ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

           53.

“Ameer ne mijin salma,yakai sati biyu na zarya gidan nan yana son ganina nace kar abarshi ya shigo gidan koda wasa,don inason yadda ya wahalar mun da diya shima saina wahalar dashi.”
Dariya maah tayi ita dasu Annie,don wani sanyi taji cikin ranta alamun dai asirin ya karye,cikin jin dadi maah tace ma salma.
“To abar kukan b’oye ga shinan yaxo biko da ban hkr.”
Dariya duka asa mata taita sunne kai tana dariya tace”nifa maah banayin kuka Allah kuwa.”
Murmushi kurun tayi don tasha kamata tana kukan,kuma bai wuce na rashin zuwan mijin nata.

Sallama yayi bakin kofa cikin ladabi da biyayya duk ya rame ya lalace,yama canza kamanni gabaki daya,bakin k’ofar ya zauna yana gaida su Abbu da su dady cikin lumana.
Dadyn yah meenah yace”iso ciki mana Ameer shigo kaima ai d’an gidane.”
Shigowa yayi yana satar kallon wajen da salma take,ita kuwa boyewa tayi bayan khairat tana jan tsaki kasa kasa.
Dariya nai mata nace”keda habibinki sweetheart,kidan kashe mai ido mana.”
Duka ta kaimun ina dariya tace”banson wulakanci wlh,ki kyaleni sai ya gane kurensa.”

Abbune ya fara magana da cewa”Alhamdulillah ala kulli hali,godiya ta tabbata ga Allah mai daukakin sarki daya daidaita mana al,amurranmu,hakika ance komi yayi zafi maganinsa Allah,kuma in akai hkr komi mai wucewa ne,yaudai Allah ya tabbatar mana da ganin dukkaninku ya mallakin hankalinsa,ya zama babban mutun domin yanzu kowane zai je yazauna da abokin rayuwarsa,abunda nakeson nusar daku shine hakuri da rayuwa,duk wanda Allah ya hadaka dashi kayi hkrin zama dashi,domin hakuri shine maganin zaman duniya,kowa yayi hkr da abokin rayuwarsa.
Sannan magana ta gaba itace kan Areef da khairat.”
Ummi ya kallai zai magana tai saurin cewa”Aa Abbun khairat,karkace komi don Allah wlh nasan duk abunda yafaru ban kyautaba,nayi danasani kuma insha Allah hakan bazai sake faruwaba,Areef na kairat ne haka kuma khairat ta Areef ce,ban isa in rabasu ba,domin Allah ne yaha da wannan kaunar inhar wani yayi kokarin shiga tsakani zaiga badaidai ba,ubangiji yabarsu tare ya kawar da shaidan,ina sake ba y’aruwata hkf abisa abunda yafaru,kiyi hkr saudah kiyafe man nayi kuskure.”
Girgiza kai maah tayi tace”komi ya wuce yaya,Allah ya yafe mana gaba d’aya.”
Dadyn su mimi yace”Alhandulillah angode Allah,daman koda hakan bata faruba mu munriga mun yanke hukunci tun ranar daurin aure,don aranar ba tashi taron daurin aureba saida aka daura nasu,munyi shirune don ganin yadda zaku sasanta kanku,to Alhamdulillah komi yayi kyau sai fatan Allah ya dawwamar da farinciki cikin wannan family.”.kowa yace ameen amman ni nakasa don bakina nauyi yayi,duk najini wani iri,nice yau nazama matar yah Areef,abun yazo mun abazata kasa kallon kowa nayi,salma sai tsinkuloni take tana mun dariyar mugunta,da tsokana”Amarya yar shagali,hankali ya kwanta yaudai buri ya cika sai ayiwa Allah godiya.”
Bugeta nai bance komiba Abbu yace”sai maganar salma da Amer,gashinan yana jinmu,kozaka gaya mana dalilin dayasa ka korota,sannan aka aika kiranka kace bazaka zoba.”
Hawaye yake zubarwa ya tank’washe k’afa yace”Abbu don girman Allah kayi hkr,wlh banson nayi ba,Abbu ban cikin hayyacina hakika sakaci da ibada dakuma wasa da lokacin sallah yasa duk abunda yafaru dani ya faru,domin raihana qawar salma tayi anfani da qawancen dake tsakaninsu ta wargaza zamanmu,itace tasaka man magani cikin abinci na naci tundaga sannan ban sake ganin salma da kimaba,banson ma ganinta ko muryarta naji jinake kamar nayita dukanta,raihana kurin nake gani da mutunci,har iyayena ban ragawa ba,nasha zaginsu idan suka gaya man abunda baimun ba…….wlh Abbu raihana azzalumar macece shu,uma tarabani da komi har gidana tayi anshe,saboda tayi anfani da damar ta ta anshe tardun gida har hannu nasa mata,yanzu haka wajen aikina sun koran,saboda wasu kudi data sani na sato mata……..kuka yake sosai kamar karamin yaro,wlh Abbu banyi da niyyaba bansan inayiba,saida asirinta yatonu,kwatsam saiga qawarta tazo rannan suna hirar,tana gaya mta cewa ai takora salma gida,kuma kwanan nanzata sani in saketa,alokacin naji kamar anbuga man guduma ga kai tunda na suma ban sake sanin inda kaina yakeba sai gadon asibiti…………har nadawo hayyacina banga raihana ba,ashe tanacan ta kwashi abunda zata kwasa ta soyar da gidan tabar garin……….sai lokacin nadawo hayyacina nagane cewar raihana bata sona tazone daman ta wargaza mana zaman mu.”
Shiru falon yayi kowa ya tausaya mashi,salma kuka take kasa kasa don kuwa du laifinta ne,data kula alaka da ita,gashinan ta jawo abunda yawargaza farincikin su itada mijinta………….lallashinsa
Yah jahid keyi yana bashi hkr,
Abbu yace”Allah ya kyauta,saikayi kokarin gyara kuskurenka kakuma yi istigfari ka rik’e ibada,domin kuwa Allah yace duk wanda yabarni yana tare da 6ata,bazai ta6a ganin dai dai ba.Allah ya bamu ikon rike ibadarmu yakuma rike mana imanin mu,salma kinji bayanin mijinki don haka saiki yafe mashi,don bai cikin hayyacinsa kuma insha Allah zuwa gobe zaki koma d’akinki,zan baku gida halak malak,kuzauna sannan zan samar maka wani aikin,saika kiyaye gaba kasan me kake ciki.”
Godiya maah tayi mashi tare da yi masu nasiha itama mai ratsa jiki,duk iyayen kowa ya tofa albarkacin bakinsa,yaja hankulansu daidai yadda zasu zauna da junansu.
Sannan tarewar Areef da khairat saita gama IT d’inta sun zana exams dinsu sannan,zuwa lokacin Airah ta k’ara k’wari ana ma iya yayeta lokacin.”
Kowa ya dauki atarsa kuwuce gida jenku Allah ya bada zaman lafiya.Ameer kaje zuwa gobe saikazo kuwuce saudah dauko mashi mukullin gidan nan na unguwar gwarumfa,yana nan cikin drower bedsed dina.”
Taje ta kawo mashi ya bashi yaita godiya yana mishi Addua,maah tace ma salma taje ta rakashi,akunyace tatashi Annie da ummi suna mata dariya.
Fitowa duk mukai don rakiyar amaren,ina rike da hannun husna ina mata rad’a dukana fake tana kuka,bilhakki dagaskoya kukan take ummi ke lallashinta tacemun inje indauko hijab na rakasu nida mimi.
Aguje ko muka koma muka dauko abayu don rakiyar amare don daman banje gidan ba zanso inganshi yadda aketa zuzutashi.
Yah Imran da Amaryarsa yah meenah itama kukan take me zamuyi masu banda dariya,sai kace ba su sukace sunji sun gani ba,Anty shida ma kukan take jikin maah,sainaji sun ban tsausayi rabuwa da iyaye babu dadi kokadan,nima sai naji kwallar ta cika idona.hadesu maah tayi yana lallashi da nasiha tare da cewa inbanda abunku ba muna tareba ina nan ina maitama,kuyi shiru kunjiko.”
Daker sukai shiru suna ajiyar zuciya,ummi ma rungumesu tayi tana goge kwallarta itama……..Annie kau kasa tsayawa tayi ta shige gida,Allah sarki abun gwanin ban tausayi saida Abbu dasu dady sukazo suka kai kowace cikin motar mijinta sannan fah yacewa su maah sukoma gida inkuma binsu zasuyi to.”
Murmushi sukai suka shiga gida nida mimi kuma motar yah Areef muka shiga.

muhadu gidan amaren pls aiki nake wlh ????

Mrs bb
Mom muhseen.????????????lov u my fans
[7/14, 3:25 PM] Mom Muhseen: ????????????????????????????
????
ABIN CIKIN RUHINA

Writing by mrs bb
Mom muhseen.

Wattpad name
Humaira7531.

DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.

           54.

Sun isa gidan amaren lafiya tunda ga get din farko zaka gane cewar wannan gidan ba na wasa bane,get din kansa kamar ka k’wal k’waleshi ka gudu, get din farko zaka tarar da wani tsalelen gini hawa biyu,daga fuskar gidan zaka gane cewar gaskiya kudi sunyi kuka bama kadan ba,wannan gida na farko shine na yah jahid,shida amaryarsa Anty shida.
Shiga sukai ciki tundaga waiting falo khairat da mimi harma dasu amareb suka fara santi,komi yaji don tsayawa fayyace tsarinsa sai mukwana mu wuni.
(Zanso kuga wannan gidan y’an zauren mrs bb.kashh kallo yabar ku baya)
Babu inda basu shiga ba suna yabawa har dakin amarya suka kaita,sannan suka fito don zuwa yah Imran.
Areef ne ya jawo khairat baya ya matse jikinsa yamata rad’a.
“Ki kwantar da hankalinki naki yafi na kowa kyau,don maigidan ki anan duk ya juye fasahar da Allah yai masa,kin san ko ai dole namu yafi na saura.”
Dariya nayi ina kokarin kwace hannuna rik’esa yayi gam yana bina da wani irin kallon kauna,daker na fizge na ruga wajen su mimi.
Wanda ke bayan na yah jahid aka wuce mimi tace “yo yah ya zaku wuce nan bayan ga amaryar nan basai mu ajiyeta ba kurun.”
Dungure mata kai yah Areef yayi yace”ankiya tun yanzu ku gane mana gida sai randa zamu tare ko suger nah.”
Harararsa nayi ina bin bayan husna dake kusada yah meenah.
Shima gidan yah imran ya had’u matuka don a iri daya bane,kowane da tsarin nasa nanma muka kara lalacewa muna zagayen gidan,daker muka fito muka kai su husna nasu,shima dai abun ba acewa komi saidai fatan alkairi ga dukkan masoyan,haka muka kai kowace tare da yimasu fatan alkairi,muma muka nufo hanyar gida.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button