After dress kawai na sanya kasancewar bum short da top ne kawai a jikina sannan na fice tareda ɗaukan tray da cups na wuce corridor ɗin da zai sadani da meeting parlor ɗinsa

Cikin sauri sauri dan ba ma ko kalli baƙin ba na fara setting dining area, haka nayita kaiwa da kawowa ina zumɓure zumɓure har na gama, batareda na gaida baƙon ba wanda ya juya min baya coz dinning area yana bayan cushions ɗin nace “Daddy table ɗin is set, ni na tafi”

“Alright!” Daddy kawai ya faɗa

Wucewa nayi ina mamakin ƙamshin turaren da jikina ke bani na san shi, taɓe baki nayi nace “whatever” tareda komawa ɗakina

Misalin bakwai na dare na sauko dan yin Dinner

Daddy da Mom na zaune kan dining table suna ɗan taɓa hira kafin time ya cika

Zama nayi kan kujera ina cewa “barkanku da hutawa”

“Anitha please je ki kaima baƙonmu abinci, he is a very important person sauka a hotel bai kama ce sa ba, that’s why nayi pleading ya zauna a nan, men ɗinsa kuma suka wuce” ya faɗa

“Huhhh! Why me Daddy!” Na faɗa ina girgiza kai

“Please, kinga idan maids suka je ba’a ɗaukesa da muhimmanci ba, and from all indication ba ƙaramin mutum ba ne duba da yanda ya zuba hannun jari a mining industry ɗinmu, so please kiyi abinda na ce” ya faɗa yana haɗe hannayensa

“Huhh!” Kawai na faɗa tareda fara serving kaina abinci, sai da na gama cinye plate ɗina sannan na miƙe na nufi kitchen na shirya tray sannan na nufi Vip lounge

Ina zuwa bakin ƙofar wajen securities ɗinsa suka ta so min ba sauƙi kamar sunga makami a hannuna, sai da sukayi scanning ɗina kafin suka bari na shiga

Tsaki na ja ina faɗin “jaraba! Sai kace in na shiga cinyesa zanyi, ni Daddy ya san sai an dizgani shine zai wani turoni nan” na ƙare ina kutsa kai cikin parlorn bayan na ja tsaki

Ban taddasa a parlor ba, nayi niyyar ajiyewa na fice sai kuma naga rashin dacewar hakan tunda yanda naga Daddy na ta kambamasa, he must be someone important

Kujera na samu na zauna inata ɓata fuska ina sauraron fitowarsa, mintina da dama sannan aka turo ƙofar

A zabure na miƙe ina faɗin “Sydeek!!” Cikin tsantsar mamaki

Kallona yayi tareda harɗe hannayensa a ƙirji ya tsureni da idanunsa da suke sexy and sleepy

“Ya akayi ka zo nan?” Na faɗa cikin tsantsar mamaki

Bai tankani ba sai ya samu waje ya zauna tareda buɗe flask ɗin, ya ɗan ɗauki lokaci yana kallon abincin kafin ya ja plate yayi serving kansa

Waje na samu na zauna tareda kafesa da ido, har ya gama cin abincin bai tankani ba

Bayan ya gama juyowa yayi sannan ya maido hankalinsa kaina sai dai still bai furta komai ba

Tsuke baki nayi gamida kauda kaina gefe, shiru ne ya biyo baya

Ganin ba zai yi maganan ba nace “wai mene ka biyoni?”

“Aurenki na zo nayi” ya faɗa a taƙaice

Taɓe baki nayi nace “ni bazan auri wanda bai san darajata ba”

Slight smile ya saki sannan yace “rashin sanin darajar ne ya sanya na baro masarauta ta nazo ko”

Shiru nayi tareda turo baki gaba

“Yaushe ne zaki sanar da iyayenki zancena?” Ya faɗa idanunsa a kaina

Shiru nayi sannan nace “amma ya akayi kasan mahaifina?”

“Maganar da ke tsakanina da shi business ce, yanzu ina miki maganar tsakanina da ke ne” ya faɗa idanunsa a kaina

Murmushi na saki sannan nace “zan musu magana yau” na ƙare ina blushing

Gyaɗa kai yayi sannan ya miƙe yace “fine!, idan na tafi mahaifinki ba zai ce nayi disrespecting ɗinsa ba?” Ya faɗa

“Meyasa zaka tafi?” Na faɗa

“Nayi reserving hotel ne, and i’m a bit uncomfortable a nan” ya faɗa

Turo baki nayi nace “zai ji ba daɗi dan baka ga yanda yake ɗaukinka ba, and yanzu idan na sanar mishi in-law ɗinsa ne, i think gara ka zauna kawai and make yourself comfortable, you are at home” na faɗa da smile

Bai tanka ba sai ya koma ya zauna yana sakin sigh

Cikin wani irin matsanancin farinciki na fara jin zuciyata, ina ƙoƙarin zama yace “Anisa it’s late, ki koma ciki hakanan”

Turo baki nayi sannan na miƙe tareda nufar ƙofa

“Anisa!” Ya kira sunana

Dakatawa nayi tareda juyowa

Ya ɗan kalleni na few seconds kafin yace “i missed you, ki gaida Mom”

Blushing na fara na ma rasa mai zance sai kawai nayi covering face ɗina tareda ficewa ina smiling, bayan na rufo ƙofar jingina nayi da ƙofar ina feeling yanda butterflies ke min yawo

Murmushi na saki tareda cewa “wallahi ina son shi” na wuce zuwa ɓangarenmu cikin jindaɗi

A parlor na tadda Mom da Daddy suna kallo, Mom ce ta ɗago kai tana kallona sannan tace “kin daɗe and why are you blushing?”

Ƙarasawa nayi wajenta tareda faɗawa jikinta ina sakin dariya

“Ke mene matsalarki?” Cewar Mom cikin mamaki

“Mom he is the guy da ya min proposing, and kinsan shine S A R K I na Abu-Dhabi yanzu” na faɗa cikin blushing

Daddy da ya saki baki yana kallona yace “mene?!!”

“Yes Daddy!” Na faɗa da smile

Sosai duka iyayena sukayi farinciki, mun ɗauki lokaci kafin na koma ɗaki na kwanta, ko da na shiga na tadda missed call har biyu da new number

Bayan na watsa ruwa na janyo wayata tareda kiran number, Sydeek ne da banyi tsammani ba, mun ɗauki lokaci mai tsayi muna hira nan ya sanar min cewar week ɗin nan idan Daddy ya amince yakeson a yi aurenmu

Da mamaki nace “week ɗin nan fa!”

“Eh” ya faɗa a taƙaice

Cikin neman magana nace “ni fa ban isa aure ba”

Murmushi ya ɗanyi mai sauti sannan yace “ai nasani, nima rainonki zanyi”

Dariya na saki cikeda kunya sannan nayi masa sallama na kwanta bacci

PRINCE YAMEEN POV

Kwance yake kan gado sai faman rarrashin Salamat yakeyi kan ta haƙura ta amince ta aureshi

Kusan kwana biyar kenan yana abu ɗaya na rarrashinta itakuma ta haƙiƙance bazata haƙura ba kuma bata yafe masa ba

Nisawa Prince Yameen yayi sannan yace “Salamat kinsan mai yasa na zaɓe ki?”

“Sai ka faɗa” ta faɗa ciki ciki

“Saboda duk cikin waɗanda nayi tarayya da su kece kika fi bani tausayi, i can recall lokacin da kika zo palace you were so innocent, nine silar ɓacinki and kece mace ta farko da na amshi virginity ɗinki, you were innocent baki san komai ba, amma sauran nasani they wanted to seduce me not knowing that ke kaɗai ce macen da ban taɓa jin kin isheni ba, i’m really sorry nasani na cuceki, but atleast idan kin amince min zan kula da ke da gidanku har ƙarshen rayuwata, zan baki dukkan abinda kike buƙata, please find a place in your heart to forgive and accept me” ya ƙare slowly

Kuka ta fashe da shi, bai ce mata komai ba har ta idar da kukanta sannan yace “please let me take care of you, mu sha magani tare, kici abinda nake ci, ki samu kwanciyar hankali without any stress, atleast zan iya affording wannan, accept me!”

Cikin shashekar kuka tace “na amince Yameen, zan aureka!” ……

LITTAFIN KUƊI NE 300 TO 1401611541 FATIMA LAWAL SAID, ACCESS BANK OR MTN CARD TO 08167888934
[11/24, 3:22 PM] Muslima????: ???? S A R K I

96&97

Washegari da sassafe na tashi na haɗa masa breakfast cikeda ɗaukin sake ganinsa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51Next page

Leave a Reply

Back to top button