ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

????????????????????????????

Washe gari bantashi ba sai twelve,kasancewar banda lectures sai 2:00 pm Abbu nanan tunda nai wanka n shirya najena gaido Annie har take tambayata meya saman jiya taga Areef yashigo dani.
“Annie turgud’ewa nayi nazo shigowa k’ofar falo,kinsan daman wannan wajen ba,a wuceshi da sauri,sai kurun na fad’i shine ya taimakeni.”
Nasan idan ba haka nace bah banda wata karyar data wuce wannan.
“Aikuwa nasani tunda nima yasha kadani,kiringa bi sannu da yarintarki karya gurguntaki,dasauki k’afarko.”
“Eh naji sauk’i sosai nashafa man zafi awajen .”
Daga wajen annie wurin maah na wuce, bata falonta na wuce uwar dakarta…….maah ce zaune kan dardumar tsakar dakinta kafafunta mik’e yah Areef ne kwance kan k’afafunta, salma na gefe tana dama mashi fura,gallala nayi ina kallon ikon Allah,dukda bawani abubane da bantab’a ganiba,amman nai zaton zuwa yanzu yah yagirma da wannan alon na yara,ai sai yabarmamu…..kamar injuya naji amman ganin duk sun ganni yasa na idasa,gefen maah na zauna ina gaidata,nacewa salma”yau bakije makaranta bane.”
“Fuskar ta duk ta yamutse kamar tayi kuka,tave”wallahi banjeba yah nebaida lafiya,bazan iya zuwaba.”
Kallonshi nayi idonsa rufe ruf,eyelish dinsa sun kwanta kamar na mace,
Can k’asan muryata nace”sannu yah Allah yasa Wake.”
KO ma ah dake musadani banyi tunanin zatajiba balle salma dake d’an nesa damu,amman shi dake kwamce kan cinyarta rasss cikin kunnensa,yace”Ameen.”
Lab’b’ansa kurun zaka gane kasan yayi magana,duk da haka ni naji jinai maah tace”baki gaidashi da jiki.”
Mik’ewa nayi nace”ai nayi mashi bari nake waken Abbu kafin time yayi.”
Banjira cewarta ba nafice,ina mamakin salma saboda wani ta kizuwa makaranta,nalura yanzu saboda shi kokadan bata son karatun…..wata zuciyat tace ita tasani.
Waken Abbu mu kayi lunch dina,ganin yana cikin yanayin jin dadi yasa nace”Abbu dongirman Allah kayiwa yah Arref magana yabarni nakoma hostel,wallahi sainafi jin dadin karatun kagafa wataranar har ten nake kaiwa ban iso gidaba,plsss Abbu don Allah kayi amshi magana.”
Murmushi yakeyi yace”ta Alkairina kean,kindai aida yayanki kamar wani dodonki ko.”
Kaina na k’asa ina wasa da yatsuna nace”Aa Abbu ba haka bane wallahi shine yake mun tsawa,Kuma ni banaso ko had’a ido mukai sai ya hararenifa,wallahi Abbu yah Areef ya tsaneni yanzu.”
Girgiza kai yayi yace”Aa ta alkairi karna sake jin haka daga bakinki yayanku bazai tab’a tsanarkiba,kin kasa fahintarsa ne kisaki jikinki dashi kudawo kamar da keda shi.”
Icon dandanan ya kawo ruwa,don basusan irin tsanar dayake mun ba,cikin karyewar murya nace”Abbu pls”
Yah jahid ne yashigo yace”ta alkairi ta shirya in sauketa makaranta.”
Goge kwallata nayi ina gaidashi,
Abbu yake gaya mashi abunda nakeso.

Murmushi yayi yace”karki damu inhar hakan shine mafita tokiyi don koni ina baki goyo baya zaman hostel din fiye da kima,don inason ganin ta Alkairin Abbu tayi karatu sosai dazai saka tayi passing.”
Murushi nayi mai kyau naji dadin kalamanshi nace shikenan zan mashi maganar inkuma baiyarda bafah.
“Abbu yace zaima yarda ai Areef nakine babu mai shiga tsakaninku ko ko jahid.”
Dariya yayi yace”sosai kuwa Abbu.”
Ahaka nabaro wajen natai nashirya yah jahid ya wuce dani makaranta.

Mrs bb ce????????
Mom muhseen
[6/2, 8:21 PM] Anty Ushe: ????????????????????????????????
ABIN CIKIN RUHINA

Written by [Mrs bb]

Mom muhsen ce

________________________

????????AINUWA ????RITER’S✍????
????SSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

              21.

Yau lecture biyu garemu sai pratical d’aya,shiyasa muka tashi da wuri…….husna da wata qawarta rahma suka rakoni bakin get muna tafe muna fira,rahma tace”kin san khairat DR MK fa yana ciki,don wallahi ydda nakejin labarinsa wajen wad’anda suka fita abu babu sauk’i,baida kirki ko kad’an kuma ga tsanani wajen test ko exam,amman abun mamakin shine yau da ya kama mu muna noise nai zaton walh korar mu zai sai naga baice mana komiba.”
Jaki naja nace”shine kuma yace maki rahma inason khairat.”
Husna dai dariya take ba tace komi ba,
“Ni bance yace haka ba,Amman kina dai gani yadda muke addabarsa da surutu class bacin ko ranar da yafara zuwa yayi mana kashedin cewar babu abunda yatsana sama da makara da noise,kuma duk wnda yshiga cse dashi yabani.”
Girgiza kai nayi nacewa husna”wannan qawartaki bata da kan gado pls kina ringa kwatanta mata pls.”
Me husna zatai ba dariya ba,rahma ranta ya b’aci rakiyar da batai ma kairat kenan ba…….munata dariyar tare nace”haba wlh kina fama da kwashe kwashen abokai marasa kan gado,shiyasa fa ni kinganni nan ban wata qawa data wuce ke,kema don naga kin zo daidai dani ne,inbacin iskanci ko ya akai tasan haka.”
Husna na dariya tace”kika sani tashiga zuciyarsa ta gano.”
Tsaki naja daidai munzo bakin get nace”ki koma yamma tayi sosai…….motar dake shigowace ta katseni.
Duk makarantar babu mai irin motar in bashi ba,motace ta gani ta fad’a kowa santinta yake school din.
D’auke kaina nayi nayiwa husna sallama na nufi fita,driver baizo ba kuma banzo da mota ba,daman yah jahid ne ya kawoni…….tracking nakeyi ina dub hanya kozan samu taxi,don hanyar ana wuyar abun hawa,duk yadda naso inje gida kan mangruba da alama hakan zai wuya……..ban gama tunani naba motar nan tayi parking gabana.
Tsoro naji ni dafarko kafin ya sauke glass din tagar gefen shi…..
“Shigo mine in kika tsaya jiran taxi zakiyi dare.”
Fuskarshi bbu alamun wasa ban iya musu da malamina ba shiyasa kurun nashiga,shima kuma don nasan yasan gidanmu nasan bazai cutar dani ba,don Abokin yah Areef ne sosai.
Shiga nai kurun ya cigaba da tafiya saida muka hau titi sosai yace”ina motar ne yau”
Ina danna wayata nace”banzo da itaba daman Yah jahid ne ya kawoni.”
“Oky,Amman ya kamata abaki mota saboda irin haka,idan kuma Abbu yana ganin kinyi k’aranta yabarki ki dawo hostel inaga hakan zaifi,don irin haka akwai risk gaki mace.”
Shiru nayi ina sauraren sa,hakika yana da zak’in murya sosai ga natsuwa komi cikin natsuwa yake har maganarsa.
“Nace insha Allah zan masa magana.”
Daga haka bamu sake cewa komi ba har mukaje gida……..ban yarda yashiga ciki ba nace yasaukeni nan ma bakin get is oky.
Fitowa nayi nace” thank u sir.”
Gajeran smile yayi yace”ur welcome, kigaida Maah.”
Nada”zataji.”
Sauri sauri nake don kar wanda ya ganni nashige ina ajiyar zuciya,don bansan yazance ba idan aka ganni ya saukeni,duk da ansashi cikin gida hakan bazai hana su tabayeniba.

B’angaren Annie na wuce in tajin dadin babu wanda na gamu dashi,yah meenah na ta gyara kayanta na wadrop tayi guga nashiga dakin,
” sannu dr kairat.”
Murmushi nayi nace”me akayi da maza yah meenah kofa first semister bamu gama bah.”
Kaya nahau cirewa tace”kamar gobene insha Allah.”
“To Allah ya Nuna mana lokacin lafiya,bari nayi wanka inyi sallah zaki rakani wajen boss.”
Dariya tayi tana tambayata waye boss,
Inacewa idan nafito zakiji.
Ban wani d’auki lokaci ba nafito shaf shaf nayi shafa nazura kaya,Allah yayini ba gwanar kwalliya bace,don ni sometimes ko powder bana sawa in zan fita school,amman i wonder nake ganin yadda wasu ke daukar heavy make up suna shiga school…….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button