ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

“me ye matsalar swee…….Khairat.”

Tabbas da sweetheart yazo fad’a sai ya fasa, tunda mukai wayau ban tab’a jin Inda yace Khairat ba, saidai sweetheart shine yau ya canza don yana jin haushina.

Salma tana kwalla tace,
“wallahi yah Aree ban sani ba, ni ma nayi nayi da ita ta sanar da ni anfi Wata Anma tak’iya,don Allah Yah kayi hakuri karka daketa.”

goge mata kwallah yayi yace,
“idan ta sanar da ni abunda yasa ta fad’i exams zan mata hakurin Idan kuma har ta saka taurin kai irin na d’azu Kinga wannan,ya nuna dorina sabuwa mik’ak’k’a, to da ita zan Zaneta.”

Hankalin ta ya tashi don tana masifar tsoran dukan dorina, haka bata son duki sweetheart dinta.

“ina jinki meye dalilin fad’uwarki jarabawa.”

Shiru nayi masa don nayiwa zuciyata Alkawarin ko zai kashe ni bazan fad’a bah, kukana nakeyi silently ina zubar kwallah…….saida yamun tambaya sau uku bance komi ba.
Yace salma ta tashi tatafi don bazai iya dukana gabanta ba, zata Karya masa zuciya.

Tana kuka tatafi takaice dai taurin kaina ya kaishi bango yayi mun dukan da na kasa motsi, ga masassara kamar ta kasheni saida Yah shahid yazo ya kwaceni,wannan dalilin shine babban dalilin da ya saka na janyewa yah Areef, kwana nayi banyi bacci bah wanda salma ma haka tayi,amai kawai nake Shek’awa har na galabaita,nace kuma karta kira kowa haka muka ga wannan daren, ganin abun zai wuce tunani yasa ta fita Aguje taje ta sanar ma da Maah, lokacin karfe shidda na safe Abbu Ya ma tafi waje aiki.

Haka Maah suka zo suka saman ban iya ko motsa d’an yatsana……Ai yah Aree kamar zai haukace suka kwasheni sai asibiti,duk tashin hankalin da suke ciki basu Kai yah Aree ba, don afirgice duk yafita natsuwar sa……..Anni ce ke kwantar masa da hankali har aka gama bani agajin gaggawa.

Mom muhsen ce
Mrs bb????????
[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: ????????????????????????????????
ABIN CIKIN RUHINA

Written by [Mrs bb]

Mom muhsen ce

________________________

????????AINUWA ????RITER’S✍????
????SSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

5.

Hana kowa shiga akai har sai nafarka daga baccin dasu kai Mani Allurarsa.

Anni aka bari wajena da Anty shahida sauran yah mujahid yakoma dasu,salma hada kukan ta bazata tafi ba saida Yah Aree yayi mata jan ido sannan.
Shima d’in bai tafin ba zamanshi yayi duk yadda Anni ke fama dashi yak’iya,dole ta kyaleshi haka sukai ta zaman zuru har ten thirty,sannan nurse din ta lek’o tace shishiga na tashi,Amman wani Cikin su yaje doctor nason ganinsa.

Areef ya tafi Anni da Anty shahida suka shiga,

Gaisawa sukai da likitan sannan ya zauna,
Bayani yayi mashi akan abunda ke damunta.
“cewa damuwa ce ta sakar mata masassara sannan da alama ma andoketa ne hada wannan dalilin yasa fever d’in tayi zafi, sannan dole akula da cin abincinta don bata cin abinci sosai,idan ba haka ba ciwon ulcer zai iya kamata, ga magani kasiya can phamercy.”

Godiya yayi mashi sannan ya fito yaje yasiyo maganin ya jiyo zuwa d’akin da aka kwantar da ita,jiya ke kamar ya kama dukan kanshi haushin kansa yakeji sosai akan abunda yayi wa sweetheart d’insa, tsoro yake kar tayi dogon fushi da shi, don yasan halinta akan rik’o…….sallama yayi Yashiga Ya ajiye magungunan gefe ya kalli Anni,

“lafiya dai ko Anni.”

“da sauk’i dai tunda muka shigo ta k’iyiwa kowa magana, sai kuka da take duk lallashin munyi Amman taki yin shiru.”

Kallona yayi nayi saurin kawar da idona, Ina shashshekar kuka k’asa_k’asa yana son lallashin ta Amman Idan ya yiwa Khairat saku saku babu tantama raini zai shiga tsakanin su, so yake ya koya mata tsoransa wanda nan gaba baza ringa yi masa taurin kai bah,ya nason bata hakuri dukan jiya da yayi mata, Amman ya girmansa zai kasance a wajenta ba makawa raina shi zatai, Wanda shi bazai so haka ba zai nuna yama manta da abunda ya faru, Shan mur yayi wanda dole idan ta ganshi haka tashiga fargaba…… Cikin dakakkar murya yace,

“jiyo nan nace.”

Jiyowar tayi gabanta na fad’uwa yace,
“goge wannan kwallar banzai, me akai maki yanzu da zaki kama yiwa mutane kuka, kin ma gaidasu tukun koko islanci ya hanaki.”

Bani kad’ai ba su kansu sunsha mamakin Areef d’in,don basu tab’a ganin yayi mana irin wannan kakkausan lafazin, sab’anin y’an kwanakin baya ko fad’a zai mana cikin taushin murya da lallashi yake yi mana, baison ma wani yaji idan kuwa d’ayan mu tana kuka kamar ya taya ta saboda baya son kukanmu,amman yau shine ke d’aga mani murya yana kwatsata dole kowa yayi mamaki katseni yayi da cewa.

“maza ki goge wannan kwallar ki gaidasu Idan kuma na dawo baki saki jikinki kamar da ba nida ke ne.”

Ya maido dubansa ga Anni yace,
“Anni bari naje na kawo maku abun break, zo muje shidah.”
sunan da shikad’ai yake ce mata kenan.

Fita sukai suka barni da Anni, matsowa tayi jikin gadon da nake ta rik’o hannun da aka cire mani drip, tana kallona kallon da ban tab’a ganin Anni tayi Mani shiba jinai tace mun.

“y’ar gidan Anni yajikin naki.”

idona ya ciko da kwalla nace,
“Anni Ina kwana.”

Murmushi tayi tace,
“lafiya lau yajikin naki.”

“da sauk’i Anni saidai inda yah ya dokeni jiya Anni ciwo yake mun ko zaki gasa mun.”

tausayi ta bata Amman ta danne bata nuna hakan sosai bah tace,
“Ayya sannu kinji bari Antynku ta kawo ruwan zafi sai agasa maki.”

“nagode Anni nah ke kad’ai ke sona ko.”

Murmushi tayi mata tace,
“Aa y’ar gidan Anni kowa yana sonki, meyasa kikace haka. “

“Anni yah Aree baya kaunata yafison salma akaina.”

Gabanta ya fad’i meke faruwa haka, Khairat yarinyar da bazata Gaza shekara 13 ba tasan kishi, danne fargabanta tayi tace,
“Haba y’ar gidan Anni Waye yace maki haka, aduk cikinmu in banda Abbu da Maah babu mai son farincikin ku sama da Areef.”

Hawaye suka zubo mani nace,
“no Anni wallahi yah baya sonah jiya naga haka yau ma naga haka, nidai daga yau babu ni babushi, Anni kinsan abunda yasa na fad’i jarabawa ta.”

Tana kuka take maganar hawaye share_share ga fuskarta,Anni gabanta banda duka babu abunda yake, sunan Allah kurun take anbata,don wannan lamarin na Khairat to saidai akira sunan Allah kurun.

sake danne yanayin da take ciki tayi tana yak’e tace,
“Ina jinki y’ar gidan Anni,meyasa kika fad’i exam dinki har kika bari aKai maki repiting.”

Wani kukan ta rushe dashi saida tayi iyakar Inda take so sannan tace,
“Anni don Allah karki gaya ma kowa kinjiko idan yah yasani sake dukana zaiyyi.”

Ai Anni jitake kamar ta zura Aguje,
(???????????????? yo baki bari Kiji komiye tun yanzu har kin shiga rud’u.)

“Namaki Alkawarin babu Wanda Zaiji wannan maganar sanar da ni kinjiko.”

share hawayena nayi nace,
“Anni tun daga ranar da Abbu yace su Yah zasu tai wata k’asa karatu nashiga cikin bak’in ciki, kullum saidai na b’oye toilet nayi ta kuka, ko idan naje makaranta inyi, har Cikin dare yi nake Anni saboda banson ya tafi, gashi maah tace idan suka tafi sai sunyo shekara shidda ko bakwai zasu dawo, Anni banson yah yayi mun nisa inaji kamar inbishi ko ince karya tafi, Anni kinsan abunda yake bani tsoro har yasa naki sanar da kowa.”

Anni tayi Wata irin zufah duk AC din dake sambad’owa ad’akin kuwa, daker ta had’iye wani kakkauran miyau amak’oshin ta tace,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button