ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Wanka nashiga najiyo wayata nata ihu bafitoba saida nagama,lokaci kuma ta tsinke kaya nasa nayi sallar la,asar ina sallamewa aka sake kira.
Dauko wayar nai babu suna aman da alamun daga wajene,harga Allah ban tunanin shi bane na d’auka nace.

“Assalamu alaikum.”
Shirune yabiyo baya nasake maimaita sallamar,
Sai sannan akai magana cewa,

“Baki tausayina khairat………..daskarewa nai inda nake don kuwa tunin duniya na gane shi……so nake na yanke wayar amman hannuna ya kasa,zuciyata dokawa take kurin inajiyo numfashinsa ahankali kamar wanda baida lafiya……jinai yace”pls dr ka sallameni wlh nagaji da asibitinnan haka.”

Silalewa nai bakin gado nazauna kasa,inajin kwallah na cika idona……cikin rawar murya nace”yah …….bak….bakada lfy ne.”

Mrs bb ce
Mom muhseen.
0934722970.
Share it plss
[7/7, 6:36 PM] Mom Muhseen: ????????????????????????????
????
ABIN CIKIN RUHINA

Writing by mrs bb
Mom muhseen.

Wattpad name
Humaira7531.

DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.

           48.

Hawaye share share fuskata kamar ankunna famfo,numfashi ya sauke baice mun komi ba duk hankalina inyayi dubu yatashi,

“Don Allah kayi mgn bakada lfy ne,meyasa baka sanar agidaba plsss kadawo gida hakanan,anan babu mai kulawa dakai……..”

“Idan ma nadawo karaman wani ciwon zakuyi,no need for that Zan zauna anan inmutu kinga kowa yahuta.”

Kuka nake sosai nace”Aa yah kabar cewa zaka mutu,don Allah kadawo gida akula dakai sosai insha Allah yadda kake tunanin abun bazai faruba.”

Lumshe idonsa yayi yanajin wutar kaunarta na sake ruruwa cikin zuciyarsa,dafe xuciyar yayi yace cikin low voice dinsa,datai sanyi kamar kankara.

“Kina so indawo.”

Ina share kwallah na silale kasa na kwanta ina kuka k’asa k’asa daker na fizgo maganar nace,
“Eh”

Sassanyar ajiyar xuciya yaja yace”ki ansa man abunda zan tambayeki.”

Numfashi kurun nake ja saboda yadda nakejin kaina,banson meyasa zuciyta take man haka ba,inhar akanshine bana iya dogon fushi duk yadda nake son nisanta kaina,dana ganshi ko naji muryarsa dandanan zuciyata zata koma kamar ruwa………….daker nace “uhh”

Shiru yayi tsayin lokaci banda numfashinsa bakajin komi,lumshe idona nai ina sairaren yadda yake sauka cikin kunnena,hawaye na silaloman inajin sabbin feelings akansa….. ……….

“sweetheart!”

Jinai duk tsikar dake jikina tana tashi,muryarsa tana ratsa duk wani lungu da sako na jikina still hawayen basu bar zuba ba,na kasa ansa kiransa saidai ajiyar zuciya da fizgar numfashi nake…………..jinai ya sake cewa.

“sweetheart are u on d line!!!”

Wayyo Allahna duk’unk’unewa nai waje guda ina shashsheka,jikina yayi masifar canzawa kadaddabe wayar nayi ina murtsike-murtsike………….bakina yana rawa nasake cewa “uh”

Numfashi ya fesar wanda yasani runtse idona ina jan numfashi,iskar dakin jinake taimun kad’an.

“did you love me?”

Cikin wani irin yanayi na cire wayar daga kunnena na kasheta duka nai switching dinta off.

Wurgata nai kan gado nazauna nadunga gurzar kuka kamar Allah ya aikoni,can lungun bayan gado nashige kamar wata mage,nai mamakin yadda har na shige wajen.

Sosai nake kuka don uku biyu ya hayeman,ga haushin kaina da tsanar halina nara shin zuciya da banayi akansa,ga soyayyarsa kaunarsa shauk’insa sunmun taron dangi,ga gargad’in maah yana amsa kuwwa cikin kunnena kamar yanxu take yiman shi,,,,,,,shin yazanyi da raina ina akeson insaka rayuwata ne wai,yazanyi………yazanyi ya akeson inyi………….ne………na fashe da wani irin kuka mai tab’a zuciya……kamar wata zararra nikad’ai naketa magana ta………waini na dorama kaina ne ehy,Meyasa har yanxu nakaa samun farin ciki dorarre,wannan masifa ta isan nagaji nagaji nagaji………..mimice tashigo da Airah nata kuka rage sautin nawa nai inajan ajiyar zuciya…….”subhanallahi,khairat lafiya kukan me kike kinga yada fuskar ki takoma?ansarta bata tasha garin rarrafe ta k’umeka da table.”

Ansarta nai na ciro nonon nabata ina tsane fuskata da kallabina,zama tai gefen gadona tana cewa”komi yayi zafi maganinsa Allah,kibar dorama kanki damuwa karta zo ta haifar maki da wani abun nada ban.”

Cikin kunan rai nace”mimi wallahi zuciyata ta fara gajiya da daukar k’unci,inajin kirjina yana mun nauyi,narasa ta inda zan kama duk inda naje babu sauki,yanzu yayanku yakirani baida lfy banyi niyar saurarensa ba amman wlh mimi jin muryarsa duk ya ruguza man komi,tabbas duk wani kwane kwane da nuk’u nuk’u nawa,insonsa banda wani burin daya wuce mallakarsa,amman mimi akwai katanga tsakanina dashi,katangar mai tsayice bazamu iya ganin juna ba sai ankaudata,kinsan komi ya faru kinsan kuma sharad’in maah gareni,cewar muddin nacigaba da kulashi inta kamani inkuka da kaina.karma intunanin zata saurareni,shikuma ya huraman wuta yace bazai dawo ba saidai ciwon ya kasheshi acan,niban tab’a ganin bala,in SO irin namu ba taurin kai ya hanashi ya furtayana sona kuma bazai iya cewa yafasa wannan aurenba,shin ki fad’i man yazanyi………….duk yadda nakai ga sonsa da kaunar kasancewa dashi wlh mimi abun yafi karfina,bazan iyaba……….nafashe da kuka.

Iyakar tausayi khairat tabawa mimi don ita kanta saida taji hawaye sun zubo mata,wai meyasa ummi tacika son ranta,yanzu ko tausayi basu bata,shi yanacan rai hannun Allah ita gatanan bak’in ciki zai kassarata cikin d’aki duk wannan bai isa yakai ta dakayar da auren ba,Dady baida wata damuwa inhar tace abarshi zaiyi mirna,don shima baso yake ba miye aibun khairat duk wanda yaganta idam ba yaga Airah bazaice iyace uwarta ba,don babu abundan ya canza daga gareta.

Lallashina mimi keyi tana ban hkr tare da karfafaman guiwa,dayin addua hakanan naji koba komi nafadi damuwata nasamu relif.
Biki yataho yau yah imran ya iso kowa yayi mamakin rashin ganin Areef,wanda ni nasan daman bazai biyo shidinba,tunda shima yagaji taurin kai irin na uwatai.
Ita ummin aitasan bai lafiya amman sabkda karma ace afasa auren yasa bata sanar da dadynsu ba,saida yah imran d’in yadawo yake gaya masu cewar ai yana can satinsa biyu kwance bakda lfy,yace kua bazai dawo ba har sai idan na amunce aurensa……….kowa yashiga shock jin cewa. Baida lfy kuma serous serious sick ne.

Dadyn su yaita fada yana cewa audaman Areef nason khairat baitab’a saniba,nan maah ta bashi labarin komi yadda ya faru abaya,da kuma abunda ya faru cikin wannan kwanakin……….kamar zai ari baki yaketa banbami ummi tayi sukuti kai k’asa,ansar no din dayake anfani da ita yayi wajen imran yashiga kiransa…….saida yakira sau uku sannan ya dauka baibari yace komi ba yahau fad’a,

“Don ubanka karka bari jirgin karfe goma ya taso baka biyoshiba jibi,ashe kai sakaran banza ne loton banza,da wofi kana sonta baka tab’a gaya man ba,kabiyewa sakarar uwarka to karfe biyu na rana ina tsumayinka gidannan dolon banza,har kake kwance sharaf kan mace maimakon katsaya kai fighting love d’inka katsaya dolanci.”
Lumshe idonsa yai yanjin abunda mahaifinsa ke cewa,kokadan zagin bai damunsa wani dadi ma yaji yana kwarara cikin ransa,yau zaiga ABIN CIKIN RUHINSA ganinta ma kadai ya isa ya kwantar da gobarar dake ci cikin zuciyata.

Daker ya lalubo kalmar cewa”insha Allah dady kafinan ma zan iso zan biyo jirgin Abudabi zaisauka abuja karfe daya.”

Tsakiyaja yakashe wayar yana cigaba da fada Abbu da dadyn yah meena keta bashi hkr,nidai daman anafara maganar nabar wajen naga yada za,ai atursasani kuma yanxu don wallahi duk da nake jawara babu wanda zai sani auren mai mata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button