SARKI HAUSA NOVEL

Gyaɗa kai nayi sannan nace “insha Allah zanyi iya ƙoƙarina”
Murmushi ta saki sannan tace “Prince Yar zai baki kwanukan abinci da abinsha da zaki dinga bashi yana ci a cikinsu”
“Toh” na faɗa chan ƙasan murya
“Ki tabbata ya amince da ke, zaki iya tafiya” ta faɗa idanunta a kaina
Miƙewa nayi nace “nagode” sannan na fice
Da tunanin wannan magana da yadda zan ɓullowa al’amarin na kwana
Washegari ban tashi bacci ba bayan asuba sai takwas da rabi, kafin tara da kwata nayi shirina na wuce wajen Junnut
Ita ta bani wani abin da zan sawa cikina sannan na wuce na nufi sashen Prince Sydeek
Gabana na bugun bugawa na tura ƙofar bayan lokaci mai ɗan tsayi da na ɗauka ina knocking
Zaune na gansa kan cushion idanunsa sanye da glass yana duban pc da alama aiki yake mai muhimmanci
Sallama nayi shiru bai amsa ba har wajen sau uku, ganin haka na koma gyaran murya sai dai bai ma ko nuna alamun ya ji ba
Na ɗauki kusan minti sha biyar a tsaye duk ƙafafuna sunyi sanyi kafin ya ɗago kansa daga duban pc ya sauke idanunsa da ke so sexy a kaina
Ganin ko kalma ɗaya bai furta ba yasanya nayi murmushi sannan na ajiye masa mayafin da ya lulluɓa min jiya nace “gashi, nagode”
Kallon mayafin yayi sannan ya kalleni sai kuma ya ɗauke kansa ya maida kan pc
Turo baki nayi dan sai naji ba daɗi, da alamu ba ƙaramin artabu zamu sha da shi ba kafin ya amince dani
Gyaran murya nayi sannan nace “uhm da..dama”, kasa ƙarasawa nayi sanadiyyar idanunsa da ya sauke kaina masu matuƙar rikitarwa da sanya mara gaskiya ruɗani
Ɗan ɓata fuska yayi kaɗan sannan yace “kin dameni”
“Ehm dama Madam ce tace nadawo nan yi maka aiki ne” na ƙare ina kallon ƙasa
Ɗan jim yayi sannan ya yatsina fuska yace “bana buƙatar maid”
Cikin tashin hankali nace “dan Allah ka ɗaukeni”
“Leave please!!” Ya faɗa a sanyaye
Girgiza kai nayi idanuna na kawo ruwa nace “please”
Cikin ƙanƙanin lokaci fuskarsa ta canza, ɓacin rai ya nuna sannan ya nuna min ƙofa cikin tsawa yace “leave!!!”
A firgice har jikina na ɗan ɓari na fita idanuna na kawo ruwa, inada matuƙar jarumta ni kaina nasani sai dai na rasa dalilin da yasanya bana jin ƙarfi a gaban wannan Sydeek ɗin
Zama nayi akan steps ɗin apartment ɗin na haɗe kaina da gwiwa na lula tunanin mafita akan abinda ya kawoni
Na jima a nan kafin naji an buɗe ƙofar, ɗago kaina nayi sai idanunmu suka sauka cikin na juna
Dubana yayi ya wuce batareda ya nuna wani impression a fuskarsa ba
Ɗan taɓe baki nayi nace “in kai taurin kai ni naci, dan dole zaka amince dani dan nafi zargin kai ne wanda nazo nema “
Ya ɗauki lokaci mai tsawo ganin hakan ya sanya na jingina da bango, iskar wajen da ta fara kaɗawa ta sanya wani ɓarawon bacci yayi gaba dani
Ƙarar buga ƙofa ce da ƙarfi alamun ya dawo har ya shige ya sanya na miƙe ina murza ido
Ganin rana ta fito sosai ya sanya nagane na jima ina baccin, ƙofar na buɗe na shiga
Ban tadda shi a parlor ba hakan ya sanya na samu waje kan cushion na zauna, ya ɗan jima kafin ya fito
Kallona ya tsaya yayi da mamaki ƙarara a fuskarsa
Murmushi na ɗan saki sannan nace “akwai abinda kake buƙata”
Siririn tsaki ya ja sannan ya ɗauki system ɗinsa ya shige cikin ɗaki
Murmushi na saki nace “hakanan zakayi haƙuri dani”
Sanin ba zai fito ba ya sanya na juya na fice
Ina fita mukayi gware da Prince Yar dake ƙoƙarin shigowa sashen
Dafe goshina nayi ina furta “ouchhh”
Cikin kulawa yana dafe da goshinsa yace “are you hurt?”
Girgiza kai nayi da murmushi a fuskata sannan nace “rannan nayita nemanka na baka jacket ɗinka ban ganka ba”
“Aiki ya min yawa kwanakin nan” ya faɗa a gajiye
“Kana aiki ne?” Na tambaya da ƴar fara’a
Ɗan tsaki ya ja yace “ina running business ne na brother na” ya faɗa
“Prince Sydeek?” Na tambaya
“Eh, he is business tycoon” ya faɗa idanunsa ƙur a kaina
Ɗan murmushi nayi nace “toh na kawo maka anjima”
Murmushin ya mayar min sannan yace “mai kikeyi a nan?”
Ɗan yamutsa fuska nayi nace “nan aka dawo dani aiki ne”
Fuskarsa ce ta canza zuwa damuwa sannan yace “shikenan, becareful with your heart please”
Cikin rashin fahimta nace “eyye?”
Murmushi ya saki sannan ya riƙe hannuna ya ɗan murza ya saki ya wuce ciki
Da mamakinsa na koma sashenmu inata nanata kalmar “becareful with your heart” ……
S A R K I IS NOT FOR FREE
[11/9, 06:05] Mss Flower: ???? S A R K I
By Mss Flower????
SIMILARITIES OR RESEMBLANCE OF STORY IS COINCIDENTAL
☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSO….
DAN ALLAH MU DINGA YI WA JUNA ADALCI, BANA WULAƘANCI AMMA BANA SON TAKURA BABU DALILI, IDAN BA PAYMENT NA S A R K I ZA KI YI BA, KADA KI NEMENI DAN ALLAH????NUMBER ITA CE 08167888934
*15&16*
Washegari misalin tara na je sashensa, ban tadda sa a parlor ba hakan ya bani damar gyara masa wajen da kyau harda canza tsarin wajen, sannan na kunna burner na saka turaren wutan da ke wajen
Bayan nagama zagaye na farayi, cikin ikon Allah idona ya sauka akan wani siririn corridor, ina bin hanyar sai gani a kitchen
Babban kitchen mai ɗauke da duk wani kayan sarrafa abinci, tsaf yake kuma komai sabo sai tukunya guda ce naga alamun ana amfani da ita, ƙara ɗan gyara wajen nayi sannan na lula duniyar tunanin abinda zan dafa masa, na jima kafin na yanke shawarar frying potato
Yanka mai kyau nayi with different shapes saboda da cutter nayi amfani sannan na soya, cikin bowl na zuba sannan na zuba soy sauce a mini bowl shima, bayan nan na haɗa masa black tea sai tashin ƙamshin cinnamon da ginger yake dan ni kaina sai da nayi salivating
Murmushi na saki dan na gamsu da abincin sannan nayi covering tray ɗin da white sheet na ɗauka na fice, a centre table na ajiye sannan na samu waje ƙasan carpet na zauna ina kallon tv
An ɗauki lokaci mai tsayi kafin naji ƙarar buɗe ƙofa, ɗaga kaina nayi na kallesa sannan nayi saurin sadda kaina
Sanye yake cikin riga da wando farare tass wanda sukayi matuƙar yi masa kyau, kallo ɗaya yayi min ya kauda kansa ya samu waje a kujerar ya zauna ya fara danna waya
“Ina kwana” na faɗa ina satar kallonsa
Bai ɗago daga duban wayarsa ba, bai kuma nuna alamun ya ji ni ba
Murmushi na ɗan saki sannan na matsa kusada center table ɗin na yaye sheet ɗin kai, na tsiyaya black tea ɗin a cup nace “ga abinci”
Ɗago kai yayi ya kalleni tareda aikomin wani mugun kallo mai cikeda gargaɗi, sannan ya maida kansa batareda ya kalli abincin ba
Shiru nayi na raɓe bayan kujera ina mamakin murɗaɗɗen hali irin na sa
Muna nan zaune haka Prince Yar ya turo ƙofar bakinsa ɗauke da fara’ar da ke masa kyau sosai
A sanyaye nace “ina kwana”
Dubana yayi yace “lafiya, kece new maid ɗinsa ne?”
Da ɗan mamakin zancen nasa na ɗaga kai nace “eh ni ce”
“Masha Allah, ki kulamin da ɗan uwana kin fahimta, baya son yawan magana saboda tana saka sa damuwa da ciwon kai, so kiyi aikinki kawai a nitse batareda kinyi hayaniya ba” ya faɗa
Prince Sydeek sai a lokacin ya buɗe baki da ƙyar yace “i still don’t need a maid, she is leaving”
Prince Yar zama yayi a kujerar da yake yace “Please accept this one, she looks quite alright ko bakomai zata dinga yi maka abinci tunda baka joining ɗinmu a na gida, please kar kace a’a” cewar Prince Yar
Prince Sydeek taɓe baki yayi yace “zan iya abincina da kaina when necessary sannan zan iya ordering wani wajen”
“No, please kaima kasamu nutsuwa, is hightime by now kanada mai tsare abincinka tunda ka ƙi yin aure har yanzu” cewar Prince Yar yana riƙe hannun Prince Sydeek