ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

“tun d’azu na so inyi masa albishir to na duba wayar taki babu Kati, hankalina ya ya d’auku ga wannan tsaleliyar babyn,wallahi ba batun son kai bah Saudah baki tab’a haihuwar k’yak’k’yawar baby irin wannan ba, tun yanzu ma angane kyanta inaga ta girma.”

Murmushi tayi tana gyara ma babyn kwanciyar ta.
tace,
“Anni kenan ai kuwa duk wanda zan haifa to saidai ya biyo bayan Areef A komai ma,don yaro na kin san indai ta nan ne to sai dai Ashafa fatiha.”

“Ai nasan da shi nace haka nufina Cikin wad’anda kika hai……………innalillahi lawisa! Don Allah kiyi shiru Meyasa zakiyi maganar nan please na rok’eki karki k’ara irin haka,yanzu Idan Areef idonsa biyu kikai wannan maganar wallahi akwai damuwa, kin san shi da kaifin basira Abun zai zauna masa karshen ya titsiyeni akan maganar.”

“yi hakuri Qawata wallahi na shafa,a Amman bazan sake wannan maganar ba nai maki alkawarin hakan.”

Ajiyar zuciya ta sauke tace,
“Qawatah,wallahi son da nake ma Areef shahid da shahida bana masu irin sa,duk da kuwa haihuwar su nayi da cikina Amman ba na jin Su irin yadda na keji da Areef, saboda shine silar kawar mun da duk wani k’unci da nake ciki na rashin haihuwa,ta dalilin sa dangin mijina da surukata Su ka fara martaba ni, Ya fitar dani halin kuka da damuwar da na fuskanta don haka ko zan haifi singa da sabon gari wallahi bayan Areef suke,kuma insha Allah Cikin yara na babu maijin wannan sirrin,ke ma don na yarda da ke ki taya ni b’oyon sa don Allah.”

“insha Allah Qawata daga bakina dai babu maijin wannan sirrin.”

????????????????????????????????

Sai washe gari aka sanar da y’an uwa da abokan arzik’i wannan haihuwar, Wanda Alhaji farouk ya kejin kamar an masa albishir d’in gidan Aljannah.
Saboda ana gama sanar da shi wannan labarin, abokin kasuwancinsu yayi masa albishir d’in burinsa ya cika, nan take ya yi sujjadar shukru, yana mai tsananin godiya ga Allah Lallai Saudah alkhairi ce garesa,haka zalika wannan Yarinya tazo da arzik’i,nan take yake sanar da Amininsa mijin lawisa cewar asaka ma yarinyar UMMUL— KHAIRI.

Saida lantana tayi kwana hud’u tana labour baiwar Allah,duk ta fice daga hayyacinta Akwana na biyar likita yace saidai aimata aiki, ranar Alhaji farouk ya dawo duk yadda lantanar take k’unziga mashi hakan bai hana yaji tausayinta ba, nan yasa hannu aka shiga da ita theater room y’an uwanta kuka kawai Suke da iyayenta.

Saudah Kanta taji tausayin halin da take ciki saboda duk taurin zuciyarka idan kaganta sai ka tausaya, har kuka tayi Areef kansa yaji babu dad’i.
Ba,a fito da ita ba sai bayan awanni biyar, ansamu nasarar fiddo jaririyar wadda ke kama da babanta kamar Alhaji farouk yayi kaki,anyi murnar sosai kafin ashiga nemo ran uwar saidai tun abun suna ganin baida wuya har hankalin Su ya fara tashi, don duk wata kafa ta sadarwar jikinta sun duba Amman babu alamun tana da rai………….sun kwashe awa biyu akanta Amman babu wani alamun zata tashi……….dole suka fito jikinsu yayi sanyi k’alau,da gudu y’an uwanta suka tare shi yaya lantanar.

Girgiza Kai likitan yayi yace kuyi hakuri Allah ya amshi Abunsa………….inna lillahi wa Inna ilaihir taju,un hazbunallahu wani imal wakil………..abunda Alhaji farouk ke ta Nana tawa kenan babu ji babu gani sauran kuwa banda ihu da kururuwa babu abun da suke, daga mai suma sai mai fad’uwa haka wannan rana ta zo babu dad’i,duk wani wanda keda alak’a da lantana yayi kuka kamar idonsa zai fita, na yarda da maganar hausawa da akace ko naman jikinka mutun yake yanka kullum,duk randa babu shi za kaji babu dad’i balle ace ma ya rasu…..hazbunallahu wani imal wakil Allah ya jikan lantana Allah ya yafe mata tayi shahada Allah ya haska kabarinta.

Abunda Saudah ke ta fad’a kenan,
Areef ganin halin da maah d’in sa take ciki Shima sai ya kama kuka, Duk yinin ranar ummul kairi tana wajensa sai idan tayi kuka ya kaita ta sha mama.

Haka akai sadakar uku Saudah ta anshi yarinyar tace zata shayar dasu tare, Allah ya bata ladar shayarwar, babanta yayi mata hud’uba da ummu salma

Haka aka share zaman makoki kowa rai babu dad’i, yayin da Saudah kejin gidan yayi mata girma, daga ita sai yaranta guda biyar ikon Allah kenan, kamar ba itace ke kukan rashin haihuwa bah shekarun baya, sai gashi yau Allah ya azurtata da yara biyar Cikin shekaran da basu Gaza bakwai bah.

Babu wani taron suna da akai, Alhaji farouk yadai yanka ma yaransa ragunan suna daga nan suka cigaba da kalawa da Yaransu.

Rayuwar taci gaba da gara wa yayin da Areef yake primary 5 zai zana common interest yaje js one, shahid kuma shida shahida suna primary 2 sai twince Dake da y’an watannin,kulawa Suke samu sosai shiyasa suke Wata irin kib’a tajin dad’i, Abunda Saudah ta lura shine Areef yafi nuna kulawarsa ga UMMU SALMA saboda acewarsa UMMUL KHAIRI ta cika kuka da fitina,da ya dawo daga makaranta ita zai fara d’auka yana mata wak’a, yana mata rawa duk kuwa ba wai yana k’in d’aukar UMMUL KHAIRI ba Aa yana d’aukarta Amman da ta fara kuka zaice,
“Maah wallahi khairy nine bata son na d’auketa kowa yana mata wasa lafiya lau Amman ni da nazo zan mata sai ta yi tayin kuka.”

Sai tace,
“haba babban yaya ai shi yaya babba hakuri aka sanshi dashi, dukansu k’annenka ne kowa ce kuma tana buk’atar kulawar yayanta.”

Tun daga nan komi zai ma guda to zaima d’ayar,har takai yanzu khairy ta daina masa kuka, har bata yarda da kowa saishi haka Itama SALMA.

Alhaji farouk likafa tayi gaba don yanzu ya bud’e sabon kamfanin sa na sarrafa yadiddika materials, boyels ne Gasunan wasu ma bazan ce ga sunan Su ba,ya zuba ma akata da yawa hada amininsa jafar mijin lawisa.

Hakan ya ka’ra karfafa zumuncinsu sosai har iyalinsu, don wata sa,in idan su shahida basu nan to tabbas suna gidan Dadyn Muhajid da Meenah,mujahid abokine ga Areef don babu Nisa tsakaninsu ashekaru,Areef zai bashi shekara biyu Meenah kuma kanwar Su shahid ce zasu bata shekara uku……..don yanzu duka shekarar ta uku.

Gida Alhaji farouk ya fara ginawa na nuna ma sa,a yayin da zai gyara ma mahaifiyarsa wannan da suke ciki.

shekara kwana inji y’an k’arin magana har gashi y’an yaran Maah sun girma, don yanzu kowace nada 12 years

Mrs bb ce kuma
mom muhsen.

????????????????????????????
[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: ????????????????????????????????
ABIN CIKIN RUHINA

Written by [Mrs bb]

Mom muhsen ce

________________________

????????AINUWA ????RITER’S✍????
????SSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

4.

Duk yinin yau Khairat bata fito ba,saidai salma ta ringa kawo mata abinci har d’aki,tunda ta dawo daga makarantar ko salma bata nuna ma result d’inta na,yah Meenah kawai ta gani Itama don tasan bazata fad’ama kowa bah, duk yadda shahida tayi akan ta bata ta gani cewa tai wai nata yab’ace idan ankoma hutu za,a sake dubawa.

Shahida bata yarda bah haka ta rabu da ita saboda sanin Khairat badai taurin kaiba.

Kwance take ta gama sallar isha,i tana saman abun sallar salma ta shigo jikinta yayi mugun sanyi, ta samu gefen gadonsu ta zauna kallon Khairat kawai take,zuwa can tace.

“sweetheart wai kina lafiya kuwa?.”

Tana daga kwance bata ko d’ago ba tace,
“lafiyar kenan mekika gani.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button