SARKI HAUSA NOVEL

Bai ɗauke kansa daga dubana ba har na idar da kukana
Taɓe baki yayi sannan yace “mene haɗina da rayuwarki da kika zauna kina lissafin, na tambayeki?” Ya faɗa yana ƙureni da idanunsa
Girgiza kai kawai na farayi idanuna na zubda hawaye
Dafe kansa yayi sannan ya jingina da kujera ya furta “Ya Allah”
Kallonsa kawai nake ina yaba rashin kirki irin nasa, ace duk ƙaryar da na sheƙo masa ya kasa nuna tausayawa a gareni sai kace busashiyar zuciya ke garesa
“Leave!!!” Ya furta a sanyaye batareda ya buɗe idonsa ba
Muskutawa nayi nace “na’am?”
Ware idanunsa yayi a kaina sannan yace “please ki fita, kin haddasamin ciwon kai”
“Sannu Prince, ko na haɗamaka shayi ne?” Na tambaya ina gyara zama
“Leave!!!!!” Ya daka min wata gigitacciyar tsawa
Cikin hanzari na miƙe nayi ƙofa dan tsawa ba ƙaramin firgitani takeyi ba
Tsaki na ja ko da na fito apartment ɗin nace “masifaffe, gobe ma sai nadawo wallahi, dagani kai ne mugun da nake nema, matsafi kawai”
Dariya nayi da nace haka, amma tau matsafi mana, in ba tsafi ba mai ne dalilin da ina kallonsa nake ruɗewa
Tsaki na ja nace “Anitha share batunsa a yau”
Ɗaki na koma, ban tadda Junnut ba sai Salamat dake shirin fita itama
Ɗan murmushi nayi sannan nace “ina zuwa haka goshin magariba”
Ɗan tsuramin ido tayi nasan tana tunanin dalilin da yasa na tankata ne, murmushi nayi nace “yawo zaki hala”
Murguɗa baki tayi tace “wajen Prince Yameen zani kinsan duk yanda akeson shiga tsakaninmu bama rabuwa”
Murmushi nayi nace “toh yayi, amma wai shi bayada wani aikinyi ne?”
Harara ta watsamin sannan tace “yanada dukkan abinda yake buƙata na me zai wahalar da kansa”
Gyaɗa kai nayi nace “hakane kam, sai kin dawo” na faɗa ina bin bayanta da kallo
Zama nayi kan gado na ɗanyi reporting ƴan abinda nasamu gameda halayyar Princes ɗin sannan na kira Mom, bamu wani jima da ita ba na kira Daddy shima mukayi guntuwar hira na katse
Bayan anyi sallar isha’i shiryawa nayi cikin simple doguwar riga blue color
Junnut da shigowarta kenan tace “dagani dai fita zakiyi ko?”
Murmushi nayi nata nace “wallahi kuwa zani walk ne kaɗan, sannu da dawowa”
Miƙomin leda tayi tace “bread mukayi nace bari na kawo miki, na kula kin fi son kayan flour”
Cikeda jindaɗi na rungumeta nace “nagode sosai Habeebty, kamar kinsan banyi dinner ba bari nadawo na ci”
Gyaɗa kai tayi tana dariya tace “sai kin dawo”
Murmushi nayi sannan na fice
Tafiya nake cikeda shauƙi da jindaɗin yanayin, zaune na ga Prince Yar a inda na saba zama
Ɗan murmushi na saki sannan na ƙarasa nace “ka fito da w uri dan ka taremin wajena”
Smile yayi kawai sannan ya ɗan matsa ya nuna min kusada shi yace “zauna”
Zama nayi sannan na miƙa masa jacket ɗin nace “ga shi”
Amsa yayi sannan ya kama hannuna ya ɗora kan cinyarsa yace “mene sunanki?”
“Batool” na basa amsa jikina duk ba daɗi ba dan ya riƙe hannun ba amma murzawar da yake sosai yake kashemin jiki
“Sunanki mai daɗi” ya faɗa da murmushi
Murmushi na sakeyi sannan nace “nagode”
“Na tambayeki?” Ya faɗa yana kallona
Sauke kaina ƙasa nayi sannan nace “eh”
“Mai yasa kika ne ɗakin Yameen rannan?” Ya faɗa cikin damuwa
Kallonsa nayi ina mamakin dalilin da zaisa ya tambayeni something personal
“I’m sorry, bansan dalilin da ya sanya nakejin na damu gameda lamuranki ba” ya faɗa a sanyaye
Ɗan murmushi na saki sannan nace “bakomai, kirana yayi ne kawai”
“Daga yau in ya ƙara kiranki please kada ki kuma zuwa” ya faɗa da smile
Ɗago kai nayi na kallesa ido cikin ido
Gyaɗa kai yayi yace “he is my brother, Batool i can’t trust him with you saboda nasan halinsa”
Murmushi nayi nace “toh insha Allah”
Ƙara matse hannuna yayi yace “akan Sydeek kuma don’t ever get yourself deceived by him, kar ki taɓa yarda dashi Batool” ya faɗa
Murmushi na kuma yi sannan nace “toh, insha Allah”
“Naga har yanzu baiyi accepting ɗinki ba, nima i am trying my best naga ya amince da ke, so please kada ki bamu kunya duk abinda nace kiyi ki yi shi wanda nace ki bari ki barshi, okay?”
Gyaɗa kai nayi nace “toh”
“Good girl, idan yayi accepting ɗinki zan kawo miki utensils da zaki dinga masa amfani da su” ya faɗa da smile
Gyaɗa kai nayi sannan nace “toh shikenan”
Murmushi ya sakeyi sannan yace “it’s getting late nasan matata ta fara faɗa yanzu” ya ƙare da dariya
Dariya nima nayi sannan nace “okay”
Miƙar dani tsaye yayi sannan yace “sanyi ake kema ya kamata ki koma, muje na raka ki” ya faɗa
Har ƙofar building ɗinmu muka ƙaraso sannan ya dubeni da murmushin da baya yankewa a fuskarsa yace “take care”
Murmushi nayi nace “thank you”, sannan na kama hanyar shigewa ciki
Bayan na kwanta a gado tunaninsa ne na dinga tariyowa, mai yasa zai ce kada nayi trusting Prince Sydeek, sanin bazan samu amsar nan take ba na rarrashi kaina na kwanta …….
S A R K I IS NOT FOR FREE
MASU SON FARA PAYMENT KUYI CONTACTING ƊINA TA 08167888934
[11/9, 06:05] Mss Flower: ???? S A R K I
By Mss Flower????
☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSO….
*11&12*
Bayan mun gama wannan zancen bathroom na faɗa dan watsa ruwa
Ina fitowa Junnut tace “yanzu aka aiko Madam na nemanki, kiyi sauri kar ki ɓata lokaci, Allah yasa lafiya dai”
Jiki a sanyaye nace “ameen”, na fara shiryawa
Hakanan naji gabana yana faɗuwa ko da na tunkari building ɗinta, a hankali na tura ƙofar
Gabana ne yayi mugun faɗuwa sakamakon Prince Yameen da na gani yana zaune ya ɗora kansa kan cinyarta yanata shagwaɓa
Tsayawa nayi bakin ƙofa ina kallonsu
“Ƙaraso nan” ta faɗa fuskarta babu yabo ba fallasa
Ƙarasawa nayi tareda zama ƙasan carpet nace “barkanki da hutawa”
“Barka, mai ne haɗinki da Prince Sydeek?” Ta jefomin tambayar
Kaina a ƙasa nace “ba abinda ya haɗani da shi ranki ya daɗe”
Prince Yameen ya miƙe yana faɗin “ƙarya takeyi, kalli dukan da yayi min fa ta dalilinta”
“Mai ne haɗinki da shi?” Ta kuma tambaya sounding ordering
A sanyaye nace “wallahi ba abinda ya haɗani da shi”
“A ina kike aiki yanzu?” Ta tambaya
“Yau Princess Zairah ta sallameni ba’a bani wani post ɗin ba” na faɗa ina wasa da yatsuna
“Yawwa, aikinki zai koma sashen Prince Sydeek ne daga yau, kuma ki tabbata ya karɓeki dan idan har yayi rejecting ɗinki aikinki a masarautarnan ya ƙare” ta faɗa da smile a fuskarta
Cikin tashin hankali nace “Madam ance shi ba mazauni ba ne”
“Shiyasa nace ki zama personal maid ɗinsa domin duk inda ya je ki tabbata kuna tare da shi” ta faɗa cikin umarni
A sanyaye nace “idan ya ƙi amincewa dani fa” na ƙare cikin sigar tausayi
Hannu ta saka ta shaƙe wuyana tareda zaro idanunta tace “ya zama dole kiyi dukkan abinda zakiyi ya amince da ke domin tunda muke dashi bai taɓa nuna kulawarsa akan kowa ba sai ke, dan haka dole ya amince da ke idan ya ƙi bazaki ƙara shan ruwan masarautar nan ba” ta faɗa tareda sakin wuyana ta tureni gefe
Wani irin ɗaci naji a zuciyata ina jinjina juriya da haƙurin da ƴan aiki keyi da iyayen gidansu
Ina tsaka da wannan tunani tace “akwai sharaɗi a aikin da zakiyi”
Idona da ke cike da ƙwalla na ɗago na kalleta nace “wani sharaɗi?”
“Dukkan abincinsa da abin shansa ya zamana daga hannunki suke fitowa, bashida yadda kuma bai san sabo ba dan haka aikinki mai matuƙar wuyane domin dole ki shawo kansa ya dinga ci da sha daga hannunki, idan naga effect na aikinki zan miki kyauta mai tsoka sosai” ta faɗa da murmushi a fuskarta