ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

yaudai nayi rashin kunya,kunja kunyar ma hada ido nake daku????????????

Muhadu second to the last page ????laifin dadi kare wa

Mrs bb
Mom muhseen????????

[7/16, 12:20 PM] Mom Muhseen: ????????????????????????????
????
ABIN CIKIN RUHINA

Writing by mrs bb
Mom muhseen.

Wattpad name
Humaira7531.

DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.

           55.

Not edited (inkunga typing error kuyi hkr ina saurine)

Ban tashi ba sai kusan karfe sha biyu,banyi mamaki ba saboda jiya naji bacci idona sosai.
Wanka na shiga na fito ina shafa mai,ahankali inabin fata ta datayi wani irin fresh,don duk gyaran da akayiwa amare muma nida sweetheart dina sai da akai mana,shiyasa jikinmu gashinan kamar na jarirai,don wacce tayi aikin gwanace sosai annie ta daukota daga maiduguri.aikuwa munsha gyara don inajin shiyasa sha,awata kara karfi.
Nai mamakin abunda ke fita daga kasana jiya na manta ashe fa nasha kaya da yawa,murmushi nai ina tuno moment dinmu najiya,lumshe ido nai inajin wani irin farin ciki yana cika zuciyata.
Yanzu zan san nayi aure,yanzu zanji dadin dake cikin marking love………Allah sarki dr Allah yajikan ka yayi maka rahma,Allah baisa zamu yi rayuwa maitsayi ba,ina maka fatan samun rahmar ubangiji.
Shaf shaf na shirya don inje in gaida Abbu naji yace zaije unguwa yau.
Riga da siket ne cikin kayan bikin da ban gama sawa ba nasa.sai na ganni na canza sosai fuskata sai annuri take,dariya nayiwa kaina ina fesa turare nafito daga d’akin.
Saida na gaido Annie da sauran yan uwanta da zasu tai yau,sannan na wuce wajen Abbu muka gaisa yake jana wai harna yi kiba daga jiya zuwa yau,don jin nasamu abunda nakeso.
Gudowa nai saboda kunyar da yabani,mimi ce mukai karo tana goye da Airah.
Zaro ido nai ina kallon babynah “yaushe kikazo sweetie nayi kewarki wlh,zo taho ga mominki kima kinyi kewarta ko.”
Na sunbaci goshinta aikuwa ta hau b’angale dariya,duk ta kara man girma nagani ansar ta nai ina cewa”sweetie me ummi ke banka maki kikai wannan girman,wlh kinyi kyau muaaahhh.”
Dariya taitayi tana k’yalk’yalawa.mimi dai kallonmu take kafin tace”Amarya kinsha k’amshi to ya amarcin.”
Harara na banka mata ina wucewa b’angaren ummi biyoni tai tana dariya”daga ganinki ma wlh na samu ansata,kinga yadda kika yi jawur sai daukar ido kike dagani wlh kinsha madara jiya.”
Zaro dara daran idona nai in rufe bakina nace”innalillahi,mimi ubanwa ya koya maki iskanci,aikuwa kamar gaban ummi kikai saina gaya mata,shegiya marar kunya kuma zamu gauraya wlh nidai kika yaudara ko.”
Dariya kawai take tana rik’e ciki tasan ta hada rigima. jiya anyi kam tasan anyi shagali.
Koma wa tai tabarsu suka shiga b’angaren ummin.
Tana ta yiwa mai aikinta fad’a a kitchen suka sameta.tana ganinsu ta washe baki tana mik’o wa airah hannu amman ta mak’ale kafad’a
Ummi tace”kinga ja ira,au kishinne ya tashi tokuwa saidai ki mutu yarinya,mijina yafi karfinki.”tafada tana hararar Airah.
Me khairat zatai ba dariya ba,hartana dukawa tace”kai ummi,itafa ba haka taje nufi ba.”
Hararata tayi tace”gashinan tana mun kallon uku saura kwata,kice ba haka take nufi ba to wlh koma mekike nufi yarinya nan gani nan bari wlh.”
Dariya nake har da hawaye don wlh ummi taban dariya ganin zan yadda Airah yasa itama tayi dariyar tana ansheta daga hannuna.
Muka fito falonta ina gaidata ta ansa cikin walwalah ummi ta canza sosai,ferfesun yan shila ta kawo mun tace”maza cinyesu kishanye roman,karki tauna kashin don wlh wancen mayen idan bakiyi dagaske ba zakisha wuya,don naga rawar k’afarsa tayi yawa.”
Na shiga uku na kunya kamar ta kasheni sai soke kai nake k’asa,jinai ta dungure man kai tace”dallah can,wakike jima kunyar zan makeki wlh ja ira saki jiki kicinye ko sai na sab’a maki,kafin infito daki kin cinye shi.kekuma kishiyata zomuje d’aki badan halinki ba.”
Fita sukai suka barni ina cinsu,wlh babu dadin gaba balle na baya inaci ina ya mutsa fuska,daker na cinye su romon kuwa kasa shanye shi nayi duka na je kitchen na zubar na wanke kwanon.
Ficewa nai don wlh bazan iya had’a ido da itaba wajen maah naje,itama da nata abun nida salma tatusa gaba saida taga ina shirin amai ta kyaleni,wasu abubuwane taringa durka mana,can nabaro salma,don indan natsaya saina amayar da duk abunda naci.
Mimi kau yini tayi tana jana kamar zan mata kuka nace”plsss karki sake irin abunda kikai jiya wlh kadan yarage………plsss kibari kingani cikin gida muke shikuma ba kunya ce ta isheshi ba baijin komi nizai bari da soke kai kasa.”
Tana dariya tace”sorry my Anty nabari bazan sake ba.”
Airah yini tay wajen ummi saboda ta tusa mata kayan wasa da chocolate,saudaya tasha nono abunda ma nalura dashi nonon bai dameta ba yanzu,sai dai koko ko costand.
Karfe shidda Ameer yazo yasha gayunsa kamar dai sabon ango,sai zuba k’amshi yake dariya kamar ta kasheni saboda tsokanar ta danake,saida tayi kamar zatayi kuka nadaina har bakin mota muka rakota ta rungume maah tana hawaye.
Maah tace”mezangani haka salma,kema sabuwar amaryarce bason sakarci fah.”
Cikin kuka tace”maah wancen karon banyi kuka ba,saboda ina murnan zanbarku ina ganin kun takura rayuwata ne baku sona shiyasa,amman saidaga baya nagane cewar banda masoya kamarku,dangin mamana da suka ringa zigani aranar,tundaga sannan ban sake ganinsu ba,babu wanda ke daukar kirana idan nakirashi,amman ku nadawo gidan kun ansheni hannu biyu,babu nuna damuwa ko zagi balle hantara,banda bakin da zan iya gode maki maah,saidai zan dawwama ina maki adduar gamawa da duniya lafiya,ke uwace tagari mai tsayuwa kan lamarin kowa,kiyafe mun maah kiyafe mun kisaman Albarka wannan karon,don nasan hakkinkine yabini wancen lokacin naimaki alkawarin yin biyayya gareshi da kuma hakuri da zama gidana,don kuwa shine zaisaka ki farincki,kiyafe mun maah.”
Babu wanda bata ba tausayiba lokacin don nida mimi kuka muke taya ta ,ita kanta maah din hawayen take gogewa tace”haba salma aike diyata ce har abadan,kuma na tabbata nono na dakika sha baki zubarba,kawaidai wani lamarine na ubangiji dakuma kaddara,na yafe maki duniya da lahira salma Allah kuma yayi maki Albarka ya azurtaku da zuria dayyiba,kibi mijinki sauda kafa koi ya umurceki inhar bai sab’a ma sharia ba kiyi,sannan zuwa yanzu kinyi hankali kindauki darasi,saikisan wanda zakiyi qawance dashi.”
Tana goge kwallarta tace “maah nida qwa har abadan,y’an uwana gasunan sun isheni rayuwa wlh.”
Dariya taba mu itama tanayi sannan ta shiga motar yayiwa kowa bankwana sukatai muna daga masu hannu.
Sauna muguwar kewarta Allah sarki naka nakane koda kai mezai maka.

Haka gidan ya koma daga ni sai mimi dasu maah,saifa sweetie na Airah,wsan b’uya muka komayi nida yah Areef,danaji zaishigo zan boye duk yadda yaso ganina nahana don yadda nakejin canjin jikina wlh ya tab’ani akwai damuwa.hutuna ya kare na koma IT dina daman sati uku yarage man na zage bakin kokarina inayin duk abunda ya kamata,saidai yah yabini har can yaganni amman ba gida,wata irin soyayya yake man maisanyi mairaysa ruhi,ina tsananin kewarsa nikaina yadda nakejin kaina ina bukatar shi,don umi da Annie da maah kamar zsu kshine da kayan gyara,musamman annie ta ke kirana tana mun darasin kwanciyar aure,ranar data fara kamar zan nitse harta gama bance kala ba,kaina yana kasa tace mun dukkansu yan uwanki babu wacce ban mawanba,saike shiyasa naga yadace na ganar dake na nusar dake,don mahaifiyarki bazata iya ba,ita kuma ummi tace kunyar ta da kike ji bazata barki kigane ba,gara dai ni na maki,don haka ki kula kikuma yi aiki dashi don wlh Areef dole saida kulawa,ina lura dashi duk yafi sauran rawar kafa.”
Haka annie tazage tun inajin kunyar harta rage,wani zubin idan inada tambaya zan mata kuma taban ansa,zuwa lokacin nikaina amatse nake wlh daker nake bacci saboda d’an banzan feelings dake hanani bacci.
Hardai Allah yasa nakare IT dina muna exams din final lokacin ummin dr tace na yaye Airah tunda ma ba shan nonon take ba,da nayi gardama saboda inajin tausayin sweetie,amman da maah ta lallasheni ta kuma nuna man hakan shine daidai saina hakura na cireta,bayan kwana biyu ummin dr tazo ta tai da ita wajenta da kuka muka rabu kwana nai ina kukan rashin sweetie,Allah ya sani ina son Airah ban san ma ina sonta har haka ba saida akarabani da ita,ganin duk nashiga halin damuwa yasa ummin taki rani tace inyi hkr idan natare da sati biyu zata kawo mun ita.
Wannan bayanin yasani na samu natsuwa har nasaki jiki aka cigaba da yimun gyaran jiki,inka nni ak ganeni,saboda canzawar danayi mimi sai santi take wai kosu Anty shida ba aiwa wanan gatan ba saini,Annie tace “kinsan ai ita tadaban ce kema ki hanzarta dai Abukhalipa yadawo atsayar da lokaci wanda yafi wannan ma yimaki za,ai.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button