ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Munanan zaune tsawon lokaci banda shashshekar kuka bana yin komi wata irin kewar yan gianuce akejin tana kamani,sonake yayiman magana yakiya,yaki motsawa yaki kallona,yaki zuwa inda nake kowa yana furta albarkacin bakinsa akan aurena,Amman shi ko tanke baice komiba,hankalina bai sake tashiba saida naga ana jana za a fitar daga cikin gidan…….kua nake ina rike Maah da Annie amman babu mai saurarena,Abbu dakanshi ya kamani yasa motar,sanan yashiga gaba dady shike tukamu,sauran motocin suka rufa mana baya…….inaji ina gani nabar gidanmu zanfada wata duniyar daban,bansan kuma wace rayuwar zanyiba……..lallashina kirun Abbu keyi har muka isa,baibari nasaka kafata ba saida nayi addua sosai,har yana aranto man ina ansawa sannan adagaafatta dama asakatare BISMILLAH.

Mrs bb ce????????????????????????????????ina Alfahari daku
[6/16, 11:11 AM] Mom Muhseen: ????????????????????????????
????
ABIN CIKIN RUHINA

Writing by mrs bb
Mom muhseen.

Wattpad name
Humaira7531.

DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.

I need ur prayers Am not feeling fine.

Not edited.

             33.

Iyayena maza sune suka kawoni har cikin gidan mijina,nayi kuka kuka mai sunan kuka har jinake kaina zai rabe gida biyu,dandanan zazzabi ya rufeni ruf rawar sanyi kurun nake su yah meenah da suka shigo motocin Abokan ango duk sun rude da halin dana ke ciki,don jikina har wani siraci yake fitarwa…….hakika ban taba dauka haka ake jin dacin rabuwa da iyaye ba in aure ya tashi,lallai ajinjina ma Aure.

Anty shidah bata kwana ba yah jahid ne yazo ya dauke ta,Husna dai nan zamu kwana da ita da yah meenah………sauran kawayen mu duk sun tafi gida suna cewa sai sun dawo gobe walima.

Ganin jikin nawa yayi tsanani yasa suka kira dr suka sanar dashi,aikuwa sai gashi kamar daga sama duk yarude…….waya ya ciro ya shiga kiran dr su ganin dr baima ganin su yah meenah rungumeni yayi abunsa babu abunda ya damai,dole suka bar dakin suka koma daya daga cikin bedroom dina,don babu karya iyayena sunyi matukar komari,Abbu gado biyu duk yayi mana da set din kujeru biyu,amman ni maah da annie da ummi suka hadu suka kara man kala guda,duk da halin da nake ciki hakan bai hana ni ganin kyan bedroom din da nake ciki ba.
Komi maroom dakin sai walwalin fitilu yake,gadon kanshi cycle ne kuma juya wa yake,kana iya tsayar dashi kana iya barinsa.
Abun gwanin burgewa da ban sha,awa.

Ina jikinsa nayi lamo sai ajiyar xuciya nake,kaina kurin yake shafawa yana jeraman sannu,tuni dama ya rabani da gyalena…….saida likita zai shigo ya rufa man shi.

Dubani yayi sosai yace”damuwa ce da kukan da tasha suka sakar mata wannan zazzabin,da tasha pen relief zai sauka kuma tayi kokarin cire damuwa insha Komi zaizama successful.”

Godiya yayi mashi ya tafi kwance nake na kudun dune wuri guda,na lumshe idona ina jin kamshinsa kusa dani.

Waya yake idonsa akaina don inajin su suna sakani takurewa.

“Ummi jalila ta hado abinci maidan saukin ci sai taci kafin a kawo na sauran,eh ummi to insha Allah, jikin ai da sauki gata nan oky to.”

Ajiye wayar ya yayi yana tab’a goshina……..ajiyar zuciya nai yace,
“Sorry my dear tashi ga abinci nan sai kici kisha magani,bazan so wannan ciwonba muna tsaka da farinciki,kokin manta yau wace rana ce bari na tuna maki,yau ranace ta farin ciki agaremu da duk masoyan mu baki daya,burin mu ne ya cika na mallakar juna Allah ne ya nuna mana don haka plss my love,ki tashi mu fuskanci sabuwar rayuwa.”

Sake lafewa nai cikin gadon mai dauke da wata irin katifa mai laushin tsiya.
Kofar aka bude aka shigo tare da sallama,

“Wayyo Antinmu kina nufin wannan dinner ba za,ayitaba gaskiya kitashi ki wartsake gidan masoyinki fa aka kawoki……….muryarsa cike da annashuwa yace”Jalila kin raina niko.”
Tashi nai ina gyara kallabina dana rufa ma kaina shi,kokarin sakin fuskata nai nace mata.

“Inayini.”
Dariya tayi tace”lafiya Anti tunda kinbarmun girman.”
Harararta yayi yaceman
“Karki sake gaidata inba haka ba rainaki zatai,kanwarki ce itace zata ringa gaidaki.”

Murmushi nake bance komi ba,
Tace”ga Abinci nan Anty amarya aci awartsake mutai party.”

“Jalila babu wani party da za,ai matata bata lafiya kibari inkingama ruwan idon zaben saurayi inbikinku yazo saikuyi koma miye ko love dina.”

Wayyo kunya kamar tasan yadda zatai dani,
Sunkuyar da kai nai ina wasa da gefen kallabina.
Dariya tayi tace”ashe kuwa zaki sha kunya don bakiga komiba wajen Dr sai ya rungumeki gaban ummi.”
Zaro ido nai ina kallonta mezasuyi ba dariya ba har suka bani dariyar nima.
Mikewa tayi tace”nayi nan amarya Allah yabada lafiya,ummi na miki sannu.”

Muryata tayi wani irin sanyi sosai nace,
“Nagode kice mata ina ansawa sosai.”

Kallona kurun yake duk naji na takure shagwabe fuska nai nace”plss d……..jin lips dinsa kurun nai kan bakina……..daskare wa nai kamar nayi kankara saida ya tsotsa iyakar yinsa sannan ya dago yana kallona,
Murmushi yayi yace”Aina gaya maki duk randa kika sake ceman wani dr ko sir saina cinye baki,to yanzu ma arzikinki daya baki daafiya da kinsha mamakina tunda bakijin magana.”

Juya mashi baya nai kamar zan kuka saboda wallahi rashin kunyar dr tayi yawa,
“Nidai kadaina bana so.”

“OK naji wannan juyo maza nabaki inada baki nabarosu ban sallamesuba.,”

Yada yayi alamun babu wasa dole yasa na juyo yana bani yana man hira,yana gaya man irin mutanen da suka halarci bikinmu………ashe daman yunwar nakeji sosai don kwana biyu bana cin komi sai dan abu me ruwa,saida yaga ina shirin sheka mashi amai yasa ya kyaleni………ya sunbaci goshina yace,
“Sai da safe ko in dawo mukwanta tare.”

Jifarsa nai da filo ya cab’e yana dariya yace”ohodai duk wayon amarya sai ansha manta,kishirya gobe anagama walima zanfara kora don nan gidan zanyi magrib.”

Dalalo ido nai baki bude dariya ya kwashe da ita yafice bayan ya jehoman filon.

Komawa nai jagwaf kan gadon,ina ajiyar zuciya tunda nake ba,a tab’aman kiss ba sai yau har yanzu jinake kamar bakin nasa yana kan nawa,numfashi na sauke ina jinjina soyayyar dr,ya iya tafiyar da ita yadda ya kamata………tashi nai na gama kalle bedroom din sannan nafito na shiga wanda su husna suke ciki ita da yah meenah.

Hira suke konace kowace hira take awaya da masoyinta,don yah meenah tuni tayi nisa wajen kaunar yah imran,love kurun suke bugawa mimi ce keta chat tana ganina tarungumeni.

“Allah sarki Amaryarmu sannu kinjiko yajikin,yayi sauki.”
Murmushi nayi nace”nasha magani na samu sauki,kunci abinci kuwa.”

Tace”yanzu muka dawo daga cikin gidan,munci mun koshi wallahi khairat kinyi dacen dangin miji kowa maganarki yake,yana yabon halinki ki zauna dasu lafiya kinga wai yadda sukaita hidima damu,abincin nan nama yafishi yawa ferfesun naman kai,gasassun kaji,yan ciki soyayyen naman rago sai wanda mutun yaga damar ci…….mahaifiyarshi tana ta tambayar jikin naki.”

Wata natsuwa ke shigata “tabbas ina fatan hakan ya dore,Allah ya kawar da shedan tsakanin mu nidasu.”

Tace “ameen muje na rakaki kiga gidanki khairat,wallahi su Abbu sunyi kokari sai fatan Allahb yabiya su.”
Tare muka fita dayan bedroom din dake tsakiya muka shiga,Italian bed ne golding color komi golding har fentin kanshi,sai daukar ido yake don yama fi wanda aka saukeni ciki,wanda su Husna keciki kuma komi purple ne da dark pink………palona biyune babba da karami babban set biyu na royel chairs aka saman,karamin kuma wasu kujerune yan gaske har wani malatsi garesu inzaka zauna zaka danna,wanda zai bakujerar wani irin sanyi ni,ima har haske suke fiddawa da daddare…….saboda farinciki har kuka nai ina gode wa iyayena.
wani abun mamakin shine wadannan kujerun wai yah Areef ya siya man su cewar mimi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button