ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Don inna mahaifiyar Abbu tafara maganar ya kamata a aurar da su yah Areef hakanan,karsu tsohe agida……….nasan har yanzu ba agaya mata zancen shi da salma ba,sai nan gaba.
Nida yah Areef kamar mage da b’era dana hangoshi zan kama gudu,ko muryarsa najiyo zanfece wanan abun yana konama shi rai,haka Anni abun yana bata haushi…tayi man fad’an har ta gaji ta rabu dani,haka maah tayita lallashina tana cewa”haba my angel dina kidaina gudunshi yayankine badodo bane,kinsan hakan haushi yake bashi,idan ya waiwayoki tau babu ruwana,kisaki jiki dashi babu abunda zai maki.”
Wani zubin ina kuka zance”wallahi maah ko had’a ido mukai hararata yake,tsoran kallonsa nake bazan iya zama inda yake ba,kiyi hkr maah.”
Hardai Abbu Da da dady maah ta gaya mawa aman babu abunda ya canza.

Yau ban samu halin dawowa sex ba,kawai nayi zama na wajen husna har mukai lectures na 8 muka gama lokacin goma saura minty ashirin……duk tsoro ya kamani Abbu nakira nace ya turo driver ya d’aukeni……..”ta Alkairi ai hamza yatafi gida tun d’azu bari naturo maki yayanku.”
Ya kashe tunani nafara to wane yayan kenan,Allah yasa yah jahid ne, don nasan shikad yake zuwa d’aukana.
Hira muke da husna tana cewa ingaida mata yah shashid.
Dariya nayi nace”yarinya takamu da son the handsome din gidanmu,nama manta ai ingaya maki tun last week yakoma,saidai inbaki no dinsa.”
Murmushi tayi tace”uhm kawai dai tun randa naje maki yawo naji ya burgeni,jinina ya had’u danashi.”
“Don’t mind friend Zan had’a wannan kaunar insha Alah.”
Dariya sukai suna cigaba da hirar.
Abbu suna hira da Dady kairat ta kira yace,
“Bari naje na d’auko khairat,yaran nan nasan basu shigo gida ba..”

Dady yace”inhar kana son daidaita tsakanin yaran nan biyu Areef da khairat dole sai kana had’asu wuri guda,ma,ana kana kusanta su da juna misali kaga yanzu babu mai daukota to katura areef yaje ya taho da ita,kirashi awaya nasan zuwa yanzu yana kan hanyar isowa gida.”
Jinina kai Abbu yayi yace”shawara mai kyau.”

Wayarsa yaciro yafara kiranshi,
“Abbu gashinan na kusa isowa wallahi yau bak’i nayi daga canada.”
“OK ba damuwa Amman kabiya school dinsu khairat ka d’aukota babu driver yatafi gida.”

Jiyai jijiyoyin jikinsa sun tsinke,bazai iya musuba dole yace”to kawai.”

Mrs bb ce????????
[6/1, 10:22 AM] Anty Ushe: ????????????????????????????????
ABIN CIKIN RUHINA

Written by [Mrs bb]

Mom muhsen ce

________________________

????????AINUWA ????RITER’S✍????
????SSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

19&20.

Kwana yayi yanajin gabansa yana fad’uwa,lumshe ido yayi ya bud’e ya najin gajiya na bin duk kanin gab’anshi,shiyasa yake tafiyar a slow kamar maijin bacci,garin akwai duhun dare ga iska mai dadin shak’a da ratsa jiki,ga dukkan alamu ma hadarine don su weather su haka take,ayi sanyi ayi zafi wataran ma ruwa zakaga anwuni anayi…….get din makarantar yashiga duk sai y’an tsiraru ke yawo……muna bakin wani department na hango motar yah jahid,don duk tunanina shine saboda motar irid’a yace.
“Kinga husna labarin gay din nan bazai k’areba bari kiga ni ga yah jahid can yashigo.”
“Aikuwa sweetie daga nan zanjuya don idan nace rakaki zanyi toni babu mai rakoni,don wallahi tsoro ake badawa irin wannan time d’in.”

Sara mata nayi nace”bakida case sweetie,good night ayi mafarkin yah shahid.”
Dariya tayi tace”ok kekuma kiyi na Dr MK.”
Murmushi nayi najuya ina tafiya sauri sauri,don daga inda yake hangena nima nake hangenshi akwai d’an nisa babu laifi,hakanan naji kafafuna suna hard’ewa,jikina yacanza gab’a daya gabana yaringa fad’uwa………innalillahi wa inna ilaihir raju,un na anbata,saboda aduk sanda najini cikin wannan condition din to tabbas dodona nawajen,saboda tsabar tsoransa dana sawa raina jikina har ya saba muddin yana kusa da inda nake tunkan idanuwata suyi tozali dashi jikina zaifara rawa gabana yana faduwa…….jikina amace na isa bakin motar hannuna karkarwa yake,Allah yasani inajin tsoronsa fiye da kima,more excspcialy tsawarsa idan ya kwatsa man ita.
Murda kofar nake tak’i bud’uwa…….shikuwa kallonta kurun yake,kafin yaja k’aramin tsaki yabude mata da kanshi…..ina kerma nazura k’afata na dosana duwawuna na zauna dandanan naji idona yacika da ruwa,kuka keson kucceman bansan daliliba,kodan banson abunda zai kusantani dashi daidai da second banson mu had’u…..tada motar yayi yafice cikin sanyinsa kamar baison tukin,tafiya suke iska na kad’asu don glass d’in tagar wjena sauke yake k’asa,dama kuma sauken na ganshi.
yayyafi akafara iska yafara man yawa,amman banda halin cewa zan kulle rawar sanyi nake tunda amotar ma AC ya kunna kuma k’arshe take…….jinai yadakan tsawar danake tsoron karyamun har muje gida……….”ubanwa yace kisauke man glass,zaki maidashi kosai naci ubanki,stupid girl.”
Hannu na yana karma nasaka namaida hawaye suka wankemun fuska,inasharewa karyaga ina kuka nan ma wata masifarce……ina gogewa wasuna zubowa.”zanci ubaki wallahi kukan ubanme kikeman dukanki nayi,ko yankar naman jikinki nake,ohhh ga mala,ika aza,ilunki ko dake nake kinaman banza.”
Yafad’a cikin tsawa…..daidai sanda aka shek’e da ruwa dama kuma muna gaf da gida.
Bansan sanda wani kukan ya kucceman ba,dukewa nai nasa kaina cikin cinya naita rera abuna…….kuka nake sosai mai cin zuciya……banza yayi mun har muka iso gidan,nibanma saniba najidai ya tsaya ban d’agoba kukan kirun nakeyi………fita yayi ruwan yafara dukanshi ya lumshe idonshi,yanajin dadinshi kamar yaita tsayuwa cikinshi har ya kare……zagayowa yayi ina nake zaune yabude k’ofar jinai kurun ya kamo hannuna nafito,rufe motar yayi yajani muna nufar cikin gida…….hannunsa cikin nawa ga ruwa yana sauka kanmu har lokacin kuka nake amman can k’asan makoshi,saboda muryar kanta ta dishe…….idona rufe yake nasa hannuna da abayata na rufe fuskata,shike yiman jagora wannan halin damuke naji tsikar jikina tayashi yarrrrr……. Sanda mukaje wajen hawan step din shiga main falon……jinai kirun an sab’eni baidirnine ko inaba sai d’akin yah meenah……idonta biyu lokacin kallonmu tayi tace”yah me yasameta”
Direni yayi kan gado yace”gatanan ki tambayeta” yafice tashi nayi nai jifa da abayata dake k’amshin turarenshi,har lokacin kuka nake sosai jin har lokacin mayataccen k’amshin baibair jikina ba yasa nahau cire doguwar rigar jiina ina cewa,
“Tsinanne wallahi sai kabar jikina,tunda banan aka haliccekaba…….ga hawaye share share…..yah meenah kallona kurun take,ganin nacire kayan ma bandaina jinshiba yasa nashiga wanka…..naita dirjar jikina saida nagaj nafito…….dariya kurun yaya meenah kemun babu sassautawa,haushinta ya kamani shiysa har nayi bacci ban tanka mata ba.

     ************

Koda yaje d’aki takalmanshi kurun yacire ya zube ga kujerar falon su,kanshi sama idonshi kulle,iskar bakinshi kurun yake fesarwa,kasancewar wannan dabi,arshi ce idan yana cikin halin damuwa.
Jahid daya fito wanka ya samai awannan hali,sai bai kulashi ba,don yasan halin kayanshi har yagama shirinsa Areef nanan inda yake,karshe sallah kurun yayai yazo ya kwanta kan kujearat,daya tashi…….jahid kallonsa kurun yake don wannan ba sabon abubane wakenshi,saidai nayau yasha banban dana sauran lokutan,don Areef baya kwanciya da kayan jikinshi,duk runtsi zai canza kaya amman yau gashi ya kwanta dasu,bama manya bane masu sauk’in bacci jeans ne da t shet jikinsa,da wannan mamakin yayi bacci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button