ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Abbu da yah jahid gaban likitan da ya gama duba ni, fad’a yake yi kamar zai ari baki, hakuri suketa bashi daker ya yi masu bayani.

“Kasan yarka na daf da kamuwa da ciwon zuciya kuwa, tun sadda na duba ta lokacin baya nasanar dakai,na kuma cema adaina fusata ta da yawa, to gashinan zuciyar ta na mataki na second to the last, muddin irin haka ta cigaba da faruwa, to bazan iya kareta daga abunda zai biyo baya ba.
Don haka ruwanka ne kasama mata farinciki, ruwanka ne kabarta damuwa ta kasheta.”

Maguguna ya rubuta tare da sallama, idan tatashi baccin wuyar da tashiga.

Suduka jikinsu yayi masifar yin sanyi,koda suka fito kowa da irin abunda yake sak’awa.

Mutan gidan duk sunzo Anni kad’ai suka baro, meenah idonta yayi jawur, Areef kuwa karkaso hada ido dashi, don kamar jangauta haka yakoma, babu wanda yabi ta kanshi tsakanin Abbu da jahid.

Ban farka ba sai wajen shabiyu na dare, dole saida nakai washe gari sannan muka koma gida.

Kowa sai nan nan yake dani maah kuwa inakan cinyarta, abinci kanshi da kanta take bani, har yanzu Abbu baice komi ba, yah jahid baya yin cikakkar one hr baizo ya duba niba wata sa,in ina bacci wata sa,in ina danna waya komuna fira da maah.

Gogan naku kuwa har yanzu banga keyarsa ba, haka zalika nima kuma ko inuwarsa bana kaunar gani, don yanzu wata irin tsanarsa nakeji har kasan zuciyata.

Salma kuwa yanzu duk ta canza Mani, bama niba kowa na gidan ta canza mar fuska, maah kuwa ta yi iskar kare da ita, ban sa mekefaruwa ba abun yana cimun tuwo a kwarya, shiyasa nace zan mata magana yau.

Yah meenah ta gama mana registration dinmu, tun kwana uku da suka wuce.
Ranar Monday zamu fara zuwa makarantar, dadi ya kamani ko banza nashafe babin wanan gayen mai bakin hali.
B’angaren Abbu na nufa don kiran maah tazo muci abinci, insamu damar tambayarta.

Saidai ina shiga nafara jiyo sautin magana da d’an karfi yana tashi, saika kasa kunne sosai zakaji maganar kamar ana fad’a………gabana ya yanke ya fad’i abunda ban tab’aji ba iyakar tsawon rayuwata.

Ahakali da najuya zanfita, saidai ambaton sunana danaji anyi yasa dole matsawa jikin k’ofar bedroom dinsa na kanga kunnena.

“Saudah baki tab’a neman wani Abu arayuwata nace bazan iya maki shiba, duk kanin abunda kike buk’ata ko ina dashi kobani dashi saina nemo na kawo maki don inga farinciki cikin akan fuskarki, ban tab’a zuwa maki da wata bukata ba tunda mukai aure, tsawon shekara talatin yanzu sai yau, Amman kirufe idonki ki watsa mani k’asa ga ido.
Ban boye maki halin da y’arki keciki ba, na sanar maki don musamu mafita, mufitar da ita daga halin da take ciki shekara goma sha, Ashe ke kina can kin saka takunkumi mai tsananin girma tsakaninsu, kinjefa yarki cikin halin damuwa, kin jefata cikin masifar da zata iya rasa ranta abisa wannan dalilin, shin idan Areef ya Auri Khairat yana nufin ya tashi daga d’anki kenan, ko yana mufin kin rabu dashi kenan.”

Kuka take tana cewa Abbun khairat shin wai kamance alkawarin mu da anty hafsat, agabanka tayi magana aranar da ta bani Areef, cewa tabani halak malak, kuma bata yafe ba idan na banbantashi da yarana, sannan gudun son juna ya kama guda, yasa tace na haramta masu juna, idan ba haka ba babu ta yadda za,ai areef ya cigaba da zama matsayin d’an dana haifa, inhar yasan wannan babu makawa duk girman da yayi wajena zata anshi abunta, don tana son Areef ya d’auka nice uwarsa har iyakar karshen rayuwarmu nidashi, ina son Areef Abbun khairat, wallahi ko shahid da shahida, da ita khairat din banajin kaunarsu irin yadda nakejin sa, saboda shine mutumin daya samomin kima da mutunci waje mutanen da suka gasa mun aya ga hannu, akanshi suka fara yimun kallon rahama, taya kuma yanzu saboda yar cikina in fallasa wanan abun, yaka keson suringa kallona bazan iya barin wannan abun ya fito bah, khairat tayi hakuri Allah zai yaye mata, ko salma ba zata aurai ba ta gama haukan nata. “

“Na gode maki saudah, akan wannan kikeson y’ata ta mutu ko, saboda kar Yayarki tace zata anshi yaronta ko, to shikenan ni zan Sanar da wanna sirrin ga kowa, zan kuma yiwa Areef tayin Auren khairat, saidai idan shine yace baya sonta bazai aureta ba, zan hakura kuma zan yiwa khairat Addua Allah ya bata Wanda yafishi Alkhairi, inhar khairat bata samai ba babu Wanda zai auresa daga salma har shahida da meenah, nagode.”

Jin alamun zai fito yasa nafice aguje, kewaye na shige nayi kuka kamar idona zaifita, nayi kukan da ban taba irin saba, Wanda har saida nayita amai akewayen…….
Mom muhsen ce
Mrs bb[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: ????????????????????????????????
ABIN CIKIN RUHINA

Written by [Mrs bb]

Mom muhsen ce

________________________

????????AINUWA ????RITER’S✍????
????SSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

12&13

Ganin halin dana shiga zai iya saka aganoni, shiyasa nayi iyakar kokarina wajen ganin na dawo cikin natsuwata, ina nan kwance salma tashigo tana wani taunar cingam cikin yatsina fusma, mamaki nake yadda salma ta canza sosai daga dawowar su yah Aree zuwa yanzu, kokadan yanzu salma bata damu da damuwata ba, sai gari ya waye har rana ta koma ga ubangiji, salma ko kallon banza ban isheta ba, idan ma ni nayi mata magana baza ta kallan ba zata ban ansa, tabbas ina hasashen wani Abu dangane da ita, salma ba haka take ba inson sanin dalilin canzawarta.

Wayarta ta ajiye ta shiga wanka ta fito tahau shirin bacci, Amman sai ka d’auka miji gareta sai kwalliya take yi, tana ta feshe jikinta da turaruka, kallon ta nake ina mamakinta.

Har ta gama bata cemun uffan ba, saida zata fita har takai kofa ta juyo cikin rainin hankali tace,

“Oh na manta fah kifito can babban falon Abbu ana nemanki.”

Ta juya bin bayanta nayi da kallo kafin na yuk’ura na tashi, sake wanke fuskata nayi nafito, tabbas nasan wannan maganarce za,ai gaba na yana fad’uwa na isa kowa nanan har dadyn yah meenah, dasu Anni da yah jahid kowa dai yana nan banda yah shahid da sai karshen wata zaizo hutun karshen shekara.

Zama nayi can gefe bakin kofa, saboda irin kallon k’ask’ancin da yayi min muna had’a ido, bacin tsoronsa da yacika zuciyata ai dana rama.

Yah jahid ne ya bude mana taro da addua,kafin kowa ya shafa muka maida hankalinmu kan Abbu, gyaran murya yayi ya fara da cewa.

“Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata,ala da yanuna mana wannan rana, ya kuma nuna mana girmanku, Wanda da ba haka kuke ba, an wayi gari kowa ya mallaki hankalin kanshi, zuwa wannan lokacin nasan wasu daga cikinku kanku yatoshe, abisa wasu al, amurrah watau abunda kefaruwa shine, azahirin gaskiya Yayanku areef ba mune muka haifeshi ba, bamune mukashayar dashiba, saidai kuma mune iyayen rikonsa, konace ahalin yanzu dai Areef namune, watau Abunda ya kawo wanan magana shine babu batun b’oye b’oye, Areef kanwarka khairat tataso tun bata san kanta ba, take kaunarka Wanda data kara girma ta fahimci cewar babu aure tsakaninku, tayi kuka tashiga damuwa Wanda wannan damuwar itace ta ja har aka mata ripeting makaranta, karshe ta kasa rikewa ta sanar da Annin Ku, ganin wannan ba abunda za, a kyale bane yasa ta sanar dani, bata gaya ma mahaifiyarku ba saboda taji irin furucin da tayi wa yarinya k’arama, cewar inhar ta sake jin wani yanayi na soyayyarka aranta bata yafe mata ba, alokacin ta nuna cewar akwai alakar aura tayya tsakaninku, Amman ta haramta mata kai, saboda wani dalili.
Ban tab’a d’aukar hakan zai kawo ma khairat matsala ba, sai gashi lokacin da ta kwanta asibiti likita ya sanar dani tana da damuwa, idan da hali a San yadda akai akayi mata maganinta, saboda zuciyarta ba zata iya d’auka ba, ban d’auki wani mataki ba, saboda ina ganin abari zuwa sadda zaka kammala karatuka sannan itama tafara hada hadar shiga jamia,sai na sameka da maganar in ka amunce na aura maka ita.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button