ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Amman am sure ni doguwace kuma tsayina ma daidaici, komina mai tsarine,amman cikar fuskata da cikar halittar jikina duk na Maah ne,da kyawawan hakoranta,da wushirya,masha Allah dai kawai za,ace komi yaji.
Sweetheart kuwa komi na Abbu ne har rashin kib’arta, Idan tayi dariya sak Abbu.
sweetheart kamar kwalin omo take ba nauyi,ga kuma fara,a ko bacci take.
Shiyasa tafini qawaye dayawa don ni k’awayena basu wuce biyar bah, itako lodi lodi haka zaka gansu,in fita mukai kan na had’u da Wanda na sani ta had’u da mutun goma…….. Kai sweetheart akwai kwashe kwashe wallahi.
yah meenah ma ba laifi don Itama tubarkallah, Allah yayi mata halitta maikyau, komi yaji kenan don tun yanzu har samari sun fara mata yawa,saida na bata shawarar korarsu don inhar tace yanzu zatai soyayya ba makawa Dady aure zai mata, duk ta firgice don tana son boko kamarni.
An tambayeni me zan karanta nace I like medicine Shima kuma b’angaren hakori,da farko Abbu da maah sunce Ina karatun yayi tsawo,kuma zansha wuya, saida nayi masu kuka sannan suka barni, Shima saida sweetheart taga dagaske baza su barni ba,yasa ta kira Yah Areef tana kukan shagwaba take sanar mashi, dafari cewa yai tabani wayar ya lallasheni, Amman nace tace nafita.
Shi yayi magana aka barmun cause d’ina, Yah meenah kuma, nursing.
kuma nace bazan je wata k’asa ba anan gida Nigeria zanyi.
Yanzu har mun cike komi an bamu admission anan Abuja zamuyi karatun, kuma day zamuyi, sweetheart kasancewar karatun bai wani d’a d’ata da k’asa ba bata wani d’auki cause mai wuya ba, don education ta d’auka fanin intergrated science.
Yanzu registration za muyi mu fara zuwa,b’an gare guda kuma cikin satin nan su Yah mujahid zasu dawo,sweetheart kamar tayi hauka don dad’i nikuwa da naji Ana maganar ma gabana fad’uwa yake sosai.
wannan kenan.
Mu had’u next page.
Mom muhsen ce
Mrs bb.
[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: ????????????????????????????????
ABIN CIKIN RUHINA
Written by [Mrs bb]
Mom muhsen ce
NI AISHA ABUBAKAR (MRS BB) INAYIWA D’AUKACIN MASOYANA BARKA DA SALLAH FATAN MUNSHA RUWA LAFIYA UBANGIJI YASA MUNA DAGA CIKIN Y’AN TATTATUN BAYI, ALLAH YANUNA MANA WATA SHEKRAR LAFIYA.
________________________
????????AINUWA ????RITER’S✍????
????SSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________
10&11.
Har na isa b’angaren Anni tunani ya cushe Mani k’walwa, ni banga abun fushi anan ba, to mema nayi masa har haka koko don na tafi wani waje bayan nasan zai dawo, to in nasan zai dawo goyashi zanyi, koko mezan masa.
Tsaki naja sanda nake ajiye mayafi na, kallona yah meenah tayi tace.
“Lafiya dai, ya kuka k’are dashi.”
Raina 6ace na wurgar da jikkata nace,
“Wai yah meenah ni za,a dizga kiga fa yadda yake ta shan k’amshi, kodai ubana in yaje unguwa ya dawo iyakar abunda zan mar kenan, to d’aukarsa zanyi don murna shine zai banza dani, to gidan ya tarar bazan lamunci wulakanci ba, idan wancan karon anyi nashanye yarinta Ce yanzu kuwa da girmana bazan jura ba wallahi.”
Mai yah meenah take shafawa tace mun,
“Ban son wanan zafin ran naki khairat, ki ringa bin komi ahankali.”
“Haba yah meenah kina ganin yadda yayi Mani halin ko in kula, ita kuma salma kowa yana magana Amman ita uffan ta kasa cewa.”
“Nadai ce maki kiyi hakuri ki sama kowa ido, karki nuna b’acin ranki afili, ki share inkikai hakan wallahi zakisha mamaki, oya shiga kiyi wanka kizo kiyi sallah ko mangaruba bakiyi ba ga isha,i anata kira.”
Haka na d’auki maganar yah meenah saboda koba komi ita kad’ai ke kulawa da lamarina.
Yadda tace nayi haka nayi, sai gashi cikin ikon Allah nasamu yar natsuwa, wanka nayi nazo nashirya cikin kayan baccina masu shegen kyau, ummin Dubai ta aiko mana dasu kala uku uku mu uku, ba k’arya ummi naji damu, more exspicialy ni bama yini guda bata kirani bah, haka d’anta yah imran jininmu y had’u da juna, don sosai yake ji dani don duk dare idan bana komi, shima yagama duk abunda zai zaikirani video call, nan zamu d’au lokaci muna hira har wani zubin yah meenah ta zo ayi da ita, har sun saba dashi itama.
Sallah nayi na gama na jawo system dina ina cireta daga caji, yah meenah tashigo.
“Khairat kifito muci Abinci inji yah mujahid.”
“Wallahi da kwanciya zan, inyaso inci abincin anan d’aki, Amman tunda yah mujahid ne muje.”
Abaya doguwa har k’asa nasa mukafito, ina cigaba da danna system din, muna hira har cikin falon maah.
Salma ta tusa shi gaba yana cin abinci, ga uban juice da ta had’a mashi, itace keta zuba mashi surutu kamar kanyar da babu dadi.
Bama tasan mun shigo ba, mu kad’aine falon maah na wajen Abbu nasani, don baka ganinta irin wannan lokacin, idan ba tazo duba muba, don duk dare zata zo taduba idan munyi baci, in bamuyi ba tace komi muke a ajiye akwanta.
Zama nayi kusada yah mujahid k’asa nida yah meenah.
Murmushi yayi mana yace,
“Kun zama y’anmata khairat, nan bada jima wa ba zamu badaku ko.”
Dariya nayi ina danna laptop dina nace,
“Haba yah janmu kake kaima, duka nawa muke ai mun samu muma muyi yar bokon nan da ake mana yanga kanta.
Har ga Allah ni ban fad’a da wata manufa ba Amman Ashe na jawo ma kaina fitina, jinai ya ajiye spoon dinsa yace mun,
” ke!”
Cikin wata tsawa da ta firgitani bama ni kadai ba, har yah meenah ta tsorata.
Juyawa nayi ina kallonsa gabana kamar zai fito waje.
Cikin kakkausar murya yace Mani,
“Da ubanwa kike wannan maganar, watau kinga na kyaleki shiyasa zaki gaya mun magana ko.”
Yah mujahid yace,
“Look Areef, ya daga dawowarka zaka fara halinka don Allah Ka daina, ba dakai take ba, karka tada mata hankali.”
” jahid kafita cikin maganarnan kana so kace man na kyaleta, bacin maganar da tafad’a d’azu bai isheta ba shine yanzu ma tasake yin wata, shin ni abokin kine khairat, koko kakanki ne ni to zangyara maki zama, ko inuwata kika hango zaki ruga.”
Idona ya cika da kwallah nace cikin karyewar murya,
“Yah……..wata tsawar ya dakan data saka na zabura zan ruga, saida yah meenah ta rik’eni……..rawa jikina keyi hawaye nata zarya akan fuskata.
” tashi bar nan falon, idan na sake ganinki inda nake sai na b’ab’b’alla k’afafunki stupid girl kawai, kenan don ubanki har kin girma ko, to daga yau karna sake ganinki inda kikasan ma zan zauna, aguje nafice ina jin wani irin kuka yana kuccemun, Wanda har numfashina jinake yamun kad’an………..kafin na idasa d’aki ban san sanda najini yashe k’asa ba, saboda wani kullutun bak’in ciki ne ya tokaremun mak’oshi, numfashin ya d’auke……………..fitowar maah daga d’akin Abbu kenan saboda tsawar da takejin Areef na kwatsawa, taga fad’uwar khairat………aguje ta rugo tana kwalaman kira da mugun k’arfi, Amman ina numfashin ya tafi, aguje ta koma suka taho da Abbu…..kankace me gidan kowa ya taru tuni Abbu ya ruga dani asibiti, donjin duk wasu hanyoyin sadarwa na sun daina aiki, kuka riris maah keyi Wanda ya ba kowa mamaki don Abu bai tab’a samun khairat tayi kuka ba, don wani lokacin ma tafi nuna damuwarta kan salma.
Amman kuma abun mamakin salma ko gezau batayi ba, don kowa yashiga halin damuwa Amman danna wayarta kawai take, yah meenah kuka take.
Tuni yah jahid da anty shidah sun tafi asibitin.