ABIN CIKIN RUHINA COMPLETENOVELS

ABIN CIKIN RUHINA COMPLETE

Mrs bb
Mom muhseen
09934722970.
Follow me on wattpad Humaira7531 and pls share it somes grps.

Abdoul-nasser (Alfah) is very nice and sweet story,don’t miss it,very soon zaifara uwa maku karki bari abaki labari ABDOUL-NASSER (ALFAH)
[7/3, 10:26 AM] Mom Muhseen: ????????????????????????????
????
ABIN CIKIN RUHINA

Writing by mrs bb
Mom muhseen.

Wattpad name
Humaira7531.

DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.

Not edited.

                 43.

Koda na fito shirin kwanciya nakeyi muna magada yah meenah,kayan nake bincika wa wadanda zasu shigeni,amman abun haushi duk sun man kad’an,saboda wannan cikin yayi girma kamar dan wata tara dariya yah meena keyi man,duk naji haushi ya kamani ficewa nai nabarta……….maah naje naiwa saida safe sannan na wuce wajen Annie don yau tare zamu kwana dady yayi tafiya shida Abbu Germany,sai nan da kwana uku zasu dawo.

“Maah don Allah ki araman rigar dazan kwanta,wlh nau duk basu shigata.”

“Dama ya za,ai su shigeki khairat inbada rigima,jibekifa yadda kika koma sunbukekiya.”

B’ata fuska nai “haba maah kema haka zakice man,kowa sai yce man haka ni wlh nagaji da cikinnan wai yaushe zan haihune.”
Murmushi maah tayi tace”kinda sauran 3month gaba”
“Nashiga UKu na maah nidai wlh yayi yawa.”

Bata fuska tayi tace”banson sakarci,kintab’a ganin an haihu wata takwas ko shidda,kiyi fatan ki haihu lfy shine kawai,anshi nan ni ki wuce kije ki kwanta kinata yawo kowa ya natsu bandake.”
Ansa nai nafita ina jin babu dadi,cikin nan ya isan hakanan,wahala nakesha ba yar karama ba.
Allah yasa dai haihuwar saidai inji ance tashi kin haihu,don wannan wuyar mankad’ai ta isa.
(????????????lallai ta alkairi to bari mujira mugani)

Rigar na saka duk da cikin ne yacikata nikaina saida naima kaina dariya,saboda yadda rigar tayi man kamar buhu……..kaina yana kan cinyar Anni muna kan gadonta,shafa kaina kurun take na lumshe idona ina tunanin rayuwata,daidai da second dr yana cikin raina,komi nake komi zanyi he still in my mind. Hawaye suka gangaro man,nashare na tuna abunda ya faru daxun falon ummi.
Bansan ma naja wani dakikin tsakiba,jinai Annie tace”subhanallahi khairat,kina lafiya kuwa.”
Gyara kwanciyata nai nace”nothing.”
“Karya kike,kinsan karya dai ko to ita kike khairat don haka gaya man mekedamun ki.”

Kwallah suka cika man ido,bazan iya boyewa Annie damuwata ba,don koda can itace kawar shawarata,duk da ga yah meenah.
“Inajinki kishare wannan kwallar kisanar dani.”

Ajiyar zuciya na sauke inajin tarin haushinsa cikin zuciyata,
“Annie wacece zulfa,a.”

“Zulfa,a!”ta sake kiran sunan kafin tace”ina kikaji wannan sunan.”

“Annie nidai wacece.”
Shiru tayina wani lokaci kafin tace” MATAR DA AREEF ZAI AURA CE.
Lumshe idona nai inajin yadda kirjina yake duka,ganin na ki cewa komi yasa tace”ya akai kika tambayeni.”
Numfashi na sauke nace”d’azu ina wajen ummi naji yace zaije wajenta.”
“Toke miye naki aciki,kina fama da takabarki,kisamu ma kisauka lafya shine burinmu,kifita sabgarsa ko har yanzu kina nan kina dakon sonsa.”
Runtse ido na nayi inajin maganarta ta karshe ta sokan,”Aa Annie nima ban saniba,amman tsanarsa tafi karfi cikin zuciyata,duk da cewar idan nace banson yah nayi karya Annie,Amman wlh tun da yai sanadin mutuwar mijina naji natsaneshi,banson ganinsa ko kadan sannan kuma gashi baimun gaisuwaba.”

“To kishin me kike dajin zai aure”
“Ni ma bansani ba amman insha allah annie zanfita harkarshi.”

“Stop da dai yafi,don sonake yadda ya baki wuya kema kirama,munanan zaizo ya sameki.”
Munjima muna hira da Annie tana ban shawarri masu ma,ana har mukai bacci.

????????????????????????????????

“Wai kana lfy kuwa Areef,ni bantab’a ganinka cikin irin wannan condition dinba,tunda ka dawo na lura baka da wata walwala,ni amatsayin dan uwanka kuma abokinka bazaka iya sharing problems dinka dani ba,atleast ai nabaka shawara,inkuma lallasheka koda banyi maka maganin abunda yake damunka ba.”

Kwance yake kasa yayi filo da hannunwansa,kafarsa kan daya,yana girgizata ko sawu cikin da yake sanye dasu bai cireba,idonsa akulle yanajin duk kalaman jahid.
Mezaice mashi dawane idon zai kalli jahid yace yabashi shawara kan abunda ada suka samu sab’ani dashi,sukai kaca kaca ina it can’t.

“Shikenan Zan kyaleka kuma wallahi kaji rantsuwar dan musulmi muddin kasake nayi promise akan ka zakasha mamakina,don bazan sake damuwa da damuwark ba,tunda bankai matsayin da zaka fad’aman matsalarka ba.”
Yajuya ya haye gadon yaja bargo.

Aranshi yake ta magana”kayi hkr jahid inajin kunyar kallon idonkanin gaya maka, ABIN CIKIN RUHINA ce ke azabtar da ruhina,akullum kaunarta sake azabtat dani take,bansan har sai yaushe zan huta da masifar so ba,nikuwa soyayya bata sona,na girma da kaunarki azuciyata tun banson kaina ba,gashi na azabtar dake atare a daliliba duk don in nuna ma waana ke tunin ina sonki cewar ni baki gabana,shin kema kina cikin masu ganin cewa baki gaba,kiyi hkr kiyafewa yayanki masoyinki baida kamarki duk cikin zuciyarsa,da sonki nake kwana nake tashi,koda wannan kika barni kadai ya isheni,insha Allah bazan sake rasa kiba karo na biyu,nine mijinki nine wanda zamu kare rayuwarmu tare,Allah yaga Abunda ke raina shiyasa ya dauke mijinki,don yasan bazan iya cigaba da rayuwa ba batare dakeba,duk wani abu danake borene amman bagaskiyar lamarin kenan ba,kiyafe man inasonki ina sonki inasonki,wlh nai ma kaina alkawarin mallakarki koda mutanen duniya zasu taru kaina don hanawa……………….wannan dare Areef ya b’atashi ne yana kua da idonsa,akan son ABIN CIKIN RUHINSA ganin kuka da sabbatu basuyi,yasa yatashi yaringa jero salloli yana gaya ma ubangiji……duk abunda yake Jahid yana jinsa,dariya kurin yake cikin duvet don yasan tatsiniyar gizo bata wuce ta k’ok’i.

      ***********

Yau salma tazo tana kuka duk ta tada mana hankali,kuka take sosai kamar ranta zaifice duk mun tusata gaba sai tambayarta ake ta kiyin magana,ummi daman har yanzu haushinta takeji,ganin takiyin shiru kuma taki fad’an abunda yafaru,yasa tatashi cikin fushi tafita tana cewa,
“Yau ga yalbura uba,do ubanki ana tambayarki kina yiwa mutane shiru,to ki kwana dubu kinyin kuka ni kunga tafiyata inada abunyi.”

Ummi badai fad’a ba ba,atab’ota ba ma wace Allah cika bakle antab’ota,kukanta taitayi har lokacin da su yah jahid suka shigo sun dawo daga office.

Yah jahid yace”lafiya me ya sameta haka take kuka.”

Maah tace”kilan kai ta fad’a maka mukan ai har mungaji da tambaya.”

Ni daman ina gefe zaune k’asa na baje ina cin gyad’a,cikinnan ya fito kamar wata randa,duk tambayar da yake mata tai ki bashi ansa yace”to Allah yabaki sa,a bari na wuce nai wanka.”

Wata tsawa da yah Aref ya daka mata saida na firgita zan ruga,saboda tsananin karfin ta.
“Ubanwa zaki tusa gaba kina wa kuka ana tambayarki kuma kinwa mutane shiru,zan b’ab’b’allaki wlh anan wajen idan nasake jin shashshekarki saina farfasa bakinki sakarai kawai common tell them what’s ur problem.”

Runtse ido nai saboda yadda yake magana kamar zai haukace,du yagigitani wlh.
Saiga salma tayi tsit kamar ruwa yacita muryarta bata fita sosai tafara magana.
“Maah,Ameer ne.”sai hawaye sharrrr kamar ankunna famfo…….cikin dakakkar murya yace”meyasami Ameer din,mutuwa yai koko baida lafiya.”
Tana gunjin kuka tace”Aa,dukana yayi shida matarsa.” (kasancewar bayan tafiyar su khairat yawon shakatawa Abbu yakirashi andaidaita ,amman yace shifa aure babu fashi sai ya auri raihana Haka dai aka samu aka sasanta ta koma akakuma yi auren sada raihana)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button