ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

(Wayyo nasan YAN ZAUREN MRS BB ZASUYI MISSING AREEF.)
MUHADU GOBE LOVE U ALL MY MASOYA ????????????????????????????

MRS BB CE ????????
09034722970
[6/8, 1:14 PM] Mom Muhseen: ????????????????
????????
ABIN CIKIN RUHINA

Written by mrs bb
Mom muhseen.

Wattpad
Humaira7531.

DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.

NOT EDITED:INKUNGA MISTEK BE SORRY????

              27.

Missing page????

Silalewa nazoyi zan zube sabo yadda jikina gaba ki dayanshi babu kuzari,babu karfi tare dani jinai anyi azamar rikoni,bazan iya gane ma kowaye ba nadaiji muryar yah jahid yan cewa abude mota,kilan shine yatareni.
Motar aka sakani sannan nafara gawowa natsuwata,ina hango jirgin ya lula cikin sararin samaniya,wani kuka ne ya kubceman mai rikitarwa,na dunkule waje guda inayin abuna………Anty ce tarungumoni jikinta tana lallashina,
“Kiyi hkr mana ance makine yatafi kenan,duka wata nawane in Allah yakaimu.”
Jinai yah jahid yace”nima cikin satin nan zantafi ai.”
Cikin rudewa tace”rufaman asiri kabari idan anyi auren saimutai duk inda kakeso,amman wlh banda yanzu azan iya jurewa ba.”

Murmushi yayi yace”to taya kike tunanin ita zata iya jurewa,kinsan irin d’acin da takeji cikin zuciyarta kuwa.”
Daina kukan nai don inason tabbatar wa shin dagaske auren za,aimun don maganganunsu sun nunaman cewa ansan da kaunarsu agida.

“Anty,wai dagaske aure Abbu zaiman.”
Kallona tayi tace”ina kiji maganan nan,bacin anhana kowa yi maku ita.”
Jinai wani kullutu yazo man wuya ya tokare,shiru nai ban sake tankawaba.
Don wani abun yafi gaban kuka sonake naje naji shin dalilin dazaisa atsigeman karatu ayiman aure,bayan ni nace baso banasoshi yanzu abarni nayi karatuna mana,wallahi duk wanda yayi dalilin wannan maganar Allah ya isarmu.

Muna isa gida afusace nafito na wuce bangaren maah,bata nan na zube kan gadonta ina sharar kwallah jinake kamar nayi tsutsuwa na bishi,wani irin yanayi nake ciki rashisa yafi mun ciwo matuka akan auren da akece za,aimana,jinake banda wani sauran farinciki ko annashuwa akan tafiyarsa,duk wani feeling’s dinsa danakeji ada can baya,na yanzu yalinkashi goma kirjina nakejin yana mun nauyi,jinake bazan iya kaiwa har wannan lokacinba,wata hudu koma fiye dahaka wannan abun danake ciki zaibarni kuwa.
Maah ce tafito daga bandaki tayo wanka,kallona take yi batace komiba.
Ina ganinta natashi na fada jikinta narushe dawani irin kuka mai tsananin cin rai………….bata kokarin lallashina ba kuma tabace mun komiba yinake yi har inajin kamar numfashina zai dauke,cikin kukan nake cemata”maah Meysa zaki yarda aiman aure nan,maah kinfi kowa sanin banso ni banso karatuna nakeso ayazu nakeson aurenba,maah wallahi in akayishi zanshiga wani hali kitai amakeni,kiyiman rai…………rungumeni tayitsam jikinta muka kara sa saman gado da ita sai lokacin tashiga lallashina,
“Ya isa haka kidaina kuka,inkinason nayi maki bayani idan kuma bakyaso to kiyita kukan.”
Dole nayi shiru ina sauke ajiyar zuciya sai shan majina nake,shiru duk mukai ina sauraronta.
Cikin taushin murya da lallami tafara man bayani.

“Bayan tafiyarki makaranta kinkoma hostel,zuwan inna gidannan yafi biyar tana zuwa wajen mahaifinku bai dawo ba,bayan yadawo tasake zuwa muna tare lokacin ko ansa gaisuwata bataiba,take yiwa Abbunku magana akan tana bashi umurnin cikin wata uku ya aurar da duk yaran dake gidannan,don salma taje tasameta akan cewa itafa batason karatu,aure takeso kuma wanda takeson ni nahana shi ya amunce da ita,ina son dole sai nabashi aurenki.”

Anan tasan cewar Areef banau bane,tayi fada tatashi hankalin kowa agidannan,har takecewa sai yabar gidan tunda bana uban shi bane,wallahi idan baibar gidanba saita tsinema mahaifinku.
Ananfa shima yanuna mata nashi b’acin ran,yace Areef bazai tafi ko inaba shine ubanshi har duniya tatashi.
Tace to kuwa wallahi zaiga bacin ranta kuma muddin bai aurar dakuba tasan matakin da zata dauka akai,kuma wallahi muddin tana raye cikin ku jikokinta babu wacce zata auri Arref,.
Anan nace ta kwantar da hankalin duk cikin yarana baida mata,domin Areed dana nacikina nake kallonsa,yayansune shi tsayyae kan lamuransu,nan tace naimata rashin kunya ke tashin hankali babu kakkautawa,saida ker Annie tafiddata gidannan.

Ranar salma bata kwana gidanba don wallahi nai alkawarin tashigo hannuna sai na lahira yafita jin dadina,bayan wannan yawuce Abbunku yazaunar dani mukai magana kan issue din,cewa salma fa ta dge akan muddin bata samu Arref ba to kuwa babu wadda zata zauna dashi,kuma Khairat bazata zauna lafiya dashiba,don wannan tsoron dakikemai salma ce takai sunanku wajen malamin zaure,akan ya shiga tsakaninku yamaki tsoronshi,yafidda maki duk wani yanayi da soyayyarshi cikin ranki,kinji dalilin jin tsorsnki.
Abbunku yaje yayi bincike sosai yagano hakan daman ni tun tana nan gidan nalura da ita,bandai cewa kowa komiba.
Anan dai yace mun kowacenku bazata aurai ba kuma aurar daku shine yfiye mashi kwanciyar hankali,yanajin tausayinki don yadda yaga kinason karatunki yanajin takaicin tsigeki yayi maki aure.
Amman Baida mafita sai wannan,da har yace akwai yaron abokinsa zai hadaki dashi,to kwatsam saiga yayanku yazo yake sanar da Abbun cewa ai kinada ma wanda kikeso karyayi maki wannan auren nahad’i…………Saboda son da areef kemaki yasa Abbun ku canza ra,ayi kan hakan,yace zayi bincike akanshi kuma yayi ya tabbatar da natsuwarshi da gidansu,.”

Zuwa yanzu idona yabushe saidai wani irin masifar zafi dasukeman,zuciyata duka kurun take nace”maah wallahi ni bason shi nakeba kawai mutunci yakeman saboda yasan ni kanwar yah Areef ce baice yana sona ban.”
Kallona tayi yace”nasani khairat,duk abunda kefaruwa yayanki ya gayaman,yaban shawarar kuma data dace dake.”
Kallonta nake cike da mamaki “wace shawara ken maah.”

“Yace in tsaya tsayin daka don ganin kin auri Dr,domin hakan shizai kawarda tsananin kishin da salman keyi dake,hakan zai dauke idonta daga kanki tabarki kiyi rayuwarki cikin aminci,saboda yanzu ta hakura dashine saboda tasan kema bazaki samaiba.
Saboda Areef yatafi kenan harsai anyi aurenku kuntare kozai dawo,don haka kiyi hkr kiyi hkr kiyi hkr khairat,duk abunda yau kaga kanata haukan sonshi baka samaiba to Allah yasan hakan shine alkairinka,bansan dalikin dayasa Allah yasa lamarin yazo ahakaba,nidai nasan zabi nabashi kuma wannan shine zabindaya bamu nidake,don bantaba hutawa ba wajen yimaku adduar samun abokan zama nagariba,don haka karki bani kunya karkibiyewa zuciya takaiki tabaro kirungumi kaddararki hakan shine Alkairinki.”
Shiru nai narutse idona ydda nakejin kirjina yana suya injin bakina yana d’aci,yasa nakama ambaton sunan Allah,ina karanta hazbunallahu wani imal wakil.

Munfi minty talatin shiru babu maicewa komi,sai lazimi nake ita kuma tana shashshafa kaina har naji abunda ya tsayaman ga makwogworona ya rage kaifi.
Nace”ita salmar waza ta aura maah.”
“Wanine d’an uwan mamanta,sun ma daidaita kansu dazu fadan dakikaji Abbunku namata kancewa ita bazaitayi karatuba ne.”

“Ita ma Antynku ai sun daidaita ita jahid,abun yayi man dadi sosai,da ace yayanku zai yarda sai y auri meenah.”

Saboda bugawar da zuciyata tayi yasa dole na rutse ido.

Tacigaba dacewa”amman bazan masa tutsuba nabarshi ya huce daga rashin samunki,sai yanzu nasan bankyaita mashiba khairat saboda tunfarko bak’inki yakeba saboda ni yakoyawa kanshi shamaki mur,baya wasa dake bayan yanayi dakowa,yanayine don kema kicire abunda keranki akanshi,yana ganin idan kunmani biyayya zanji dadi.
Inason Areef saboda biyayyarshi gareni,indai zanyi farinciki tokuwa komiye zaiman,zanyi kewarshi sosai dalikin kukana kenan dazun,don nasan wallahi bazai dawo don yanzuba,nakira yaya hafsa nayi mata bayanin komi takuma fahimceni,nace tayi kokari bayan bikinku ta sashi yadawo,takuma tabbatarmun da hakan.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button