ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Koda na sha ruwan daker ya wuce kuka kurun nake ina shashsheka……..”ummi ban sani ba baigaya man ba,ummi kutai maka man kukaini inson ganinsa ummi banson rashi idan dr ya mutu yabarni nima mutuwar……..”karki sake fad’an haka insha Allah zaitashi bani wayar maza maza imran sake kira kaji wane asibitine.”

Ansa yayi ya shiga kiran number ba jima wa aka dauka,
“Don Allah wane asibitin aka kawo mai wannan wayar.”

Mutumen yace”kuyi kokari kuzo yana nan FMB HOSPITAL sai neman makusantanshi yake don aiki za,a shiga dashi ba lallai ai nasara ba,matarsa yaketa faman kira ita yake son gani kuyi kokari kuzo kafinan da minty talatin…….wyar ta yanke……tashin hankalin da na shiga bazan iya kwatan tashiba wani irin rawa jikina yake bansan ma me bakina yake furtawa ba,ga cikina da yadunkule waje guda ban iya mik’ewa tsaye aduke na isa motar……ummi ke rik’e dani muka shiga motar dagani sai ita da imran,
Lallashina take sosai har muka isa,,,,,tunda muka doshi emergencybanda karkarwa babu abunda jikina yake…..yah imran ne yasake kiran wannan mutumen yagaya mashi inda zamu samai……….ba,a barin kowa shiga d’akin babu inda baya rwa jikina hawayen ma sun k’afe kaf.
Mutumen yayi man iso cikin d’akin………Idan kaga dr bazaka tab’a iya gane shiba……fuskarsa tayi kaca kaca babu inda babu rauni,jikinsa gab’a daya nannad’e yake da bandage………..idanunsa baka ganin komi cikinsu banda jini dake kwance……kuka ya kubceman “innalillahi wa inna ilaihir raju,un hazbunallahu wani imal wakil,,,,,,,nashiga ukuna wayyo Allahna dr na kaine haka dr na Allah yasa mafarki nake,Allah ka farka dani daga wannan mummunan mafarkin,,,,jinai yarik’o hannuna……muryara kanta ta canza ba kajinta yadda ya kama ta,saida na kanga kunnna saitin bakinsa wanda ansaka mashi oxygen……..magana yake son yayi mni,shiyasa na cire mashi shi…….bakin kanshi babu kyan gani,,,,,

“My love…….ki kula man da yarana,Allah baiyi zamu cigaba da rayuwa tare ba,naso in kasance dake iyakar rayuwarmu…..amman da alaman burina bazai cimmaba…….kikulaman da abunda ke cikinki banson hukuncin Allah ba da ya jarabemu da wannan kaddarar,Amman inaji ajikina zakoyi rayuwa mai kyau…….zaki samu mijin dazai kuka da ke fiye da yadda nakeyi maki,ina kuma kyautata zaton yadda zaisoki haka zaiso yarana,idan Allah yasaukeki my love in twins din danake fata kika samu,,,,ina rokon Alfarmar ckinsu kibarwa ummina guda,idan kuma dayane nabar wasoyyar arubuce nabarmakishi har abadan domin kisamu abun kallo kina tunawa dani,,,,,kiyi hkr kidaina kuka zakiyi farinciki nan gaba……..tari yake kasa kasa kirjinsa yana d’agawa yacigaba”inarokon ki alfarmar da kidunga man Addua aduk sanda kika kai goshinki k’asa,my love zan tafi da tsananin kaunarki,zanso ko lahira kizama matata kiyi alkawarin bazakiyi man kukaba,,,,domin kinsan illar da yakewa mamaci karkiyi man alkawarin haka……..kuka nake ina shashsheka bakina karkarwa yake “Aa Aa Dr na kabar fd’ar haka na rokeka kadaina cewa zaka mutu,bazaka mutu kabarni ba inhar katafi nima binka zanyi,yazanyi da kewarka ina zan saka kaunar ka,kataimaka katashi mutai gida kaganifa yaranka najinka tab’akajisu takai hannunsa saman cikinta…….idanunsa ke kakkafewa yayinda wani uban tari ya tirnik’eshi babu kakkautawa…..dandanan jini yaringa anbaliya ta hanci tabaki…..afirgice nake kallonsa yafice daga hayyacinsa likitocin dake kulawa dashi suka iso cikin gaggawa,fita dani suke ina rizgar kuka,,,,ni subarni naga mijina subarni muyi hirar bankwana……su ummi suka mik’amani kuka kurun nake ina kiran dr……suna can aka shiga dashi operation don tunda dama aka kawo masu accident din shine wanda yarayu zuwa yanzu sauran duk babu wanda yarayu.
Don kafarsa guda jijiya kurun ke rik’e da ita dole suka cire ta don bazata tab’a gyaruwaba,,,,,,akwai wani karfe daya soki hunhunsa sunyi nasarar ciresa tun sadda aka kawoshi, yanzu aikin cikin zasuyi mashi,aikin yana da had’ari sosai don sai maitsawancin kwana da rabo yake rayuwa,amman dayawan mutane sun rasa ransu wajen irin wannan aikin.

Nayi kuka har muryata bata fita,su kansu su ummi kukan suke suna share hawaye,,,,,, tun yamma har dare suna nan suna jiran tsammani har baccin wahala ya daukeni………su ummi ne sukajira anfito aikin susan wace akeciki…….tsoranta daya kar dr ya mutu in yamutu ba karamin tashin hankali khairat zata shigaba,ga cikinta zai iya samun matsala………likito cin basu fito ba said wajen karfe d’aya……..sunce sukara hkr zuwa safe aga yadda jikin zaiyyi,sun kwantar masu da hankali sosai sukace suje gida da safe su dawo lokacin ya farka.

Haka mima koma gida har lokacin bacci naked,van farka ba saida mukaje gida…….anan dadynsu yake tambayar me yafaru nan take sanar dashi halin da ake ciki………..ban iyayin bacci ba wannan dare tun bayan wanda nafara asibitin,yanzu kuwa ko alamarsa banji saboda tashin dake kaina……waya mukai da umminsu tace sunana isowa da safe yanzu jirgin zatashi zuwa shidda na suba sun so…….lallashina take sosai tana kwantarmun da hankali wanda nima nasan itama tana cikin wanda yafi nawa,saboda ita d’anta ne bata iya sake haihuwar kamarsa,nikuwa zan iya sake wani mijin………kuka shine yatayani hira kafin gari yawaye…..saboda kerma har raui aji aman ba dauba daker nayi sallar asuba na k’agu muje ko naganshi insamu natsuwa…….zuciyata karkarwa take sadda nafito zamutai jikina kamar ansakani cikin frig k’arara…….bayadda ummi batai dani ba akan inci wani abu amman nace bazan iya cin komi ba dole ta rabu dani hada dady muka tai wannan karon a harda Areef.
Wanda nakejin wata iri tsanar sa saboda duk shine yayi silar faruwar komi,,,,,,alokacin dabai bankeniba nasan zan samu dr ya gaya man inda yake aje adaukosa……amman dayake mugune shi azzalumi gashinan tasilarsa Dr na yasamu mummunan illar dako yarayu balallai ya zama yadda yake daba……..muna isowa kofar asibitin naji wani mummunan fad’uwar gaba ta riskeni……cikna yawani motsa har saida na dafe marar.
Kamoni ummi tayi na rungumeta inajin jiina amar ansakaman electric………banda rawa babu abunda yakeyi…..idona kuwa banda hawaye babu abunda yake fitarwa……ina hango umminsu da su jalila harda Abbansu durkushewa nai kusadasu ina rizgar kuka……..mai tsuma zuciya d’agoni tayi ta rungume duk da cikina daya turo sosai…….itama hawaue take gogewa su jalila kam kuka suke sosai itada fati………adaddafe dai aka gaisa kafin likitan yazo yace “mutun uku kurun zasu shiga don baison hayaniya……….nida umminsu da Abbansu muka shiga kafafuna kerma suke hangoshi danai, kuka kurun nake inajin zuciyata tana kakkaryewa……..idonsa kurun yake waje yanzun ma Izzy ne hancinsa da bakinsa……..hannu ya mik’oma mu duk muka karasa gareshi….umminsa kuka tafashe dashi tana cewa,
“Muhd,kaine haka muhd garin yaya innalillahi ya Allah katashi kafad’ar wannan bawan naka wayyo Allahana idan narasa ka muhd yazamuyi ina zamu saka ran mu muji dadi…….kuka taitayi Shikanshi Abban kasa magana yayi saidai hawaye dayake sharara daga idonsa…….hannunsa yasaka daker ya cire oxygen din……muryarsa adishe ta shak’e yace”kudaina kuka ummi,,,,,,,don Allah ko na mutu karkuyi man kuka hakan zai cutar dani………ummi koda na mutu nabar wasiyya arubuce tana dakina cikin drowar na komi na rubuta don Allah ayiman……sannan ina rokon ku dakuyita yiman Addua,,,,,,,,,kallona yayi yasakarmu wani murmushi zan iya cewa tunda nake dashi ban tab’a ganin yayi manshi ba,yace”inasonki matata,inasonki zanbarki badan raina yaso ba,ummi Abba kuyi hkr inata fadan maganganu gabanku,ban da yadda ina iyane idan ban fad’a yanzu ba banda sauran lokaci dazan sake ganawa da ita……..rike hannunshi nai gagam ina rusa kukana muna cikin haka yafara wata irin shak’uwa………dandanan na rikice ina rik’e da hannunsa har lokacin…….aguje likitocin suka shigo,suka roki su Abba dasu fita amman nace babu inda zanje,,,,,sai dai su dubashi gabana daker da sidin goshi akajani waje kuka nake kamar raina zaifice………kowa hankalin sa yayi kololuwar tashi ganin andauki awa guda babu alamar zasu fito……ina jikin ummina likitan yafito sai uban gumi yake……Abbansu dr ya fara nufa yajashi gefe amma bama jin mesuke fad’a……Abban mukaga ya silale kasa yadafe kai nana take naji wani irin duka ga zuciyata…….kaf kaf kaf kawai jikina yake dadunsu yah imran ne naji yana cewa ma su umminsu dr.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button