ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

17.

Salma ce da k’awarta raihana suketa kwasar dariya cikin d’akin,har basujin sallamar da nake…….abayar na cire ina cewa,
“Sai Ihu kuke har ba ma kujin sallama ko.”

Wani kallo naga raiha nayi mun kafin ta sake kwashewa da dariya,salma na taya ta binsu nayi da kallo tsayin lokaci kafin na shige toilet,don na lura wanan dariyar dani suke kuma babu tantama salma labarin abunda yake faruwa ta bata,nasan kuma wannan labarin kaf k’awayenta ta basu shi……..wani takaici ya kamani har naji k’wallah ta taru idona……..sharewa nayi nayi wanka na tare da alwallah nafito har lokacin hirar su suke ta samari,wani zubin sai su yab’oma gana wanda daji dani suke,ban sake kula suba na hau yin sallata nagama nafara shafa mai inaji raihana nacewa,
“Saiki kula kinsan ana iyayin komi don aga anrabaki dashi,don kinsan y’anmatan yanzu sun b’aci da bin maza kina zaune da saurayinki lafiya saidai kiji wuf anfige,kinsan ma wani abun haushin wallahi nakusa dakai shine zaki samai da wannan hali,kidai kula wallahi.”

Kad’an ya hana ban tankaba,saboda maganar takai mani mak’ura don har zuciyata wani irin ciwo take,haka suka cigaba da hirarsu turarena nashafa duk jikina,sanan na saka kayan doguwar rigace marar nauyi ina gama wa ana kiran isha,i sai kawai na tada sallah sai lokacin tayi niyyar tafiya…….fita sukai naci gaba da salla ta ban fito ba sai wajen takwas,d’akin maah na shiga na sameta suna waya da ummin Dubai……..zama nayi gefe injiran su gama har nafara bacci sannan naji tana gyaraman kwanciya,tashi nayi ina mik’a tare da hamma,hannu tasa tarufe mani baki”akwai gajiya ko,gashi da ganin wannan cikin baici abinci ba”

“Nayi missing d’inki duk yau maah,wlh school akwai wuya amman fa lectures akwai dad’i maah.”

Murmushi tayi tana shafa kaina tace”oh my angel kibar dai cika baki kwanan nan za kifara mana kukan kingaji.”

Shagwab’e fuska nayi ina sake narke mata nace”maah kinga dai salma ko.”

Maido hankalinta tayi kaina tana sha fa kaina tace”mekuma tayi maki dear.”

Na gaya Mata abun da ya faru d’azu……….shiru tayi na d’an lokaci kafin tace”my angel karki biyeta,bake ba harni nan salma ta canza mani daga halin dana d’orata akai,tabbas akwai abunda yake faruwa,fatana kici gaba dayin hakurin dana sanki dashi,karki ga don na hana Aurenki da yayanku kiga kamar ban sonki,aa my angel ilove u more than expected,haka kuma ina duba abunda yadace daku ne,inason har bayan raina Areef ya kasance yayanku mai share maku kukan ku,koda aure kukai kunada babban yaya da zai kula da lamarinku………kid’auka dama babu aure tsakaninku kinji ko angel d’ina…….karki saka damuwar komi cikin ranki Allah zai kawo maki miji nagari na nuna ma sa,a sannan kiyi kokari ki nuna ma Abbunku cewar komi ya wuce wajenki hakan zai saka ya daina fushi dani,ko kinason yayita fushi dani.”

“Bana so maah insha Allah zan bashi hkr yadaina fushi dake,aman maah kija ma salma kunne wallahi kar wataran takaini k’arshe,ni wallahi maah tun daga randa akai abun nan nituni na yafe shi cikin zuciyata,to akan me zata ringa yayatani cikin friends d’inta………wannan cin mutuncine…….sallamarsa tasaka nayi shiru ina kwance har lokacin kan cinyar maah tana shafa kaina………..idasa shigowa yayi yazauna gefen da nake……..yadda ya canza fuskarshi daga shigowar sa yasa ni tashi daga kan cinyar maah,kallon k’asan ido yake mun bansan fassarar da zanba kallonba………gyara kallabina nayi har lokacin idonsa na kaina nace batare dana sake kallon inda yake ba.
“Maah bari naje Wajen abbu inci abinci dama wajenshi zanje na biyo in gaidaki.”

Kallon Areef tayi ta b’allamai harara tace”haba my angel daga shigowar yayanki zaki ruga.”
Ina nu far k’ofa nace”Aa maah dama yanzu zan tashi idan ya tafi anjima mun ida maganar,saida safe.”
Nafice inajin dukan da gabana keyi yana sassauta,don yanzu wani irin tsoransa nakeji har cikin k’ok’on raina…..wajen Abbu naje nayi sa,ar kuwa lokacin yake cin Abinci…….zama nayi nasaka hannuna kamar yadda yasa nashi,kasancewar Abbu baya cin tuwo da spoon muna hira muna ci har muka gama,nan yake gaya man yah shahid ranar monday zaidawo Anty shida kuma sai Tuesday zata zo weekend……..naji dad’i sosai don nayi kewarsu sosai…..nasiha yashiga yimun cikin hikima da jan hankali har yazo kan batun shekaranjiya……cikin tattausan lafazi yace”ta alkairi kinsan cewar duk abuna kaga baka samu ba da hakan ba alkairi bane,don haka kid’auka cewa yayanku dama ba mijinki bane,kiyi hkr insha Allah mijinki zaizo nagari mai nagarta,fatana kisaka tawakkali da hakuri kinjiko inhar kinada damuwa kisanar dani karkice kibar abun ga zuciyarki,don zai illataki karkiji komi ta alkairi na komi kikeso sanar da Abbunki inhar ina dashi zan maki.”

Godiya nayi mashi tare da yi mashi alkawarin cire damuwar,sannan nace yajawa salma kunne akan abunda takeyi,na gaya mashi abunda ya faru don gudun abunda zaije yadawo…….shima ransa ya b’aci yace inbarshi da ita,har zan mashi maganar zaman hostel su yah jahid suka shigo shida dodona don yanzu sunan dana rad’a mashi kenan cikin zuciyata……tashi nayi nayiwa Abbu saida safe,don banson abunda zai ringa had’amu waje guda.

Mrs bb ce????????[6/1, 10:22 AM] Anty Ushe: ????????????????????????????????
ABIN CIKIN RUHINA

Written by [Mrs bb]

Mom muhsen ce

________________________

????????AINUWA ????RITER’S✍????
????SSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

18.

Har nakai k’ofa Abba yace”ta Alkairi zonan.”
Kamar in zura aguje haka naji…….Amman babu damar hakan,kamar wadda kwai ya fashewa aciki haka nake tafiyar,inda na tashi na koma ina jin bugun kirjina yana sake yawa,don har ga Allah atsorace nake gani nake kamar zai kawo man duka………
“Kamar kina son fad’an wani abu ko.”
Yak’e nayi nace”aa Abbu babu komi.”
“Banson gardama kinsani don haka menene.”
Lagab’ar dakai nai kamar zanyi kuka nace”Abbu sonake na koma hostel da zama,idan ina can sai nafiyin karatun sosai,nan gida wani zubin inason yi wani abun zai d’auke man hankali.”
Kafinma Abbun yabani ansa yayi zak’al yace”Abbu babu wani hostel da zata zauna,duk salon ta biyewa abokan banza aringa yawo ga gari,idan ma na sake jin kin anbaci zaman hostel saina tattakaki,tashi kibamu waje.”
Kuka nafita inayi saboda haushin abunda yace………yauma wajen yah meenah nakwana,mun raba dare kowa na bin abunda akamana jiya,nice searching ga computer banyi baci ba sai daya da rabi nayi bacci..yah meenah ta rigank kwanciya…………

     ********

Rayuwar ta mik’a taci gaba da kasancewa yayinda karatunmu yake tafiya successfully,duk da irin yadda lectures suke zafi hakan bai hana ni jin dadin suba,agajiye lik’is muke dawowa don yah meenah tana rigana,su sunyi gudun duniya sukai 4:35 pm mukau 6:oo pm wani zubinma idan abunyayi zafi har lectures din 8:oo to 9:30 muke……..kuma haka zan dawo gida sex in yi wanka da sallar magaruba inci abinci sannan in koma,duk wannan wuyar yah baijin tausayina na zaun hostel,shiyasa gashinan duk na rame cikin abunda bai gaza 2 to 3 weeks ba…….suma yanzu ba zaune suke ba kasancewar sun samu aiki yah jahid dama engineering yayi to yanzu b’angaren yake aiki,cikin wata guda sun sake komawa wasu handsome gays……duk wanda ya gansu yasan suna kwanta kudi Yah Aareef kuma Act ya yi zane zanen gidaje da sauransu……….tsakanin sa da salma kuwa bazance komi ba,don wata irin kulawa sukewa juna,itace abincin safenshi idan zaitai ofis itace lunch nashi itace dinner,gyaran b’angarensu ko karatunta bata bawa muhimmanci ba kamar yadda take kaffa kaffa da duk abunda ya shafeshi,zuwa yanzu babu laifi ni da ita muna magana tunda Abbu ya kirata gani gata yayi mana nasiha da fad’a,har hira munayi babu laifi Amman ba kamar da ba,sosai suke buga soyayyarsu yah shahid yazo hutu satinsi biyu yakoma don sun kusa kammalawa…….Anty shida ma tazo kwananta biyar ta koma zuwanta na fahimci wani abu,akwai boyayyar alka itada yah jahid….nadai yi shiru don nasan basu son asani sai nan gaba,bai wuce kuma kammala karatunta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button