ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

“Ya matsayin karatuna yanzu kenan.”

Ajiyar zuciya tayi tace”yananan,kuma kobayan anyi bikin zaki cigaba insha Allah,ai muhammad bazai hanaki karatunkiba kiyi kokri kiyinashi biyayya kikoyama kanki sonshi,nasanma zaki soshi don yanada komi da yadace asoshi.

Anty shida tashigo mun da abinci,don sai yanzu natuna da ashefa ko break banba,tashin hankalin danake ciki yadanne yunwar danakeji,dukda haka wanda naci baia yawa wanka nai nazo nakwanta daker nsau bacci.

Karfe shidda nayi shirin komawa school,gaba d’aya bana cikin yanayi najin dadi,xuciyata ciwo take anya zan iya jure rashin yah tare dani,wai wannan wane irin lamarine,yah Allah kaine ka halittamun wannan zuciyar,kafini sain halin data keciki ka kawo mata agaji………basan ta yadda zan sarrafa taba goge kwallana nayi bayan nagama shiryawar,fitowa nai na samu duk suna falo,wajen Annie naje narungumeta naji kwallah sun cika man ido,nai saurin sharewa nace masu zanwuce.
Yah meenah tace”saina biyoki gobe,munyi magana da dady ya amunce saigobe idan nagama shiryawa zakiganni,koma kibari mutai tare.”
Murmushin dole nayi nace”inada class karfe takwas,bazanso nayi missing ba,saboda lecture tana da muhimmanci sosai.”
Jinjina kai tayi tace”da kyau DR KHAIRAT anason irin haka.”
Duk dariya sukai Anty tace”dr dama wlh inason inganki,tashi nai banda lfy kozaki dubani.”
Dariya ma tabani nawucesu suna ta dariya,nalura sosuke su rageman radadin da nake ciki.
Jikkata na dauko nafito nacewa maah”maah don Allah aban mota hakanan wlh nagaji da yawo kan taxi.”
“Kibari kiyiwa Abbunku magana idan yayarda sai abaki.”
Sallama nai dasu nafita saboda tunani bansan ma nazo bakin titiba,haka dai na isa makarantar husna bata kai ga isowa ba,zubewa nai kan katifarmu nahau tunanin dai da yanzu nasan mun kullah kawance dashi.

Saidai a class muka hadu da Ita,tace shigowarta kenan wlh da bataso dawowa ba don dai tanason taji yadda akecikine.

Ganin yadda idona yayi raurau zanyi kuka yasa tace”aa karkiyi anan bari agama komi kenan saiki gayaman.”
Ranar ba komi nagane ba sosai amman inayin bakin kokarina ganin nafahimta,don akan darasin zaimana test gobe.
Koda muka koma hostel kuka na naitayi sai daker na iya gaya mata duk abunda kefaruwa,ina kuka ina shashsheka ita kanta saida tariga kwallah,rungumeni tayi tashiga bani hakiri,kamar yadda maan tayi,don yanzu babu wata mafita data wuce hakurin.
Wannan dare ban iya samun bacci ba,har garin Allah yawaye sadda za,ace rana tayi wani mugun zazzabi yasauko man,har wata makerketa nake,hakorana suna gugar juna…….duk inda hankalin husna yake yayi masifar tashi,kuma na hana ta takira wani dan gidanmu……karshe dai saboda dole gida nakoma saboda ciwon yaki sauki,zuciyata ciwo take babu kakkautawa saida na dangana ga asibiti,kwana na biyar cikin kwanakin nan kuwa Dr mk zaruarshi bata kilguwa safe rana har da dare ma zaka ganshi,har mahaifiyara yakawo tadubani.
Saida nakara kwana biyu aka sallaman.

Mrs bb ce????????
[6/9, 7:32 PM] Mom Muhseen: ????????????????????????????????
ABIN CIKIN RUHINA

Written by mrs bb
Mom muhseen.

Wattpad name.
Humaira7531

DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.

GODIYATA GA MASOYANA BATA DA IYA KA,SAIDAI NACE MAKU ALLAH YA BIYA MAKU BUKATUNKU,HAKIKA BANDA KAMARKU INAMATUKAR ALFAHARI DAKU.

LOVE U SAHIBA TA ALLAH YA RABA LFY????????

               28.

Gida na koma bayan an sallaman,don maah kin yarda tayi danace abarni makaranta na samu sauki,wai ita aa tafison ina gabanta har na idasa wartsakewa.
Yah meenah kamar ita ke ciwon duk tabi ta damu,kin komawa tai hostel wai saina warke mukoma tare,Abbu kanshi yashiga damuwa matuka inhar yana gida yini yake zarya dakin maah yana dubani,in yatadda ina bacci zai sunbaci goshina yace”Allah yayaye maki ta alkairi,Allah yana tare dake.”
Cikin ikon Allah nasamu sauki sosai,har nakan fito falo adanyi fira dani,sabanin kwanakin baya da ko magana banson yi,kuma banson aiman,don idan aka cika man magana zan fashe maka da kuka,dole suka kyaleni amman yanzu ni da kaina nake fita can.
Dr yau yace zai zo ya sake dubani,kasancewar yanzu muna waya ba laifi,don anyi komi game da maganar auren mu,manyan shi sunzo anyi komi cikin mutuntawa.
Han itama salma nata sunzo duk rana daya za,a daura amman nasu Anty shida ba yanzu ba,yajahid yace ayi mashi hkr sai nan gaba akwai abun da yake maimuhimanci.

Nayi kokari matuka wajen ganin na cire damuwa da tunaninsa,amman lokaci lokaci nakan boye nayi kukana don shine abunda zai rageman radadin da nakeji na rashinsa.

Na fawwalama Allah komi na anshi dr matsayin mijina,tunda na lura son da yakeyi man maigirma ne,soyayyar sa mai sanyi da shiga ran duk wanda akemawa,hakika nayarda da maganar maahda take cewa ya nada duk abunda za,a soshi,nafarko dr handsome guy ne dan gayune sosai,daga ya nayin shigarsa zaka gane hakan, sannan ma,abocin son kamshine kamar dai yah Areef,don shi kafinma ya iso waje turarensa ne d first dazai sallama wajen,to shima dr haka sannan ga fara,a ban taba ganinsa yana shan murba ko cikin aji fuskarsa asake,baza kace yana dariya ba kuma ba zakace yana shan mur ba,kadaran kada han,ya iya barkwaci,duk yadda kake cikin bacin rai zai iya saka ka dariyar dabaka shirya ba.

Dr Ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin ya daidaita natsuwata,nadawo cikin hayyacina shiyasa maah takejin dadi duk randa yazo,itace hada wannan itace hada wancen,haka Annie kai duk yan gidanmu kowa yana son dr sosai,amman banda salma don har yau salma bata shiga sabgar kowa.
KO Ameer dinta yazo babu mai wani rawar jiki,idanma ya samu gaisuwar kirki wajen yan gidanmu,saboda shima halinsu guda da ita,daidai gwargwado maah tana kwatanta adalci tsakaninmu duk da cewa ba itace ta haifeta ba,amman duk abunda ta siya man to zata soya mata itama,saboda tace har gobe salma diyace wajenta haihuwarta ne kurun ba taiba,don haka zatai mata duk abunda uwa take ma yarta.
Duk da wannan abun bai saka salma taringa gaida maah ba,bata gaidakowa yanzu,har gara idan yah shahid nanan zai ci ubanta yace kuma sai ta gaida duk wanda ke saman ta,duk randa akai irin haka bata kwana gidan sai tayi tafiyarta gidan inna,wannan abun da ta keyi ya kara sakaman salma tafita raina,don duk wanda bai girmama mahaifana ba nayi dashi.
Abbu duk yasan wainar da ake toyawa baidaice komiba,don inajin inna tayi kalami mai kaushi akan salmar,bansan dai me tace mashi ba.

Rannan Abbu yazo har dakin maah yayi man ya jiki,ya saman ina bacci hirar su ta tadani,sai ban nuna na tashin ba,naji maah tana mashi complain din salmar yace”saudah,kiyi hkr kibar yiman zancen yarinyarnan,tunda kinsan bazan iya yin komi ba,akan kunnenki inna tayi man Allah ya isa idan na sake takurata ko nayi mata wani abu daya bata ranta,kibarta tayi duk abunda ta ga dama kowa rai yaima dadi baya ga maishine,Godiyar danake ma Allah daya bata miji daidai ita,munanan daku Allah shine zaiyyi maganinta.”
Maah bataji dadi ba tace”karkayi mata baki Dear,hannunka baya rubewa ka yanke kayar,ya kama ta kayi mata addua kurun.”

Murmushi yayi yace”hakika samun mace kamarki mai tsarkakakkar zuciya sai antona,Allah yai maki Albarka Addua kuma ai tunda aka haifeta nake mata ita,don haka kifita batun salma karki ma sama ranki damuwa.”

Hakan baisa maah ta daina duk wani shiri ba akan bikinmu,wanda yarage sauran sati uku.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button