ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

“Don Allah karkaga laifina,wlh yah maah zata dauki mummunan mataki kaina muddin na kware mata baya,ka fahimceni,wlh na damu nadamu sosai akan wannan halin,karka yiman bahaguwar fahimata,wlh inasonka banda burin daya wuce kasancewa dakai tsawon rayuwata karka ce zaka hukuntani ahaka zuciyata bazata iya daukaba,wlh inajin ka tamkar fitar numfashina karkayi man haka don Allah……….na fashe da kuka ina shashsheka……zare hannunsa yayi yace “idan da kinsan kalamin dani ummi ta yiman akan gujewa wannan auren ke bazakice haka ba,amma kasancewar ina ganin idan na biyeta abanza zan illata rayuwata,dole tasa nadage wajen ganin nasamo kanki,amman shine zakice ke bazaki iya ja da umurin maah ba,yes hakan na da kyau bance kija da umurnin taba,amman ai saikisan hanyar da kika bi don ganin ta gane cewar kinson kasancewa dani,inba dai kema kin gwammace mutuwar tawa da rayuwata ba.”

Sake rik’e hannunsa nai ina kuka sosai “yah karka gujeni wlh ina sonka zuciyata takai limit d’in da bazata cigaba da daukaba amman kasani daraja da kima sun wuce komi,gara ka rasa komi daka rasa su………cikin wani irin yanayi ya juyo afusace wanda ya tsoratani,,,,,,,har jijiyar kansa ta fito sosai…….idonsa yayi jaa sosai kwallah sun kwanta ciki muryarsa ta dishe sosai yace jinjina”is ok hakan ma ya isan.”
Ya fizge hanunsa ya shige cikin gida yabani zaune ina kuka mai tsananin tafasa zuciya,daker na tada motar bayan nadawo inda yake na shiga cikin harabar gidan.
Parking nayi lokacin sha biyu na dare,ta baya na shige cikin gidan dakin yah meena nayi masauki……..bacci suke don dagani sun gaji don duk dakin na same su salma ma k’asa tayi shimfid’a ta kwanta………..silalewa nai kasa bakin kofa naita rusa kuka na,yazanyi da maah ne wai meyake son nace mata,wai ko yamance irin zafin zuciyarta idan ranta yab’i da abu,ba ayenta bane tayi man mugun duka wlh,wata shawara tazo man nai saurin amuncewa da ita don idan ba haka ba banda wani hanya,kewaye na shiga nayi wanka nazo nai sallar isha,i na kwanta duk da ba baccin nakeji ba duniyar tunani natafi wai yau yah Areef ne yafurya man kalaman da nashekara aru aru ina tsumayinsu daga gareshi.yau iyae man kuka da idon sa akan yana sona,wannan kadai ya isan farinciki haka na lalalce ina tunaninsa bansan sadda bacci yayi awon gaba dani bah.

       **********

Washe gari daurin aure ant hidima nikuwa bacci kurun nake har wajen sha d’aya saboda ban samu nayishi da wuri ba jiya,kukan Airah ya tadani.
afigice natashi ganinta nai ita kad’ai tashi nai naisaurin daukota ina dariya.
“Oh my sweetie,I miss u so much muuaahhh naringa kissing dinta babu k’ak’k’autawa itama ganin sai dariya nake ina kiss dinta,itama saita bangala dariya tana mamuk’eni mukaita dariyar naji anturo k’ofar Anty shida ce tasha gayu na fitar shari,a tayi masifar kyau saidai kuma fuskarta hawaye nagani,dariyar tau tab’ace tashi nai na dauki zanen goyon Airah na goyeta nace”anty lafiya kuka kike fah don Allah kibari yaufa ranar farin cikin kuce.”
Rungumeni tayi tana shashshekar kuka tace”kinanan anacen ana tashin hankali cikin gida,wai maah da ummi suke fad’a cikin taron mutame khairat,kawai saboda keda Areef,gashican dangin zulfa,a sun maido lefe suna wulakanci da cin fuska,wai ummi ce ta roki alfarmar hadin auren saboda anata alkawarin kujerar minister of communication,yanzu wannan dacewa ne har k’asa yah Areef yake rokonta ta barshi ya aureki amman tasa k’afa ta halbeshi,gashi can anfita dashi asbiti…….mafarin kenan maah takai karshe wajen zuciya take aya ma ummi magana cewa,ta saida mutuncinta da darajarta wajen mutanen da basu da mutunci da kirki,gashinan sun watsa mata kasa ga ido ranar auren sun maido komi sunce basuyi……..ta gwammace d’anta ya mutu bacin tanada halin taimakonsa……shinefa taji haushin maganganun ta mari maah,itama maah ta rama wlh khairat abun babu kyan gani dole akakira su Abbu awaje,yanzu haka ummi ta yi oarking kayanta wai barin gidan zatai………ga mutane kahirat cikin taro wace irin masifa ce wannan wlh duk naji natsani ma auren…..”
Kina kasa zuwarmun yayi saboda wani irin abu daya kulleman ga zuciyata,wani yanayine nakejina da ban tab’ajin zuciyata ciki ba,saidai gani na tayi na zube kan gadon ga Airah ga bayana……wata k’ara ta fasa wadda ta janyo utanen dake falon Annie,kuka take sosai ta sauke Airah dake kukan itama,umminu dr ce ta ansheta Annie ta shiga shafa mata ruwa amman ina ko sake motsawa batai ba,aguje aka kira Dadyn su yah meenah shima ya rud’e daukar ta yayi annie biye dashi yasata mota,
Daman maah da su mimi duk sunacan wajen areef da Abbu,
Dadyn su mimi yaga sadda aka dauko khairat lokacin ya na tama ummj balbalin masifa,ya ce “wlh wani au yasamu yaran nan saint kinyi danasani wlh.”
Mota shima yashiga yabi bayan dadyn su yah meenah……..inda aka kai yah can aka kaini cikin k’an kanen lokaci aka ansheta,……..likitan ta nana lokacin wanda ke dubata lokaci lokaci,dashi aka shiga don ceto ranta……kuka maah keyi kamar ranta zaifita,Annie keta bata hkr itama Annie kukan take abbu ko ya dafe kai da duk hannayensa.
Dadyn su mimi ya iso yana tambayarko ansau ka d’aya daga cikinsu,girgiza kai kurin Abbu yayi.
Dadynsu yah meenah yace”inaga dole ai sanarwa andakatar da daurin auren sai zuwa sadda hankali yakwanta ko inaga hakan zaifi don dukan mu bamada kwanciyar hankali.”

Abbune ya d’ago idonsa yad’an canza yajasu gefe yace”aa jafar(dadynsu yah meenah kenan)baza,ai haka ba amuje ad’aura aure tunda akwai sauran lokaci nanda karfe biyune bazamu iya dakatar da mutanen dasuka taso daga wata uwa duniya ba don halartar daurin auren ba,sai sunzo kuma ace anfasa hakan baidace ba.abunda za,ai kawai kai kamal(dadyn su mimi kenan)ka zauna anan u zamuje muji da mutane kahid da ya iso da imran sai shahid dadyn su mimi yace “Aa muje duka wani cikinsu sai ya tsaya.”
Likitan da ke kula da yah Areef ya karaso yace”ku kwantar da hankalinku munankan kokarin cetoshi,insha Alkah cikin kankanen lokaci zai tashi,kuje ga hidimarku harkun gama kudawo insha Allah zasu sama very save.”
Jinjina kai sukai sannan suka bar angwayen sukatai,lallashin su maah sukaitayi yayinda sukansu suna cikin damuwa,kamar daga sama suka ga ummi taniso wajen tana kuka,babu wanda ya kulata cikin su maah harda su Shahid.
Sai jahid ne yaketa bata baki rungumeshi tayi tana kuka tace”nayi dana sani mujahid nayi nadama,wlh son zuciya da kwadayi suka kaini ga haka amman duk duniya banda kamar ku yarannan,wlh bank’i Areef da khairat don inso ba,shedanne yyi nasara cikin xuciyata………kaje kace wa iyayenku don Allah suyi hkr su daura masu aure yau hakan shine zai dawo dasu sucikin hayyacinsu.”
Agigice maah tatashi daga duken dabtake tana kuka,share kwallar ta tayi tace cikin tsananin fushi da bacin rai.
“Hafsa!”
Zaro ido tayi ummi tana kallon maah da mamaki bama ummin kadai ba har su dake wajen abun ya basu mamaki,don basu tab’ajin ta kirata haka ba saidai yaya koda yaushe.
“Ehy hafsa,koba sunanki bane to idanma mafarki kike kifarka hakan bazai tab’a yuwuwa ba,khairat bazata auri d’ankiba kije kibashi duk wacce kike ganin itace ta cancanta,.”
Ummi kuka take tace”haba saudah,Areef fa nakine kece uwarsa……………ada ba ada nasan nice uwarsa amman ayanzu nabar maki kayanki saboda kin nuna man ikonki akashi,kibashi budurwa sabuwa dal aleda,ba dai jawara ba wacce ta haihu.”
Annie tai saurin rufewa maah baki tana cewa”haba saudah! yazaki koma kamar yarinya,duk wannan bai dace ba kufa y’an uwane ciki daya kuka fito yazaku bari aganku arana,kidufa yadda mutane suka gaye mu,acan gida kunyi yanzu ma nan bazaku hkr ba.”
Maah kuka ta fashe dashi ta rungume Annie tace”wlh gara munke saudbu miliyan akan hafsa,ta nuna man ni bakowanta bace ta tozartani cikin tarona ta wulakanta yarana danice na tarbiyantar dasu ta anshi d’anta da itace taban da hannunta,duk saboda abun duniya sabida mulki shege abun banza da wofi da zai kaika jahannama……….ta jefa rayuwar yara cikin garari gasunan kwance cikin halin mutuwa da rayuwa.mezanyi danita wlh tfita raina tafita daga cikin raina narantse da wandake busa man numfshi babuni babu……………..aguje ummi ta rugo ta rufe bakin maah tana kuka sosai,duk tafice hayya cinta har numfashinta yi yake kamar zaifita,……..”karkice haka narokeki karkice haka ni takice ke tawa ce saudah bazan iya rabuwa dakeba,kekadai garan sai jabir taya kikeson nayi rsyuwa babu ke……….Annie ta janye daga maah umi ta samu damar rungume maah kamar zata maidata ciki……kuka suke suduka idan kagansu saikayi masu kwallah……..duk wanda ke wajen kukanyake masu shahid da imran barin asibitin sukai mujahid ne kurin ya tsaya shima kukan yake,daker yake basu hkr durkushewa kasa sukai rungume da juna kowace tana jin son yar uwarta ya ratsata……..ba wacce ta sake cewa komi sai kuka da ajiyar zuciya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button